← Book details Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 110

Sashe 99

Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read

Soyaya kuwa ta dinke da Mariama da Fahad, inda ya hadata da familynsa a vidio call suka gaisa da yar hausarta da bata taka kara ta karya ba, dan kuwa french dinma ba wani sosai take ji ba, buzanci ne shi kuwa ba yarensa ba, soyayar dai ana yinta ne karfi da yaji domin wani sa.in sai a rasa ta yanda za.a isar da sakon khalb.

Niger

Da gaske yake, ko nace da gaske suke,
Abu ne ake tamkar ba gobe,
Dukan bukatun Ayya kan lamarin tarewar yarta an cika mata, inda ake shan rigimar shi ba za.a yi wani taron diner ba, kawai a yi saukar alkur.ani, Ayya kuwa tace ai ko walima ne sai ta yi ta gayaci mutanenta an yi taro na kirki itama ta aurar da yarta,
Ido ya kawo ya zuba , yama maida hankalinsa kan aikinsa wanda kulun cikuluftu ke karuwa,

Ayya kam ba kama hannun yaro, wani irin shiri take yiwa yarta wanda siri ne,
Ya kasance ko masu aiki basa gannin Agaishat a dakin da ta kilaceta, daga ita sai ita,
Du a tunanin Ayya y'artata ta saan aure, hakan ya sa take wani irin shiryata dan ko ba komai ta iya zama a gidanta, kar a rainata ta wannan fannin,
Sosai ta bata magannin infection, kafin ta shiga bata lakaninika ciki harda yusufa da kankanna,
Kwata kwata ta haneta shan ruwan sanyi, inda take dumamata da masu dan dumi ,
Haka indai jikinta ya ji iska tofa wanka ta shiga, tana fitowa take maida lulubinta ta lulube, dalilin haka har yan kurajen zafi ta yi, suka mutu dan kansu jikinta ya saba ya kasance koda yaushe cikin dumi yake,

A kulun zai yi zuwa biyu gidan, yakan bi Ayya da kallo ne, tun lokacin da ta masa iyaka da tambayarta Agaishat, ya kawo ido ya zuba mata, wai tana gyarata, har sai da ya ce"Ayya, ni guaran na menene? Me kike gyarawa ne?
Ta yi masa shiru ta kawar da kanta, dan ba za.a ja maganar da ita ba, idan shi bashi da kunya ita kam tana da ita
Shi kuwa daga shi ya yi shiru ya daina tambayarta ita, kuma abinda ke bashi mamaki ko wulginta da baya gani, ya dai san lokaci ta deba, kuma saura kwana uku, hakan ya saka ya kawo ido ya zuba mata,

Yau sauran kwana daya kacal tarewar Agaishat,
Kowa ya dauka kan tarewa ne, dan ta taba aure,
Jama.a da yawa na mamakin wannan aure , General ya auri bazawara? Ayar tambaya, wa.inda suka san matar da amininsa Mu.azam ya saka ce kuwa suna yayata maganar daidai da mandan bakinsu,

Wardugu, bai san irin halin da zai kwatanta yake ciki ba, ga aiki da ya sako shi gaba domin ana yawan kawo hare hare yankin Diffa, tsaye kan kafafunsa , dan haka ya kara neman alfarmar kar a yi maganar diner, gannin halin da ake ciki ya saka Ayya amincewa , aman hakan ba zai hanata yin nata taron ba,
An kawo garar amarya da akwatuna,
Zama zanowa bata lokaci ne, Wardugu ya kashe kudi sosai, kaya kuwa an zuma na yar gata,

Agaishat kan fashewa da kuka wani lokacin , kukan murna, kukan godiya ga Allah, tana jin Ayya har kasan zuciyarta, girman Ayya daban ne, tana sonta so irin na da da uwa,
Saima idan ta zauna tana tuna hirarsu ta yau bayan salar asuba, yau da ya kasance za.a mikata dakinta, gidan mijinta, wanda take fatan sai dai a fitar da gawarta, Ayya ta dubeta ta ce" zan so biyayarki, tsoron Allahnki, ya kasance bayan zuciyarsa da kika shiga, ki shiga kowani motsi nasa,
Agaishat, ban hore ki da rashin kunya ba, ban hore ki da tsayaya ga miji ba,
Agaishat, shin wanda aljanarki take karkashin kafarsa wani irin motsi zaki yi dan gannin ya dage kafar nan tasa ya baki damar shigewa?
Ki yi masa biyaya,
Ki barshi ya fada,
Idan ya daga murya ki kaskantar da kanki,
Kar ki yarda yana fada kina fada Agaishat, da haka gwara ki yi nesa da shi! Ban ce ki zauna ya wulakanta ki ba fa, ko daya, ina dai doraki kan hanyar da zata kai ki ga ci ne,
Kin ga kar ki yarda daga saman salayarki ki sauka da asuba ba tare da kin furta kwali a kwayar idannuwanki ba, ki adana kwalin ki kusa da abin salar ki!
Kar ki haye gadon da kika gyara dominsa kafin shi ya hau (ina kuke ne mutanenmu , iyayen mu🤣, gafa wajen🤣),
Idan ya yo dare, ki kasance mai jiransa , kar ki je ki jibge saman gado, har ya zo ya gama abinda zai yi kina minshari (😅 kin ji ko maniu🤣🤣),
A duk lokacin da kika ga da hali, akoy robar wankin kafa, akoy dutsi, ki zauna a yar kujera ki saka kafarsa ki wanke, ba dan ta yi dati ba, sai dan kara shakuwa tsakaninku koda kuwa bai saba gani ba, kar ki wani damu ke dai ki koya masa irin zamanki da kike so ku yi,
Akoy wahala fa, domin kuwa ba ke ya fara aura ba, ba ke kika fara rainonsa ba, zaki ga abubuwa da yawa wanda haka matarsa ta hore shi da su, wasun zasu canzu cikin hikima da juriya da hakuri, wasun kuwa Agaishat sai dai ki rayu da shi a haka!

Sai maganar kananun kaya,
Ina mamakin zamani, ina mamakin yayi,
Wai idan za.aiwa yarinya aure da budurwar da bazawarar da datijuwar sai ki ga ta kama kwasar kananun kaya , kananun kaya ita dai,
Uhum, kuskure baba,
Ke Agaishat shin sex din ne kawai ya kai ki gidan auren? Tabas shi ne jigo, shi ne farkon gini, aman shi din an gaya maki zama kusan tsirara a kulun ne zai saka shi armashi?
To albishirinki, walahi ni na fada maki, du abinda ya kasance shi kulun a fili a bude yake komai darajarsa a hankali take raguwa har ya kasance ta bace bat!
Shigar kananun kaya, akoy lokaci, ba ina nufin kowani dare ba, no , aa, lala!
Ki sayi masu tsari, masu ma.ana , masu kai,
Masu taushi!
A cikin gidanki Agaishat, ki kasance cikin shiga ta kamala, ki ringa yawan yi masa rowar ganninki gaba dayanki arha,
Agaishat, ki ringa saka riga da zani da dan kwalinki, ki yi sasaukar kwaliyarki sannan ki zauna cikin kanshi,
Ki ringa saka sket da rigarki na atamfa, ki ringa saka doguwar rigarki au ta atamfa ko abayoyinki, ki ringa nada saharinki, ki ringa hawan lesh da shadarki kina zamanki, ke wani lokaci ki yi sasaukan shiri abinki,
Ki ringa daukan lokaci kafin ki yi masa shiri na kananun kayan, ya kasance a ranar yana kusa, ki saka abinki , ki juya a gabansa,..... Agaishat zaki baiwa wani labarin mahinmancin hakan, mijinki zai kasance yana mai jin zumudin riskar ranar da zaki hade masa cikin shirin nan, sannan koda lokacin da zai ziyarce ki ne, zaki ga zai warewa wannan lamari mahinmancin da za yana nuna maki, ( iyayen mu, na zaunar da mu ne, su yi mana huduba, fila fila, shin da wada take yarena ta tabatar? )

Sosai Ayya ta yiwa Agaishat nasiha, gargadi, ta ankarar da ita zaman duniya, dama hasashen na auren da take, kafin ta nanata mata maganar cewa *AGAISHAT* ,tabas kyau, fari, mulki, arziki, na jan soyaya,
Sai dai ki sani *ZUCIYA NA SON MAI KYAUTATA MATA* ,
Wannan kalma kuwa , ta tsaye mata a rai kamar yanda sauran suka tsaye mata,

Haka aka wuni shagulgula kamar ba gobe,
Sosai Ayya ta gayaci mata, mata kuwa sun amsa kira, inda aka wuni ana tafiar da taron yan gayu,

Kai amarya, ba.a tashi shirin amarya bama sai wajen karfe goma na dare,
Ayya ce da kanta ke darwaye yarta, kafin ta mulketa da turaren Angel,
Haka ta zaunar da ita ta saka mata kwali kadai a idannuwanta kafin ta damka mata shi a hannunta,
Wata arniyar Lafaya ce ta nada mata saman lafiyayiyar doguwar rigarta ta atamfa mai ruwan ja da fari kar,
Ba.a saka mata dan kune ko awarwaro ba, takalmin kafarta kansa wani plat ne,

Dirar motoci suke ji , tun suna hasashen za.a dakata abin gaba kawai yake,

Labule Alhinayet dake tsaye cikin shigar wata dakakiyar shada ta daga,
Gaba daya sai da tsigar jikinta ta tashi,
Hasbunalahu wani.imal wakim,
Shi ne abinda ta furta a lokacin da ta hango motoci layi biyu, kowace tana kilyoten yan wutocin gaba, kowace da soja tsaye a kusa da ita,
Sun layu gaba dayansu suna ta tafi ana shakiyanci irin na sojoji a cikin yannayin farin ciki,

Ta tsakiyarsu yake ratsowa a lokacin da Alhinayett ta hango shi ta saki wata buda tana kada harshenta ta shiga kwasar shoki,
Wato wani irin shirya daukan amarya ne aka yi wanda sai wanda ya gani,

Haka Ayya ta kamo hannun Agaishat dake ta hawaye tana jin wani irin lamarin a jikinta wanda bata taba ji ba a aurenta na farko,
Ya Allah, ya Allah,
Ayya na fitowa da ita daga dakin nayake ainayin nata aka shiga guda ana zuba mata kudi,
Ayya ta riketa da kyau suka shiga saukowa daga matatakala inda ta shiga neman aminiyarta dan ta mika Agaishat dakin mijinta,

Tsakiya suka saka Agaishat suna tarairayota,
Alhinayet kam har jikinta rawa yake , domin gaba daya wajen fa ba dama, muryar sojoji ne suna fadin"Hei Hei Hei Hei,
Inda Wardugu ke takowa a kafarsa, jikinsa sanye da kakin soja marroon , wandon da kadan ya zarce kaurinsa sannan ya rike shi daga kasa, rigar kuwa baka ce jikinsa aman bai sakata cikin wandon ba , janta ya yi ya dorata saman yar karamar bindigar dake tsatsonsa, sai ranjes maroon waro takalmin sojoji, rigar mai karamin hannu ce , hakan ya sa damatsunansa du a waje,
Du taku da zai yi sai kura hei tun karfinsu murya irin ta garada, sannan su yi wata yar rawa da kafarsu ta dama baki dayansu a haka har ya karaso wajen yan matatakalar da zai taka ya hau kafin ya shige dakin Ayya , aman sai ya ja ya tsaya,

Daidai nan su Ayya aka bude masu suka fito da amarya,
Chapter 99 · 0% Book details