← Book details Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 110

Sashe 26

Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read

Juyawa ta yi ta nufi bangaren Wardugun cike da isa, sai a lokacin Mu.azam ya lalaba Agaishat ya cire mata tsoro suka fito daga motar,

Mu.azam ruwan sanyi sai ya nufi wajen su dan gaishe su,

Walyn ta daga ta watsar da idannuwanta sannan ta zabgawa Agaishat wata muguwar Harara da kallon kyama ta juya tana riko hannun mamanta suka koma bangarenta,

Agaishat dake dafe da kirjinta jin yanda zuciyarta ke dokawa Mu.azam ya kallo,

Murmushi ya sakar mata ya ce" mu je Matar Mu.azam,

Ido ta zaro kafin take daga kafa da sauri ta yi gaba tana jin wata kunya kunya da wani irin abu game da Mu.azam din, yakan mantar da ita wacece ita ta halin nuna mata itama mutun ce mai cike da cikeken inci, yana yaba kalar fatar jikinta ta hanya kawatata da kalamai masu tsari da sence, yakan ce Allah ya datar da shi samunta, ita Agaishat yar gidan Sofo? Tana so ta biye masa tana tsoron ko wasa yake mata? Tana son ta yarda tana tsoron yan birni,

Ayya na shiga ta zarce har dakinsa na baci tana fadin" ina kake janyau, ka hargitsa mana gari ka lafe a gado, tashi tashi kaima ka yi kwanan zaune dan nema kawai!

Da wani irin sauri ya mike ya diro ya warci doguwar rigarsa yana faman sakawa ta shiga dakin,

Wardugu ya ce" Ayya, wai yaushe zaki dauna shigo min haka zaraf kawai? Me ya fito da ke a tsohon faren nan? Ya aka yi kika ratso sojawan hanyar nan? Wa ya kawo ki?

Maimakun Ayya ta bashi amsa sai cewa ta yi" baka da sutura a jikinka ne kake kwonciya Wardugu?

Wardugu ya dafe kansa ya furrta" Ya Allah,

Bakinta ta yatsina ta ce" fito ina jiranka

Sai da ya saka kayansa ya biyo bayanta,

Yana fitowa ya ga Mu.azam, da bakuwar nan ta ayya da shi ba zai iya fadin sunnanta ba dan bai wani rike ba,

Sai dai mamaki yake, yanzuma wasu kayan ne jikinta, shi abinda ke bashi mamaki yaushe ta iya saka kayan tubawa har yake bin jikinta haka? Yaushe ta iya saka kayan kansa nema ?

Kawar da kansa ya yi da sauri yana yatsina bakinsa yana ayyana ina ruwanka yo, ba dai Ayya ta daure mata ba?

Ayya ta karbi kulin maganinta ta umarci agaishat da ta bude frij dake nan falon ta fauko ruwan roba

Agaishat ta nufi frij tana tambayar kanta ina wajen budewar yake? Domin ba irin na gidan Ayya bane, wannan wani glass nema a jikinsa ko.ina tar tar yake ana hangen abubuwan dake ciki tar sai dai ba lale ka san wajen kunawarsa ba,

Ja ta yi ta tsaya tana kallo,

Ayya dake jira ta kallo wajenta ta ce" Agaishta kawo mana,

Agaishat ta juyo tana raraba idannu ta ce" Ayya, ina zan bude??

Wardugu ya girgiza kansa, Mu.azam ya mike ya je ya nuna mata ya bude mata, ta nuna masa wanda take tunanin ruwan ne?
Mu.azam ya ce mata" wannan ai jus ne, gidansa da kamarsa yake yannayin ruwa, aman kin ga jerin ruwan nan,

Nan ta dauko suka dawo wajen Ayya dake ta yiwa Wardugu fadan ya kwonta bai ci abinci ba dan ba sai ta tambaya ba ta sani ne kwonciyarsa zai yi, aman kwata kwata bata sako maganar matarsa ba ko iyayenta, bata da wannan lokacin,

Wardugu dai kallonta yake, ta bude ruwa ta tsiyaye fiye da rabi ta zuba maganin ta girgiza ta mika masa ta ce" shanye,

Wardugu ya cee" Ayya meye kuma wannan
?

Ayya ta ce" Wardugu, magannin baki ne, bakin mutane, ka san baki fa ya fi maye mugunta, baki ai ba dan uwa bane, bare yau ka janyowa kanka maganar mutane

Robar ya rike a hannunsa ya ce" Ayya, bayan walahaulan da nake yi kuma dai kin bani wannan jike jiken naki?

Ayya ta ce" walahaula hanyarta daban, wannan ma nasa daban, kai harda garin hantiti nake tafe, maza shanye ka dauko min buta a bayinka na zuba maka ka yo wanka ka turaru sai mu juya,

Ido ya zaro yana kallonta, kafin ya maido dubansa wajen Mu.azam da irin kallon kai ka kawota ko?

Mu.azam ya juyar da kai wajen Agaishat dake zaune kasa yana kallonta, domin kallonta na saka shi nishadi

🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫

Na *SAJIDA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

2️⃣8️⃣

Bani da bakin da zan yi godiya a irin tarin kulawar da kuka nuna, da tashin hankalin da kuka nuna na wannan abin da ya faru, kunya ta kama ni, na ji kunyarku sosai na irin hada ni da Allah da kuka yi, wacece ni? Ni ba kowa bace da zan ki yin hakuri dan haka nake shaida maku ga *BAK'A* . Daga taku yar mutan niger

Kun yi sake , kuna gani tana zuwa ta shige dan ta samu ganninsa aman mu tun da yama muke zaune, a matsayin mu na iyayen matarsa yace ya gaji ba zai fito ba, kina ganni da takama bayan ta fada mana magana ta shige abinta,
Auntyn Walyn ke fada ranta na kara baci,

Mahaifiyar Walyn ta ja tsaki , ta ce" koma me take takama da shi ai mijin ya nuna mata iyakarta, yanzu ba da kishiyarta bace yaronta ke fada? Banza ita har ta isa ta nuna ita wata ce? Bayan an ci mata mutunci kowa ya sani?

Walyn dake zaune, gaba daya zuciyarta ke wani irin tashi, ta rasa me ke damunta kwanakin nan takan tsinci kanta a irin yannayin rashin jin dadin jiki, bata iya kara furta masu komai ba ta mike ta je dan ta saka a kara tsaftace masu wajen da zasu kwana, domin ba zata lamunci a rufe iyayenta ba, za.a samu matsala sosai,

Sai da aka sha rigima da Wardugu ya shiga wankan hantitin da Ayya ta jika a butarsa ta karfe,

Yana yin wankan ya fito yana jin yanda yake warin magannin, sai dai yana fitowa ta kuma tare shi da hayakin Hantitin nan yana ta bade shi ,

Jajayen idannuwansa kawai yake binta da su, in ba Ayya ba, wannan uwar gajiyar da ya kwaso ta zo ta tirke shi da wannan abubuwan? ,

Tana gamawa ta fita fallo da hayakin bayan ta debo turaren wutar dake jere saman coiffeuse din dakin tana tafe tana dan sakawa yana tashi a hankali,

Kansa kawai ya girgiza, ya cire jalabiyarsa ya saka rigarsa mai karamin hannun wace ta baiwa jikinsa damar bayanna ya saka wandonsa dogo fari na jalabiya saman gajeran ya fito,

Ayya dake kallon Tv, Mu.azam kuwa sai wani kara shigewa Agaishat yake yanai mata labari kasa kasa, wanin ta zaro dara daran idannuwanta, wanin ta dan yi murmushi, wanin kuwa sai dai ta rufe fuskarta da hannayenta wai kunya take ji,

Galala ya yi yana kallon kusancinsu da kuma yannayin su,

Ayya ce ta juyo wajensa , sai dai ranta ne ya baci gannin irin rigar da ya fito da ita, ita kam ya zatai da wannan sakarar dabi.a ta wardugu ta saka kannanun kaya? Sam ba al.adar batuben mutun bace, Batuben mutun yanda mace zata ji kunyar bayannar da jikinta haka shima namijin, sun fi saka manyan kaya sukan yi rawani ko su aza hula saman kansu, suna saka kananun kaya irin na zama aman dogon wando har kasa, riga mai mutunci su yi zanzaro abinsu, aman fa siri batube sai mata nai, shi ya saka take mamakin Wardugu, gatsai gatsai sai ya bi gari da wando daidai gwuiwa, riga mai yankeken hannu har yana wata takama,

Rai bace da yaren tubanci ta ce" Wardugu ! Nigey medi nubazzu ? Ay kubu nukoy ? Anna gnuduro indi hadin ? ( Wardu! damme bakajin magana , wannan wane irin rigane ? Idan mutane suka ganka me zakace?),

Wardugu ya kalli rigar jikin nasa, kansa ya shafa wanda haka kamar ya zame masa jiki, ya juya ya sako wata riga a saman wannan duda haka bai bala boturanta ba,

Yana dawowa ya zauna yana kallon Ayya,
Ayya ta girgirza kai ta ce" a gaskiya wannan abin sam bai yi ba, kai ba wani karamar kira ba , ka wani saka kananun kaya, yanzu haka a haka sirikanka suka ganka wardugu? Salon a fita da kai a baki ko?

Wardugu ya lumshe idannuwansa ya bude ya ce" basu ganni ba,

Me kake nufi da basu ganka ba?,

Wardugu ya daga kafada ya ce" ai na gaji ne, sai idan na huta Ayya,

Da kallo take binsa, a sanninta yana matukar jin kunyar iyayen matarsa yana darajasu, ko dan irin yanda sirikan namiji keda matukar daraja wajen mijin yarsu a al.adun tubawa, domin kuwa suna da dama sosai a kan mijin yarsu, aman yau yace wai ya gaji bai je ya gaisar da su ba? Ta so ta tsawatar sai kawai ta kyale, domin dai Walyn da Wardugu auren so suka yi, shi bai taba kawo mata karar matarsa ba, itama bata taba kawo masa karar rashin girmamata da Walyn bata yi ba, ai ido ba ma.auni bane abin duba ne, yana gani kuma yana sane, dan haka ta watsar ta mike tana duban Agaishat ta ce" ku tashi mu tafi kar mu kwana a gidan nan kun ji?

Wardugu ya kaleta yana talabe habarsa, ya ce" Ayya, ai yau sai dai ki yi hakuri da gorin wai kin zo gidana, yau kwana ma zaki yi Ayyar wardugu,

Ayya ta zaro ido tana kallonsa, ta ce" kai, ka rufamini asiri, ni na kwana a gidanka wardugu? Aa aa, ka tashi ka mayar da mu da kanka man,

Wardugu ya dubi Mu.azam ya ce" kai, zaka bado hankalinka nan ne? Bakin karfe dayan dare dokar ba wani karbar uzuri, motocin yan tafiya kawai za.a bari su je masaukinsu, suma sai dai su waye a can, ba zai yiwu ni na karta dokarnan ba Mu.azam zaka saka baki ko sai na ...

Mu.azam ya taso yana dariya ya ce" Ayya, karfe daya saura kadan, ki yi hakuri, mutuncinki, girmanki ya fi karfin ki je cel Ayyarmu, kuma ke ke fadin ya yi aikinsa tsakani da Allah a rayuwa, ki yi hakuri Ayya,
Chapter 26 · 0% Book details