← Book details Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 110

Sashe 22

Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 7 min read

Ayya na gama daura mata kunshin ta mike tana leka windows, mamaki take irin yanda yanzu wardugu ya ajiye kafarsa a gidan, duda ta san amininsa na nan dole za yana yawan zuwa aman abin na bata mamaki, bai jima da fita ba fa aman har ya dawo, sannan yanzu basa fada da mu.azam akasin da da sai ta shiga tsakani ko ta gindaya masa doka kan Mu.azam din kafin yake barinsa ya huta, yanzu kuwa bini bini ya shigo ya haye wajen Mu.azam su yi ta hirar da ita bata san ko ta meye ba, yanzun ma tsaye suke su uku, da yar jajar nan Alhinayettt sai hira suke suna dariya,
Rufe windows din ta yi ta juya ta fice ta bar Agaishat na zaune tana jira ya bushe ta wanke kamar yanda Ayya ta fada

Bayan kunshin Agaishat ya bushe, ta mike ta saka takalminta silifas ta yi bayi,
Wanke kunshin ta yi, jan kunshi yayi jajajir, ga mamakinta ya fito sosai a fatarta har ya haska mata fatar kafar da hanayen,
Da sha.awa take kallon kunshin ya yi kyau a idannuwanta,
Ta dauki lokaci a bayi domin sai da rmta yi wanka ta fito ta je bakin madubi tana goge gaban goshinta inda ruwa ya taba kannanuwan kitson da Ayya ta dage akai mata wa.inda sai warwarewa suke dan kansu ,

Turarukanta ta zauna ta shafa na madara masu sanyin kanshi, ta shafa mai kadan a jikinta,
Kwali ta dauka tana adu.a domin har yanzu ta kasa sabawa da saka shi da dadi sai ta yi ta fama, bayan ta saka ta caje girarta, ta dauki wani jan baki mai ruwan lebe wanda Ayya ta fada mata kadan za tana shafawa a lebenta na kasa,
Hakan kuwa ta yi ta shafa kadan kafin take tsurawa madubin ido, tunda ta zo garin nan ka.ida ne a wuni sai Ayya ta tsareta yin wanka sau biyu wataran har sau uku, idan kuwa ta yi wanka dole ne ta zauna ta kula da du wata gaba ta jikinta, tun tana kallon haka a wani iri har ya kasance idan bata yin ba itama bata jin dadi, sannan ta yarda da mutun sai da gyara, wannan mugun bakin da take gani a jikinta a ruwan wanka ta ga yana sauka daga jikinta, tsabar rashin wanka na kirki ne da kuma karin bakin turkidi(tufafin buzaye), yanzu fatarta ta kasance bak'a mai haske, irin bakin nan mai kyau mai birgewa, ga gyara yana kara samu yau da kulun, har santsi santsi take ji fatar tata ta fara yi mata,

Mikewa ta yi dai ta shiga fitar da riga da siket din da Ayya ta rataya jikin abin turaren wuta tun da safe kan su zata saka,
Wani ni.imtacen kanshi suke na turaren tubawa,
A hankali ta saka slipe (pant) dinta, an ta kasa saka breziyar domin har yanzu bata iya aiki da ita ba, kai ita bata ma sonta ne ,
Kayan nan ta saka sket da riga, sun amsheta sun mata cicif a jikinta dinkin zamani ,
Tsaye take tana kallon lufayar da Ayya ta bata, ta nuna mata ta koya mata daurawa sai dai bata iya ba har yanzu (daura lufaya sai a slow),

Gashin kanta kawai ta sakawa ribom ta saka yar bakar hular da Ayya ta hada mata da kayan ta luluba Lufayar ta fice da takalman a hannayenta dan Ayya ta nada mata da kanta,

Alhinayettt karfe nawa ne zaki je wajen auren? ,
Agaishat ta tsinci muryar Wardugu da bata da siri tana tambayar Alhinayettt dake zaune tsakiyarsu Ayya kuwa na wajen table din diner tana gyara shirin da mai aikinta ta yi mata domin bai mata ba!

A hankali ta sauko, ta karaso tana hangen yanda Mu.azan ke sakar mata murmushi,
Karasawa ta yi sosai kafin take gaisar da su a jimila ta hanyar fadin" Ina kwanan ku,

Alhinayett ta amsata tana yaba kunshinta da harshen buzanci wanda Wardugu ya ji me take fada ya yatsina fuskarsa yana girgiza kai.

Mu.azam ya kai dubansa wajen agogo ya maido wajenta ya ce" Agaishana, yanzu ne safiya, duba karanto min karfe nawa ne? Na ga ko kin gane yanda na koya maki,

Ai kuwa ta juya wajen agogo ta shiga nunawa da hannayenta tana irgawa tana faman fada masa lokacin Ayya ta karaso ta kama hannunta ta ce" a bar y'a na gama shiryata, ita da bata yi safiyar zuwa wajen namiji ba ai ba lale ne ta gane safiya ce ko rana ko yama ! Ayya ta karasa tana murguda baki irin na tsofafin nan masu rigima ta kai dubanta kan Alhinayettt, wato dai da Alhinayettt ake,

Wardugu ya mike ya karasa wajen Ayya, ya kasance sun saka Ayya a tsakiya shi da Agaishat wace hannunta ke cikin na Ayya tana so ta warware mata Lufayar nan ta nada mata,

Sosai ya so rage muryarsa, sosai ya yo yaki da muryarsa ya ce" kin ce baki tsufa ba? Da yaren tubanci,

Juyowa ta yi ta murguda masa baki ta ce" eh da saurana,

Wani tsadaden murmushi ya sakar mata yana dan juya kansa, ya kamo dayan hannun nata cikin nasa ya ce" kin san du duniya ba a yi ba ba kuma za.a yi ba macen da zan so kamar mahaifiyata ko?

Ta kawar da kanta bata bashi amsa ba, ya ce" in dai kina irin abin nan sai in fara tunanin na bani Ayyana ta fara tsufa,

Hannunta ta warce ta dungure kansa kamar yanda takan yi idan ya hasalata ta ce" ni ba wani tsufa ko rashin tsufa bane, ina jin haushin irin yanda kuka dauki al.adar yahudawa kuka mayar naku, tun da safe take gidan nan

Wardugu ya ce" Mu.azam ya gayace mu baki daya mu raka shi ya ga gari,

Ayya ta yi tsam tana kallon sa, Mu.azam ya gayace ku?

Wardugu ya gyada mata kai,
Hannunta ta kai wajen wuyansa ta taba wai ta ji da zafi,
Kalau ta ji wuyansa, ta saki ta dafe habarta da mamaki, ta ce" yaushe mage da bera suka fara shan innuwa daya har shawararsu ta fara zama daya? Me ke damunku? Shirin naku kuma ya fara bani tsoro,

Wardugu ya saki hannun nata yana murmushi ya karasa ya ce" ku fice mu je ta fito idan an gama shiryata, kai yama zaka hada mana fita da karamar yarinya? Yanzu fa dole ka saka mutun ya rike bakinsa gaban yara!

Mu.azam dake biye da shi yana dariya Alhinayettt kuwa da naci ta zauna sai da Ayya ta nadawa Agaishat ta saka takalminta plat, suka kamo hanya Agaishat ta mugun yi mata kyau a idannuwanta, sai ta fito kamar wata chocolate color din balaraba, ta hade ta yi wani sihirtacen kyau

Haka suka karaso suka bude bayan suma suka shiga, ita dai Agaishat kanta a kasa, irin kalon da mu.azam ke jifanta da shi ke bata kunya, sai ta rasa me ya sa yake irin kallon nan,?

Alhinayettt ta mika hannu ta dauko wayar Wardugu ta dawo ta shiga nunawa Agaishat hotuna suna dariya,

Wardugu ya ce" ina muka nufa oga?

Mu.azam ya ce" ka kai mu Bienvenu a Wardugu place,

Wardugu ya taka wani wawan birki, ya kalo shi ya ce" wasa kake?

Mu.azam ya ce " aa can nake son zuwa, yana mai hade rai shima ya mayar da dubansa gefen titi (BIENVENU a Wardugu place, waje ne da mahifin Wardugu ya buda da sunnansa tun suna tare suna ganewa juna kafin abinda ya hada su ya hada su su bar shi da mumunar rantsuwa a tsakani, an ce yanzu matarsa da ya aura take kula da wajen wai ita Aisata ,......mugun tsama ne tsakanin wannan family masu matukar kaunar junansu a da, kuma har yanzu da daya kwal da ya malaka dai Warsugun ne..........).....

🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫

Na *SAJIDA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

2️⃣5️⃣

Wardugu da ya mayar da dubansa gefen titi ya kai hannunsa yana shafa kansa a hankali, tabas Mu.azam yana tako shi kwanakin nan, in sha Allah shi kuwa zai yi iya yinsa dan gannin ya faranta masa...

Motar ya tayar ya dauki hanya, tafiya ce suka yi mai dan tsayi kafin suke karasowa wajen,
Daga mu.azam har Alhinayettt sun yi mamakin yanda ya yarda ya zo wajen,
Mu.azam ya ji wani girman Wardugu ya karu a idannuwansa , kaunar aminin nasa ya linku a zuciyarsa, adu.a ya yi masa da fatan alkhairi ...

Sai dai me, suna shiga da motar suka fara hango wasu abubuwa,
Yan mata ne da muguwar shiga, shiga ta kananun kaya sosai, da samari suna kai kawo suna dan badalar su,

Gaba dayansu kalon wajen suke da mamaki, Wardugu ya jinjina kansa a ransa ya ayanna, *Abinda ka zabarwa kanka kennan Uban Wardugu!*

Mu.azam ya yi tsam ya ce" Wardugu , ko mu juya dai? Domin wajen shi har ya fara bashi tsoro irin yanda ake shiga ana fita ana wasu abubuwan,

Wardugu ya juyo bangarensa, ya saki dan murmushi ya ce" ai mun zo sai kun shiga,

Ya bude ya fice bayan ya dauki hularsa casquette dan baya so kowa ya gane ko waye shi,
Chapter 22 · 0% Book details