← Book details Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 110

Sashe 90

Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read

Juyawa suka yi suka je gaban layin inda Wardugu ya cira kafarsa da Walyn da hannunta ke cikin nasa ta gama wayar da take amsawa suka bi bayansu,
Da farko tsakiya suka saka mijin Alhinayett, daga baya ta bar wajen ta koma bayan su Alhinayett ya kasance su Wardugu da Alhinayett sun sakata tsakiya,

Yau Wardugunma bata iya gaisarwa ba, dan a dan rikice take , fama take su yi su shige, aman ganninta kusa da shi sai ta ji ta samu nutsuwa, ko ba komai ta san idan wani abin ya nufota da yardar Allah zai tare mata, kai ba ita ba, du wanda ke wajen bashi da dar!

A hankali suke takawa, salon kidan ya canza, daga can gefe aka harba bindigar toka ta yi kara sannan aka saki kidan harbin bindiga wanda ya saka du jiki ya kwashi wani tsam,

Idannuwansa a kanta, du wani motsi nata , sannan hankalinsa du a tashe yake, sai dai a fuskarsa ba zaka taba fahimtar hakan ba domin ya hade fuskar tamau ba wani fara.a, hakama yaran nasa ba wani mai isashen sakewa dan kuwa kasancewa a wajen party ba zai hana ya ci ubanka ba idan ta kama!

Yanda tsarin yake sai amarya da angonta sun zauna kafin kowani namiji da ya jero da mace ya rakata har wajen zamanta gefen hagu sannan ya koma gefen dama domin rawar guitar, (sai wanda ya san yanda ake yi zai fahimata🤪🤪🤪🤪🤪),

Amarya da ango na zama suka fara juyawa dan kai yan matan wajen zamansu,

Dan tsai ta yi a lokacin da ta fahimci yanda wajen zaman yake, haka ta juya jiki sabule zata je wajen zaman yan matan ta zauna ita daya,
Bai fi taku biyu da ta yi ba ta ji hannunta cikin nasa, ba zata iya rasa sannin hannunsa bane domin ta gama karantar yanda hannunta ke zama daram cikin nasa,, ta yannayin da jikinta ke nuna mata du idan ya yi irin wannan lamari ya saka ko dubansa bata yi ba ta karantawa zuciyarya shi din ne, a hankali ya kara kusanta kusancinsa da ita ya shiga bin takunta ba tare da ya kaleta ko ya ce da ita ufan ba har suka sauka suka nufi wajen zama,

Suna karasawa ya tsaya wajen kujerar da kanwar Alhinayett ke zaune, wace take facing dinsa ,
Kallonta kawai ya yi da idannuwansa ta mike a wajen ta koma wata inda ya kali yannayin kujerar kafin da hannunsa na hagu ya yi mata nuni da ta zauna,

Cikin nutsuwa ta dago idannuwanta da sukai mata nauyi , nan ta ga ikon Allah ashe du yawancin hankalin mutanen wajen na kansu, tun daga kan sojojin har yan matan wajen, uwa uba Farid da ta gani zaune shima ya yi zuru yana kallonsu,

Da sauri ta zauna tana dan zaro idannuwanta inda ya dan yi tsai , kafin ya rage tsayinsa wajen kunnenta ya ce" Na haramta maki motsawa a nan har sai an tashi!

Du mai kallon su, zai yi tunanin maganar soyaya ake a wajen nan, zai yi tunanin an gama mutuwa a son juna ne, bai damu da kallon da ake binsa da shi ba, hasalima sai da ya dan kara tsayawa ya mike da kyau ya bi kowa da kallo hakan ya sa mutane suke kawar da dubansu daga kansa kafin yake nufar kujerarsa,

Walyn, Walyn, walyn, wani kakausan kallo take binsa da shi har ya gama du abinda yake ya dawo ya zauna a wajensa wato kusa da ita,

Bata dubi tarin mutanen wajen ba, bata yi la.akari da wajen ba bale ta ari kissa irin tamu ta mata ba, yana zama ta shiga magana kamar haka" Wardugu, wannan wani irin mulakanci ne? Meye hadinka da kaskantaciyar yarinyar da muka dauko daga kasurgumin jeji dan cireta daga kangin talauci? Meye daraja a bakar mace har da zaka dauki hannunka mai daraja ka rike nata? Wardugu menene tsakaninka da tsohuwar bazawarar da amininka ya aura ya saki dan ba zai iya zama da ita ba? Wardugu wacece ita a wajenka? Wardugu!

Ta karashe tana mai dan daga murya da wawatsa hannayenta wanda duka na kusa da su na jin abubuwan da take fada da irin dibar albarkar da take tafkawa inda na nesa da su ke hangen Walyn na yuwa Wardugu fada , domin kuwa geste dinta kamar uwa na yiwa yaronta fada ce, irin zazafan fadan nan ma kuwa,

Dubansa ya dago ya dora saman kanta, hauka? Shirme? Aa Raini! Kai tsaye, ido cikin ido, ba wani gargadar murya, ba wani kawar da fuska, ko tausasa harshe Wardugu ya ce" kina son ki san ko wacece ita? Ita din *ORRONUR* dina ce.......

Dankari,
Kaka kara kaka
Ku samo ma.anar ORRonur sai na baku wani page😕

Walyn? Walyn! Wardugu!
Agaishat

More comment bilahi🙄🙄🙄🙄🙄

🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫

Na
*SAJIDA*

7️⃣4️⃣

*KUTKALE* (PRISON)

*AURE YAKIN MATA NE*

*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*

daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA* in sha Allah,

........kar ku bari a baku labari.....

Wannan kalma ta daki Walyn a lokacin da bata shirya ba,

Zurbat ta mike daga zaunen da take inda wayar dake saman cinyarta da jakarta suka fadi saman fari kal din careau din wajen,
A lokaci daya gaba daya jikinta ya dauki rawa, ba inda baya rawa a jikinta,
Bakinra ta kara budewa da bila adadin dan yin magana sai dai kawai hakoranta suke hadedewa bakin na rawa lebunanta na marmarmar,

Juyawa ta yi da karfi wajen da Agaishat take,
Kafarta ta daga da niyar karasawa wajen Agaishat din idan ya so idan ta isa sai ta aikata mata abinda ya samu koma menene,
Sai dai me, idannuwanta ne suka rufe ruf,
Bata gani sannan a hankali lumfashinta ya yi sama ya dauke dif, inda ta aniya zubewa a wajen,

Du hankalin mutanen wajen ya yo kanta inda du aka mimike hankali tashe, domin bata karasa kasa ba ya tarota jikinsa ta sume a jikinsa,

Tsai ya yi ya kurawa fuskarta ido, a sumen abin sha.awa da ita, ta yi fayau ta nuna fuskar innoscent,

Dan mayafin da ta yiwa wayo ne yake faman sabulewa inda Alhinayett ke tsugune inda suke hankalinta tashe ta shiga magana kamar haka" War, mu je asibiti, ta suma fa, bata motsi, Wardugu mu kaita asibiti,

Dubansa ya dago a hankali inda take ,
Murmushi ya sakar mata yana dubanta , muryarsa ya rage sosai domin ana faman zagaye su du kuwa da irin tsaron da sojawan ke faman bayarwa da tsare du wani wanda zai yi gigin karasawa inda suke sai wa.inda aka tabatar da kusancinsa da wardugu mai girma ne ake bari ya karasa inda suke, hakan bai hana mutanen dake wajen zaman amaren karasawa da sauri suna tambayar wai lafia? A hanzarta kaita asibiti mana?

Wardugu ya ce da Alhinayett, " Alhi, bafa wani abu na yi mata ba, ke ai kin san ina hakuri da ita ko? Gaskiya ce kawai na fada mata fa,

Alhinayett ta ce" menene ma.anar Orronur?

Wardugu ya lunshe idannuwansa ya kai dubansa inda Agaishat ke tsaye tana so a barta ta karasa wajensu aman an hanata dan gurin faman cakulewa yake sai kacaniya ke tashi kowa na faman a barshi ya karasa ya ga kwakwaf,

Ya dawo da dubansa wajen Alhinayett ya lumshe idannuwansa yana dan shafa gaban goshin Walyn dake kan kirjinsa sume kafin ya ce" *ORRONUR* na nufin *RAINA*

idannuwa Alhinayett ta zaro cike da tsoro ta kai dubanta da sauri kan Walyn, Balaki! Shi ne kalmar da ta fito daga bakinta, ai kuwa da sauri ta mike tana fadawa mijinta a saki hanya a kai Walyn asibiti, domin tana adu.ar Allah ya sa lamarin ya tsaya a iya sumar kawai, kar ta samu mutuwar barin jiki na bugawar zuciya,
A yanda Walyn ta baiwa kishi madaukakiyar daraja a rayuwarta, a yanda walyn ta dauki lamarin soyayar mijinta a zuciyarya da son kai mai girman gaske, a yanda Walyn ke taka tafiarta na rayuwa da izgili da fariwa da neman magana? A yanzu, wardugu , ya ce kau bani gu, Wardugu a yau zata iya kiransa da Masifafe, ohk so yayi ta daga bali, ta jawa kanta ya daki banza, tabas suma ta zama wajibi a rayuwar Walyn a yau, domin da wannan lamari bai razanata ta suma ba, zata tafka haukan da Wardugu zai sumar da ita, ya salam, ya salam, haka kai tsaye? Tabas tana hangen Wardugu zai zama jarumi wajen fadawa Walyn wannan lamarin a duk lokacin ta sani ya bayana, aman bata taba tunanin kai tsaye haka ba? Mata? Me ke yawo da kusoshin kanmu ne? Gashi dai, da darajarta , da girmanta, da dan shakunta da yake ji ta bale ta saka lokaci daya ya janye du wani laka na jikinta! Ribar me ta ci? Ana kishi, kishi halal ne, kowace mace na kishin mijinta, aman kishima ai taku ne, 🤦‍♀,

Da sauri aka bude wajen aka shigo da mota, du wannan tsare tsare haka mijin alhinayet ya take da mota har kusan matatakalar , aka bude motar ,

Mikewa Wardugu ya yi da ita a jikinsa ya samu ya sauka a hankali ya sakata cikin motar,

Bai shiga ba, ya dawo bayan ya cire rigarsa ta saman wato kaki din mai dogon hannu sai bakar body ta ciki ta bayana mai dan gaheran hannu sannan ta tantanke jikinsa baki daya, hakama ya sakata cikin wandonsa ya yi zanzaro da ita a ciki,
Hular kansa ma cirera ya yi, ya koma wajen da Alhinayett ke tsaye ya dubeta ya ce" ki zo mu je,

Da sauri ta juya dan dauko jakar Walyn da wayarta, har ta bude ta saka cikin motar ta ji muryarsa ya ce" ita fa?

Ba sai ta tambaya ba , ta san wace yake nufi , dan haka ta karasa kusan Agaishat ta damko hannunta kawai ta janyota suka nufi motar inda shi ya shiga gaba su kuwa suka shiga baya suka zazauna,

Gudu yake da motar, baka jin komai sai kuryar Agaishat tana ta tamabayar abinda ya samu Walyn, me ke damunta? Me ya sameta ? Bata da lafia ne? Ko gurdewa ta yi? Alhinayett ki bani amsa mana? Dibi fa ta suma fa,
Chapter 90 · 0% Book details