← Book details Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 110

Sashe 80

Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read

Ido ya zaro yana duban Sarki, shi bashi da damuwar wai mutanen wajen su ji abinda ya aikata, shi damuwarsa hangen daya daga cikin wa.inda suka bashi kudaden su Mariama da ya yi, ya tabata idan sarki ya kore ahi daga Timiya ya kade, dan haka ya gyara rawanin kansa ya shiga bada labari kamar yanda Anna ta bada har zuwa ranar da zai tafi da ita inda ya ce" a ranar safiya na yi na koma wajen bokana, wanda yake anguwar Talagué pays ba, ina zuwa na karbo abubuwan da na bashi ajiya domin ni ke kai masa abubuwa shima yana neman kudi da ni, inda ya dora ni a hanyar da zan hadu da yar masu kudi,

Maganin cire ne, wanda hasalij kirana daga garin haihuwana wato tanut dan ina yawan ciren yayansu,

Dakatar da shi aka yi ta hanyar tambayar menene cire?

Dago da kansa ya yi ya ce" Cire, wani asiri ne da fulanin daji ke yi , wanda na gada wajen kakana na wajen mahaifiyata dan shi filo ne, cire asiri ne da idan aka yiwa mace take bin namiji , bata da wani ra.ayi nata sai nashi,
Na hada da cire da asirin da bokan ya samo wajen wani bokansa dan dogon dutsi cewar idan na aikata idona idonta an kare zata bi ni ne du inda zan je, kuma ko me zan mata ba zata iya barina ba dan zatana jin tsoron zuciyata da bacin raina , sai dai kar na yarda ni da bakina na ambata mata sunnan garin su , ko sunnanta na asali, ko na yan uwanta, in dai ba ni na fada ba koma wa zai fada sai dai ya shiga tunani kamar ta san abin aman ta watsar daga baya dan zai tayar mata da hankali sosai

Na ci sa.a na cireta, muka fice a gidan daidai salar azahar muka dauki hanya da kudaden jakarta inda na yi wurgi da wayarta muka dauki yawon duniya,
Masalatai sun fi a kirga na je dan a aura mana aure, aman sai su ce koda bamu da kowa a duniya sai sun yi magana daga su sai ita, daya na amince sun fara maganar na ga sai wani tambayoyi yake yana faman tona asirina na bige shi da sadanta na dauketa muka kara shiga yawon duniya kafin daga baya na yada zango a nan,

Zufa ce ta shiga karyowa Gaishata, sarki kansa ji ya yi lumfashi na neman gagararsa,

Gaishat bata san lokacin da ta ce" kana nufin ba.a daura aurenka da matarka tsawon zaman da ka yi da ita harda hayayafa ba?????

To fa

🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫

https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp

*☀IDAN RANA TA FITO WRITER'S ASSO🌤* ____________________________________________

*Fad'akar da al'umma tare da nishad'antar da masoya shine fatanmu*😘🤝🏻😘

Na
*SAJIDA*

6️⃣7️⃣

Sai da ya gama murmushi ya shafa gemunsa ya kara kafin ya ce " Elhaj, ai fure ce, zan so na yi mata yayafi,

Wardugu ya rintse idannuwansa, kansa ya kawar kafin yake ajiye wayar ba tare da ya kasheta ba,

Jikinsa ya matsa ya jinginar da jikin kujerar da yake kai, idannuwansa ya lumshe yana mai jin wani tukukin tashin hankali na taso masa daga zuciyarsa yana yin sama,

Idannuwansa ya rintse irin ruf din nan ya shiga kokowa da zuciyarsa, aman ina ya kasa ba zai iya ba!

Mikewa ya yi rai bace ya dauki kys din sa ya fito yana gannin garin ya yi duhu sosai ,

Motarsa ya shiga ya bale da gudun gaske ya yiwa gidan Ayya tsinke,

Yana karasawa ya fice a motar kys dinsa a hannunsa ya nufi falo dan ya tabata irin wannan lokacin suna zaman falo ne

Yelemin kuwa, suna zaune Ayya na yi mata dankwashi ita kuwa tana zuba shagwabarta ,
Jikinta doguwar riga ce har kasa sai dai irin yadin nan ne mai likewa a jikin mutun ko ya ka motsa zaku motsa tare ne kuma komai rashin kabrin jikin ka zayana nuna motsin halitar jikinka, tana da irin rigunnan da yawa dan yannayin zafi Ayya ta kwaso mata a lokacin da akai mata aure.

Da katon takalminsa ya shigo falon domin bai riga ya cire takalmin da kayan dake jikinsa ba ya samu kiran Elhaj Mubarack,

Haka ya takawa Ayya capet din falonta, abinda ta tsana a rayuwa , dan haka da mamaki take dubansa dan shi ne mutun na farko da zai fadi bata son a shigo mata daki da takalmi, hasalima shi din ma ya tsani hakan a rayuwarsa,

Takim takim yaa tunkaro su inda suka dago su duka suna binsa da kallo har ya karaso gaban table din kwalbar dake gabansu mai dauke da ruwa da jus
Yana zuwa ya zuba kys din hannunsa da garaje saman table din hakan ya saka suka bada wani kara tamkar zasu fasa table din,

Hannunsa na hagu ya doro saman table din, da na dama kuwa ya dago yatsansa na kusa da baba ya nunata ya ce" ke , daga yau, daga rana mai kamar ta yau, na soke du wani shige da ficen ki a shigar da ba nikaf, hijab dogo da safa, idan kuwa ba haka ba sai na babala ki Agaishat!

Ya karashe yana mai daga muryar da ya saka ta mike tsaye da sauri ,
Mikewar da ta yi ya ainahin girgiza jikinta da karfi domin irin mikewar tsoracen nan ce,

Ido ya zaro ya ce" ba ga irinta ba! Ba ga irinta ba! A ce yarinya baki da kimtsi sai tsale tsale da guje guje da juye juye a gaban ko wani karamin dan iska? Ke ko kunya bakya ji zaki fito da wani mayafi mai kama da rariya ki wani zo kina juyi gaban madubi? Ke ke......
Da haushi haushi ya nufeta da niyar gaura mata mari domin a tsaye da take baki ta turo tana kikifta masa ido, wanda hakan ya kara hautsina masa lisafi

Ayya da ta yi mutuwar zaune cike da mamaki, da kuma darsuwar vakon zargi a kan tilon dan nata game da yar amanarta ta yi sauri cewa" walahi ka dakar min y'a sai ran ubanka ya baci Wardugu!

Ja ya yi ya tsaya, a hankali ya juyo wajen Ayya ya ga ta mike tsaye, kansa ya sada ya karaso kusa da ita a hankali kafin ya ce" Ayya, ya zaki sakawa yarinya ido tana fita da mayafi dan Allah?

Ayya ta ce" Wardugu, auren wani ke kan yarinyata ko bakon abu ne fita da mayafi a matar aure ma bare wace bata da aure? Ba wani shigar tsiraici take yi ta fita ba, aman idan ka saka mata irin dokar nan ba zan dauka ba !

Wardugu ya dago jajayen idannuwansa ya ce" Ayya, sai ta fita da dan mayafi zata samu miji ne? Wani irin miji take nema a rayuwarta ne? Shin ba karatu kika ce tana yi ba? Dan Allah du yanda za.a dagawa mutun hankali an sani? Yaya kuke so na yi ne?

Ayya ta kwalalo idannuwanta kafin ta tafa hannayenta ta ce" Warsugu wani laifi muka yi maka ne?

Wardugu ya yi shiru ya tsurawa cafet din falon ido, can ya fago idannuwansa ya sauke saman fuskar Agaishat dake tsaye tana dubansa, idannuwan su ne suka sarke da juna, kallon second 5 , idannuwan Wardugu jajaye jir da su tamkar gauta, sai dai da wasu yan kwala da ba zata iya kiransu da kwallah ba sai dai tace da su na bacin rai, wani irin kallo mai nauyi, mai tafe da sakwonni, mai dauke da ma.anoni ne ya zuba mata a cikin maraitatun idannuwanta da ta yi tsai ta jefe shi da kallo mai tura sakon *Ka ji tausayi na*,
A hankali ta lumshe idannuwanta ta ji wani irin sulbi a cikin idannuwan nata sannan suka fara rawa sanadiyar irin dokawar da zuciyarta ke yi du idan ta yi arba da shi,

A hankali ya taka ya nufe ta, wanda du takunsa ke barazana da tunanin kwakwaluwarta har ya kasance tunanin ya tsaya cak, ba wani sauran abinda ke aiki a cikin kwakwaluwar nata sai tarin kwalar da ta cika gurbin idannuwanta a hankali ta shiga zubowa,

Kure mata waje ya yi, ya shaki kamshin turarenta,
Idannuwansa ya lumshe ya kai hannunsa ya riko nata , riko na ya riko hannun kanwarsa, riko na ya kamo hannun kanwar sa dan ya jadada kashedinsa a gareta,
Sai dai laushin su ya saka shi dago da hannun da kyau ya bude idannuwansa ya tsura masu ido,
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yake daga dan yatsarsa ya ce" ki bi dokana ki tsira, idan ki ka kiya zaki saka mu a uku ne, dan zan farauce ki a duniya ne, zan yi maki farautar kwai ne, Agaishat ki rufa mana asiri ki bamu lokaci, ki rufawa Ayyanki asiri kar ta yi zaman jinya !

Yana gama fada ya juya ya dauki kys dinsa ya juya yana tafe yana hada hanya ya fice a fallon,

Kuka Agaishat ta fashe da shi wanda ya farfado Ayya daga uwar sumar mamakin abinda ya faru da raka Wardugu da ido da ta yi,

Da sauri ta nufi wajen Agaishat ta kamota ta ce" ke Agaishat, menene? Tsoro kike ji ko? Kar ki ji wani tsoronsa in sha Allah ina tare da ke ba abinda zai yi maki!

Agashat ta rike hannun Ayya da kyau , da kyar ta bude bakinta ta ce" Ayya zuciyata ke bugawa, Ayya jikina rawa yake min, Ayya wayo zuciyata gabana ke faduwa du idan na ga yaya Wardugu, Ayya ciwon zuciya ne nake ko????

Shiru Ayya ta yi itama gaban nata ya fadi, kai ina! Aa ba su ba, menene haka? Me ke shirin faruwa ne?

Wardugu na komawa gidansa bangaren Walyn ya nufa,
Kai tsaye ya ritsata zaune tana kallon film a nollywood hankali kwonce,

Hannunsa ya saka ya mikar da ita, a hankali ya jata jikinsa ,
Idannuwansa lumshe ya lalubo lebenta jajir ya kai masu lalausan harshensa ya shiga kissing dinta passionately,
Chapter 80 · 0% Book details