← Book details Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 110

Sashe 34

Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ta rungume shin itama, ta shiga sauke ajiyar zuciya tana shakar turaran jikinsa wanda koda ya yi zufa bata hadewa da turaran ta bayar da wari wari, turaran ke cin karfinta bama zaka gane ba sai dai idan mafi kusanci da shi ta ji gishiri gishiri a jikinsa a irin wannan yannayi 🤣,

Gajiya ta yi da tsayuwar domin daman ba wani karfin jikinta take ji ba,

A hankali ya bita saman kujerar domin shi a wannan lokacin bashi da bukatar komai sai na ya jima a jikinta , ta rungume shi, yana so ne kawai ya ji shi a jikinta ba komai ba,

Haushi Walyn ta ji, aa me wardugu ya dauketa ne? Jiya ya gama wulakantata, ya fanshi jikinta, ya tashi ya yi tafiyarsa, ta je saloon ta kwashi rashin mutunci dan shi, ta zo gida mata na wawarsa shi oga! Yanzu ya kuma dawo mata da bukatar sa? (Domin a tunanin ta , bukatuwa ce ta dawo da shi a irin wannan lokacin ),

A hankali ta zame jikinta tana dubansa yanda ya yake ringeshe jikin kujerar idannuwansa du a lumshe,

Baki ta dan yatsina, a fili ta ce" ka san yau a saloon wata karuwa ke ikirarin sai ka aureta?

Daga yanda yake kwonce yake dubanta, a hankali ya ce" ki zo gare ni Walyn.....
Ya mika mata hannunsa,

Kafadarta ta make irin na yangar nan na mata ta ci gaba da fadin" ka saurare ni mana, ina maka hira ka wani basar,

A hankali ya kai hannunsa wajen goshinsa kafin yake mata alama da ta ci gaba, domin ya lura kwata kwata matar tasa bata lura da yannayinsa ba, bata da niyar fara sauraronsa, zata tiso abinda ke damun nata wato *kishi da isa*,

Zamanta ta gyara tana mai dubanda da kyau ta ce" ni kuwa na bata amsar cewa , Wardugu mijin mace daya ne, ba zai kula wace ta san mutuncin kanta bama bare ita karamar yar bariki, Wardugu nawa ne ni kadai!

A hankali, ba tare da wani damuwa ba ya ce" *wa ya yi miki wannan albishir?*,

Da sauri ta dubo shi, da yannayin mamaki ta ce" me kake nufi?

Dagowa ya yi yana dubanta ya ce" *Auten zobe muka yi da ke?*,

Walyn ta kara zabura da mamaki ta ce" kana nufin sai ka kula wata macen?

Wardugu ya buda idannuwansa da kyau, ya ce" *To waye ni?* , an fada maki ni ba mutun bane? ,

Yanzu sai ka ci amanata Wardugu? Sai ka dubi wata macen da sunan so?

Kallon kar ki raina min wayo ya yo mata sannan ya ce" tunda hirar kike so mu yi bari ki ji, da farko dai ni mutun ne dan Adam wanda nake tara ba goma ba wanda nake cike da laifuka , nake dauke da zuciya mugun nama, wanda na kwonta da sannin Allah ya halasta min auren hudu na jera, nake da sannin ina da wajen saka su, ina da abinda zan ciyar da su, na tufatar da su, sannan ....ya yi murmushi ya ci gaba da fadin" na sauke hakinsu saman lit (bed) ba tare da gajiyawa ba! Ke kin san wa kike aure shi ya sa kike kishi! To a haka da nake, akoy wa.inda ban yi masu ba, sam bana gabansu, bana cikin tsarin da zan samu koda gaisuwarsu ne! Walyn, ana aure dan soyaya, da tausayi, dan sha.awa, dan arziki, ba zan maki karya ba, ba zan yi maki rantsuwar ni na isa na kauce kaina daga kan *mace yar dagwas dagwas mai dorinar dukan maza ba* , ciki kuwa koda yar barikin ce da kike fadi mai yiwuwa na zama silar shiryuwarta!

Gaba daya har Walyn ta fara fita a hayacinta , ta hayayako ta ce" me na gaza da shi Wardugu da kake kiran min sunnan wata a gabana?, *Kyau, fari, tsafta, girki, iya tarairayarka,* wane na gaza a cikin nan?

Haushi ya kara kama shi, itace ke ikirarin iya tarairayarsa bayan yanzu ya shigo mata a wani yannayi maimakun ta dubi halin da yake ciki ta zauna a kusa da shi aa, sai ma ta tsankalo kabarun banza da wofi, kai da Walyn a wajen aikinsa take kai koda ficewa take ta hanyar da an kwashi yan kalo da ita da matan dake kai masa ziyara, wai kuma ta yi ikirarin ita ta san kanta ita mai kyau me memememe, *Isarta* ta hanata ta duka masa yanda ya dace, takamarta da halitarta sun hanata gane ainahin biyayar aure, sai idan baki ya bude ta shiga zubo masa abubuwa mararsa tsari, dan haka da yannayin haushin nan ya mike yana daukan rigarsa ya ce" *Kin san dadin miya ke sakawa a yi kari!*

Wai wai wai wai , shin fans zaku kuwa iya zama da mai hali irin na wardugu🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀,

Su waye wardugu ke ikirarin ko arzikin gaisuwa baya samu daga wajen su? Me ke damun wardugu?

Me ke damun kwakwaluwar Wakyn? Ta hada kyau, fari, tsafta, kanshi, girki, bata isa ta daki kirjin mijinta na ita kadai bane?🤔

Mu.azam, zai kai labari kuwa?

Agaishat Ayya, Anna, Ba, Marahut, ya labarin su ne?🤔🤔🤔

🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫

Na *SAJIDA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

3️⃣6️⃣

Rigarsa ya rataya a kafadarsa, ya juya da niyar barin mata bangarenta domin bai ga dalilin fa zai saka a caza masa kwakwaluwa a waje, ya zo wajenta dan samun nutsuwar zucuya itama ta caza masa, yana bauwa Walyn damarta ta mace, na ta yi korafi a kan abinda bai mata ba, ya sha duba korafinta ya nuna mata ya tuba a aikantance ta hanyar daina abinda ta kawo masa korafin a kai, sai dai abubuwa na damunsa na irin yanda ita ba abinda ya sha kanta da damuwa da damuwarsa, bata wani damu da yannayin da zata ganshi ba indai da abin fada zata rufe ido ta fada da gatsali,
Murmushi ya yi yana girgiza kai bayan ya kare mata kallo du ta fice a hayacinta daga wannan yar maganar? To idan Allah ya kadarto min kara aure yaya zamu kwashe da Walyn?

Rai bace tana kokarin fashewa ta kuka ta ce" Wardugu, idan ka yarda, idan ka saki, ka yi saken kula wata mace sai dai a kwashi gawarwakin mu baki daya! Wardugu kamar yanda Batuben namiji zai iya suka da wuka dan an kali matarsa toh zan iya suka da wuka dan an rabe ka!

Tsayawa ya yi yana dubanta, iya gaskiyarta ta fada domin a tsaye take tana dubansa ido cikin ido, jikinsa ya ji ya dan yi sanyi, karasawa ya yi kusa da ita , ya dan sasauta murya aman a cunkushe ya ce" Walyn, bakya aiki da adini ne ke? Kin san da sunnar ma.aiki ce? Me ya sa zaki daukarwa kanki zafi haka? A haka Walyn ban ma nuna zan yin ba idan zan yi fa?

Idannuwanta ta dago dan sakawa cikin nasa domin ya darata tsayi, ta ce" na tsinci kaina a zazafar kaunarka, haka na wayi gari na ganni zundum , na shanye wulakanci kala kala dominka, kai da kanka ka sha wulakanta ni mai girma, karaya uku ka min a gabai na, du na shanye! Kai a tunaninka ba zan shanye azabar kawar da du wata tsagerar da ta tunkaroka ba? Wardugu, mahaukaciya ce ni a kanka! Sakara ce da a yaren ka! , kamar yanda ka sumar da saurayin da ya yaba maka ni, ni kuwa ka yi min marin da na yi ta ihu sai da kyar jina ya dawo dan na yi kwaliyar da aka yaba ni, haka zan iya rike makigwaron du wata yar iskar da ta yabe ka!

Kansa kawai yake dan girgizawa yana dubanta, Walyn, walyn Wardugu...ya saki murmushi ya juya,

Haushi ya kara rike mata zuciya ta daga murya ta ce" ciki kuwa harda wannan tsohuwar kilakin da ta ki aure take binka gida ma.aikata, anguwa! *Alhinayett*, ciki harda ita,

Dawowa ya yi ya tsura mata ido, kafin yake fadin" ki daina zagin Alhinayett domin mai son ki ce, tana yaki kan ki, tana yi min fada kan ki,

Karuwancin kennan! Karuwancin kennan Wardugu! Ta shiga jikinka har ka ji in ba ka kasance da ita ba , ba zaka ji nutsuwa ba!

Wardugu ya zauna saman kujerar dakin ya ce" Walyn, Alhinayett ba yar bariki bace, mutun ce mai daraja, mutunci ne tsakanina da ita, ke kin san da soyaya ne da tuni na auri abina na kilace, jimawarta ba aure kuwa Allah ne bai kawo lokaci ba, aman an kusa saka aurenta, ki daina magangannu irin haka Walyn , ke macece, ko a kan ki ba haihuwa zaki yi watarana, ba.a so mutun ya cika izgili,

Kai ta kawar ta ce" wardugu, gaskiya ne baka so? Alhinayett ai kowa ya san kilakin ka ce!

Wardugu ya mike a karo na uku kennan, ya karasa kusan Walyn yana mai binta da kallo, hannunta ya damko ya bude yana dubawa, ya riko fuskarta ya daga idannuwanta yana dubawa, ya gwale bakinta ya saka yatsunsa ya ciro harsanta yana dubawa, ya saki ya kama rigar dake jikinta ya dage sosai har biyu suka bayanna, nan ya tsura masu ido yanai masu kallon kurullah,
Cikata ya yi , ya dan taka ya tako kafin yake nunota da yatsarsa manuniya, muryarsa ya saki baki daya ya ce" Ba karuwa bace! Aminiyata ce, du wanda ya zagar min ita zan bata ransa! Kika kuma kiranta da karuwa na rantse da girman mahalicina sai na aureta koda kuwa ta tsane ni , koda mutuwa zata yi dan kina na kawota na kwana da ita saman gadon ki! Ke da ba dan ina hangen kamar mai shigar ciki ba yau da na nuna maki tsagwaron rashin mutunci! Ya ina taro ki kina raina min hankali? Walyn ni in ban kara aure ba ni ba dan babana bane!, ni ba jinin tubawa bane! Walyn dole ki zauna da kishiya in baki kona mu ba ke ba yar babanki ba ce!
Chapter 34 · 0% Book details