← Book details Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 110

Sashe 75

Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read

Saman luntsumemiyar kujera suka hango shi zaune da mai wajen baki daya,
Yau kam shada ce jikinsa mai ruwan maroon , an yi masa tazarce kawai, ba.ai mata adon komai jikinta ba sai kace karamar shada, abinka da an wanku an jiku sai ta yi bada wani samfari a jikin nasa, ga wata hula da ya kafa yar daidai da kan nasa da ra kuma hau da kayan jikinsa,
Kai wardugu mai kyau ne,
Hira suke da mutumen, da alama ba yau ya fara zuwa wajen ba, koma sun san juna ,
Yau baki dayansa annuri yake fitarwa, inda suka tsinci muryar Elhajin na fadin" Oga, ai sai ka fada min gaskiya kawai zaka gwangwaje ne, kai zaka dauki amarya haka? Gaskiya Oga kana ja,

Wardugu ya yi murmushi yana girgiza kai, daidai sun karaso ya ce" aminiyata ke aure ba ni ba, Alhinayett fada masa ko ya bani lafia,

Yana ganninsu ya juya wajen yaronsa ya ce" kai Idrissa, zo kakabe kujerun nan maza, ai ko yanzu aka ciro su a leda sai an goge domin hajiyoyin ne da kansu,

Alhinayett kawai ta yi murmushi tana duban wajen da za.a goge masu wai, wajen sai daukan ido yake a hakama, aman dan da mai ajin suke tare sai suka caje inda suke har aka zo aka goge masu wajen zaman suka zauna,

Gaishe shi suka yi,
Wardugu ya amsa da lfy, kamar yanda ya saba amsa gaisuwa a datse,

Duban Alhinayett ya yi, a kasan ransa kuwa ya ji kamar ya shige su da fada, wai ita ba zata daina yawo da yarinyar nan ba? Ba zata barta a gida ta yi zamanta ba? Han,

Katon albom aka kawo masu aka ajiye,

Dubanta ta kai itama wajen Wardugun da yannayin tambaya,

Wardugu ya ce" ki bude ki zabi wa.inda sukai maki

Kallon kur take masa bata kawar da fuskarta ba dan neman karin bayani ,

Mai shagon ne ya ce" hajia, ai idanma a nan basu yi maki ba sai na yi kira su turo mana sababi ki zaba cikin sati zaki ga kayanki,

Sai da ya gama magana tana dubansa kafin ta maido dubanta wajen Wardugu,

Fuska ya hade ya kawar da kansa,

Ajiye litafin ta yi ta katsa kusa da shi,
Murya ta rage ta ce" Wardugu, me kake nufi?

Wardugu ya ce" ban gane me nake nufi ba? Kayan daki zaki zaba Alhinayett mana, kin san minti nawa na yi a wajen nan ? Ina da taro fa ,

Alhinayett ta juyo da kallonta wajen Agaishat, gani ta yi ita kawai ta tsurawa wata agogo ido mai ruwan dawisu sai kyali take ta hadu karshe,

Dubanta ta maido wajensa, hannayenta ta hade waje guda ta ce" Warsugu, kennan zagin nawa da ake cewar na makale maka wai kawance dan dai na tsotsi abin hannunka ne zai tabata? Wardugu, kayan dakin ka rasa a inda zaka siya min sai a wannan tsadaden shagon da idan ba isa ka yi ba zaka saka kafarka bama koda dan kalo ne? Wardugu Abanna me zai ce? Wardugu wahalar ta isa haka, dan Allah ka rufa mani asiri ka bar maganar kayan nan ,

Wardugu ya zaro ido da mamaki, murya a kausashe ya ce" ni zaki rainawa wayo Alhinayett? Ni zaki fadawa irin magangannun nan? Ni?

Da sauri Agaishat ta juyo da dubanta wajensu, mikewa ta yi tsaye domin ta ga ya nuna Alhinayett da yatsa alamun ransa ya mugun baci,

Muryarsa ta kuma ji ya ce" walahi yau da wata ce ta mani irin haka sai na dauke mata hakora kafin ta karasa maganar, an gaya maki ni sakarai ne mai daukan jita jitan mutane? Ko qn gaya maki idan ban yi magana da Aban ba zan yi gaban kaina? Malama da na kiraye ki ki zaba dan na san halayenku mata da shegen tsare tsare ana iya zabar maki ki ce basu yi maki ba! Ki zaba ku bace min da gani kuma idan na kara gannin wacen ba hijab sai na kade ku!

Hawaye ne ke zubar mata a idannuwanta, wasu na korar wasu, rayuwa kennan, ita ta taba tunanin zata hau irin wannan gadon? Wajen Agaishat dake tsaye tana kikifta ido ta dawo da sauri ta dauki litafin ta mika mata ta ce" zabar min,

Agaishat ta dubeta ta canza harshe zuwa yaran buzanci ta ce" me kuma mukai masa da zai kade mu? Yaushe ne zai kade mun? Kuma muna cikin motar za.a iya kade mu daman? Kin ga Ayya amanata ta baki idan kika bari ya kade ni ke da ita ne.

Alhinayett ta ce" Agaishat kin manta yana jin yarenki ne?

Da sauri ta zaro ido, ran harga Allah ita ta manta da yana jin yarenta, dubanta ta waiga wajensa ta ga yana danna waya, da alama bai jita ba, dan haka ta sauke ajiyar zuciya ta ja Alhinayett suka kara matsawa tana duban har yanzu ta ki yin shiru,
Hannu ta dago tana dubanta ta ce" to wai kukan fa?

Alhinayett dake shasheka ta ce " Agaishat, wai na zabi kaya fa yace?

Agaishat ta ce" to menene?

Alhinayett ta ce" Agaishat, ba zaki gane ba,
A wajen nan kayan masu tsada ne na yayan gata, sun fi karfina, ni wa? Yar wa?

Agaishat ta yatsina bakinta wanda du idan ta yi sai dimple dinta ya loma, ta karbi litafin ta shiga dudubawa,

Hankalinta kwonce ta kallo tana ta santi a ranta, a fili ta ce" kin ga ni na rikice, karbi ki zaba,

Alhinayett ta karba ta ja hannun Agaishat har gaban Wardugu dake dan zantawa da Elhaj, duda ransa a bace aman yana amsa shi,

Suna zuwa Alhinayett ta ce" War?

Wardugu ya dubeta bai bata amsa ba,

Ta ce" ka yi hakuri, na tuba👏🏻,

Idannuwansa ya dan lumshe ya bude a kansu,

Alhinayett ta turo Agaishat gabansa, irin sosai ta matso kusa da shi domin turota ta yi da biyu, ta ce" Agaishat, ki taya ni godiya wajensa, bani da bakin gode masa ki kama mani,

Agaishat ta zaro ido ta juyo da dubanta wajen Alhinayett , kafin take juyawa kusa da shi,
Kamshin turaransa ne ya saka ta fara jin wani irin dadi a ranta,
Wardugu dake kallon kasa kasa ya shiga wani yannayi na jinta gashi gata,

Agaishat ta shiga kame kame tana dan shafa gaban goshinta,
Dago idannuwansa ya yi ya zuba mata saman fuskarta, yanda take shafa fuskar tana dan waige , tana kuma kallon wajen da yake abin sai ya saka shi nishadi, irin ta daburce ne? Ai kuwa sai ya saki murmushin da ya nuna fararan hakoransa,
Yan wushiryarta ne suka bayana na sama wajen hakoranta biyu da suka dan yi kasa kamar na zoma sai dai basu fito sosai ba sun bada wani kala mai birgewa da tsari ne, suka bayanna, ta lumshe manyan idannuwanta ta bude ta ce" Mun Gode, Allah ya kara arziki, Allah ya kare ka a duk inda kake, ya baka kaima masu yi maka domin Shi👏🏻,

Bai iya amsata domin yakan zama wawa a duk lokacin da suka samu kusanci irin haka, shi ya sa ya daina yawan zuwa gidan Ayya, domin a gidan Ayya wani lokacin yana tarar da ita tana zuba tabara shi kuwa uwa wawa sai ya saki baki da ido yana rakata da kallo yana sakin murmushi 🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀

Paris

Alhamdulilah, jiki ya yi kyau, a hankali har ya fara dan fita daga gidansa yana gannin gari ya koma,

Khadija dake fama da shi ta fara kosawa kan maganar aurensu aman abin mamaki ya nace aa, ba yanzu ba, shi ba zai iya auren da ba Wardugu ba, shi sai wardugu ya aminta zai iya auren ko wace mace!

Takan ji takaici da gannin bai san darajarta ba, sai ta nuna ta yi fushi , sai ta kasa ta dawo ko dan ya ci abinci dan idan bata nan baya ci!

Kamar yau yana zaune yana kallon fulawowin tsakar gidansa,
Iska mai dadi na busa shi ya.....

🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫

https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp

*☀IDAN RANA TA FITO WRITER'S ASSO🌤* ____________________________________________

*Fad'akar da al'umma tare da nishad'antar da masoya shine fatanmu*😘🤝🏻😘

Na
*SAJIDA*

6️⃣6️⃣

Kai jama.a ni dai wollah Azumi🙄🙄🙄🙄

Iska mai dadi na busa shi yana mika hannunsa a kai a kao yana dan tsigo fulawar ya sinsina hat sai ta yi laushi sai ya zubar ya kuma tsinko wata,

Tsaye take bayansa tana dubansa, ta dan dauki lokaci kafin ta juya ta shige gidansa ta dauki wayarsa ta dana masa kira,

Ya jima, kai harma ta cire rai da zao daga domin ta kira ta kara bai daga ba , da kyar dai ya daga bai yi magana ba sai dan hayaniyar muryar Alhinayett bakinta ya kasa rufuwa dan murnar abin alkhairin da ta samu na aurenta,

Salama ta yi a hankali na wajen uku kafin yake amsawa shima,

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce" Wardugu Khadija ce,

Wardugu ya ce" na gane,

Khadija ta yi tsam ta ce" Wardugu kun san gaba ta fi kwana uku salar mutunma ba.a karba?

Wardugu ya ce" eh na sani,

Khadija ta cire wayar da mamaki a kunenta, kafin take maidawa ta ce" kun sani aman kuke yi?

Wardugu ya ce" ke din wa ya baki damar kirana ki min tambaya irin haka? Ni mace ne da zan tsaya gaba da wani?

Khadija ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Dan Allah ka yi hakuri, baya jin maganar kowa idan ba taka ba,

Me saurayin naki ya yi maki? Ya tambayeta kai tsaye,

Wata kunya ce ta kamata, kennan ya san halin da take ciki ko me? Ai tunda ya sani bara kawai ta fito a mutun, ta ce" Wardugu, ya ki maganar aurenmu, yana irgawa Agaishat ta fita a ida, wai shi sai ka yafe masa, dan Allah ka yi wani abu, idanma hada mu za.a yi a yi auren ni da ita in dai zaka yafe masa dan Allah ka yi,

Idannuwansa ya rintse, ya jima kafin ya bude ya furzar da wata iska ya ce" haka yake tunani ko tunanin ki ne?

Khadija ta ce" neman mafita nake,

Warsugu ya girgiza kai yana murmushi ya ce" ki iya da shi kin ji?
Chapter 75 · 0% Book details