← Book details Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 110

Sashe 74

Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read

Tsai ta yi ta tsura masa ido,
Tunda suka yi aure ya kasance cikin tsaf tsaf, ko dan sun raba bangare suna haduwa lokaci zuwa lokaci ne? Ba zata ce ga ranar da ta ganshi da kazanta ko ta tarar sumar kai ce ko saje bale jiki,
Yana da kula da adininsa, baya wasa da sallah da ibadun da yake a bayanne da wa.inda yake yi a boye,
Yana da fitina, rigima, tashin hankali aman fa idan an shiga hanyarsa, tabas bashi da saurin hadiye wulakanci ko.na waye, aman yana da kawar da kai, abinsa ba zai hada ka da shi ba, uwa uba mijinta tsarare ne, Allah ya yi halita mai nitsa zuciya , ko a cikin kawaye idan aka tashi maganar dogon yaro ga fari ga farin jini ga yayan banki sai an fara ajiye masa gaisuwarsa kafin a hangi wani dan tafe yake da zamaninsa, sai dai kash zuciyar nan tasa na tayar mata da hankalinta, zata so ya zama yanda take son ya zama, da ta yi ihun ta more miji,

Kafa ta saka ta fice a falon , bata wani damu da irin zamansa, da dalilin zaman ba, ita dai abinda ta saka a ranta zatana zuwa ta kawo masa kanta, ya samu nitsuwar da ba zai dubi wata y'a da wannan muradin ba, sauran zata ji da su , dan ita dai ba aikin fari take ba na baki ba, tana kwashe salarry kafin a yiwa ma.aikatan gwanati biya, tana shiga babar mota tana zuba zinaria ta saka shada, damuwarta Wardugunta, zako ta ci uwar uban du wata mai rawar kan da zata rabar mata miji!

Basa zama a kwanakin nan,
Shirye shirye suke tun karfinsu,
Ba wai wani yawon kaiwa yan mata cati ko wani gayace gayace ba, aa siyaya ne suke a hankali na abubuwan da zata bukata a gidan miji inda matar mahaifin Alhinayett ke saka su a hanya da zuciya daya tana mai basu kyawawan shawarwari,

Ayya kam ta hakura da jajen ita gaskiya a bar fitar mata da y'a gannin fitar da y'ar nata na kawo ci gaba ta hanyar kara iya mu.amala da mutane kala daban daban da take gani a wajen siyaya ne, a saloon, da wajen gyaran jikin da Alhinayett ta biya suke zuwa tare a yi masu dan kuwa itama tsale ta yi ta dire kan tana so ,

Sukan tsalake kwana biyu basu fita ba, idan aka ce zasu fita kuwa Ayya kanta har mamakin itin tsararen shirin da y'ar tata ta koya,
Ta iya saka kaya masu saka jiki a nutsuwa, ta fi nacewa atampopi dinkunnan dogayen rigunnan zamani masu tsari irin na yayan yan gayu ba masu fitar da tsiraici ba,
Wani sa.in takan zurmuka hijab dinta a saman shigarta mai kyau da birgewa, wani sa.in kuwa sai ta yafa dan gyalenta ,

Idan ka ganta ba zaka taba kawowa ta taba aure ba, hakan ya saka du fitarsu sai ta samu mai tayawa dan ba karya dorinar kyau ne da ita ga dorinar ado, kaya saka su kawai take su yi mata das ba ciko ba acuci ko daya.

Alhinayett na lure da irin kokarin da mahaifinta ke yi, dan haka ta kwatanta zuwar masa da shawarar tana da yan kudadenta a banki, idan ya amince ra kawo ya kara ya yi mata gadon, sai dai ya yi murmushi ya ce" Alhinayett, ke dai Allah ya yi maki albarka irin dawainiyar da kike da mu baki daya, aman ba zan amshi kwandalarki ba, zan yi kamar yanda na yiwa kannun ki, ki je kudaden ki ki kara abubuwan nan naku na zamani na gayu ,

Haka ta mike ta yi godiya ta fito, itafa tausaya masa take domin nauyi ne ba kadan ba a kansa, gashi da y'aya mata masu cikuluftun yau a sayi kaza gobe a sayi kaza, gashi dangi na kauye du a kansa suke, ta so ya karba ko ba komai zai rage wasu abubuwan aman ya kiya gashi aure har sauran sati biyu,

Zuwa ta yi dakinta ta tsala wanka ta saka abayarta baka sannan ta daura nikaf a fuskarta ta fito ta yiwa yan gidan salama kan zata je wajen gyaran jiki da karbo dinki da kai wasu dinkunnan, wai a nan du irin tarin suturun da take saya ne , lefe an ce sai gobe za.a kawo,

Tuki take hankalinta kwonce a yar karamar motarta ta nufi gidan su Wardugu dan dauko kawalin nata wace take kanwa a wajenta kuma kawar shawara dan a duniya nitsuwa da hakuri Agaishat ya saka ta aminta da ita,

Tana tsayawa ta bude ta fito sai jin karan shigowar messages ta yi a wayarta rututu,

Dakatawa ta yi ta bude pos dinta ta ciro wayar inda ta maida hankalinta wajen tagar Agaishat tana hangen ko zata ganta ta nuna mata ta zo fa,

Tana buda wayar ta shiga, wata sabuwar number ce ta Niger, dan haka ta shiga cikin messages din,
Hotunnan ne , hotunnan gadaje, kujeru, table din tv, na tsakar daki, na cin abinci, show glass, kowane da katon tambarin katon butik din da ake siyar da su, irin kayan wajen nan ne,

Murmushi ta yi tana fita a wajen ta ayanna a ranta yo wannan ko gidanmu za.a siyar ba zai kai kudaden wadinnan kayan ba, ni me ya kai ni?

Murnushi ta yi ta shiga gidan,
Ai kuwa ta shirya cikin wata doguwar rigar atampa A yi mata dinkin mai dogon hannu aman a bude sosai dan kuwa du hannun ya cinye sauran atampar,
Ta yi daurin dan kwalinta da irin carto din nan baki, ta dan fitar da yalwatacen gashin kanta daga kasan dan kwalin,
Kunnenta dauke da yan kunayen azurfa mararsa nauyi da fadi sai dai tsayi,
Hannunta dauke da dan zobe karami na azurfar shima,
Fuskarta ba wata kwaliya sai dan kwalin da ta saka sai lebenta na kasa da ta shafawa dan jan baki kalar ja aman ta murje shi ya kasance kadan ne ya fito a jikinta,
Kamshi take bazawa ta dora kafarta ta dama saman ta hagu tana dan kadawa ta cuno baki wai Ayya ce ke fadan bata son saka takalma masu dan tsayi ita kulun sai plat kamar wata tsohuwa wanda ko ita Ayyan na saka mai tsayinta idan ta yi ra.ayi, dan haka ta karbe katon hijab din da ta dauko da takalmin ta koma ta dauko mata wani mayafi fari kal mai shara shara da takalma masu dan tudu farare da pos fara kar mai igiya yar doguwa ta dawo tana fadan sai kace wata datijuwa ta wani kinsima hijab kulun kulun? Ke da nake so kema na wanke ki abina na maki aure mai sunnan aure?

Alhinayett ta yi dariya tana kallon yanda ta daura takalman a kafarta tana cuno baki ta dauki pos din ta saka wayarta a ciki kafin take juyawa wajen Ayya ta sakar mata murmushi ta ce" Ayyana, ni ba zan yi auren ba, na hakura da auren, kin ga ba kin mini auren ba aman na dawo maki? Kawai mu yi zamanmu ,

Ayya ta gala mata harara ta kawar da kai irin ta shakan nan bama zata bata amsa ba, dan haka sukai mata salama ta bi su da adu.a suka fice a motar Alhinayett din.

Tafe suke suna dan hira inda wakar guitar ke tashi kadan kadan a motar suna bin mawakin Buzun mai sunna Bombino bisa wakarsa ta *Arakkham nah*,

Wayarta ce ta dauki kara dan haka ta samu waje ta dan tsaya,

Tana dagawa ta ji yana cikin kayaniya dan haka bai tsaya sun yi wata doguwar gaisuwa ba ya isar mata da sakon inda zata tardo shi yanzu yanzu ,

Da to ta amsa ta datse kiran tana duban Agaishat ta ce" Wardugu ne, yace mu tarda shi shagon nan na siyar da kaya yanzu ko lafia?

Agaishat ta tsura mata ido bata ce da ita komai ba har ta tada motar ta dauki hanya, Agaishat kam na so tace da ita dan Allah ta ajiyeta ta je ta dawo sai dai ta san bama zata saurare ta ba , dab gaja ta tsurawa hanya ido,
Ita ba komai ke rikitata ba sai irin yanda gabanta ke faduwa idan ta hadu da shi, ko dan ya cika fada ne? Wani lokacin yana da saukin kai, aman yawancin lokutan ya cika fada da daure fuska, ita kuma tsoron hakan take.,

Sun jima suna tafia kafin ta tsaya kofar tankamemen shagon kayan dakin,

Baki da hanci Agaishat ta saki tana duban wajen da suka tsaya,

Alhinayett ce ta fara fita a motar ,
Gannin Agaishat bata fito ba ta leka dan gannin abinda ya hanata fitowa,

Agaishat kamar an mintsineta ta juyo wajen Alhinayett ta ce" ke gala, ko dai mun bace da wajen ne? Na ji kin ce yana gudan siyar da gadaje , ke kuwa na ga kin kawo mu wannan waje dake shige da manyan ma.aikata?

Alhinayett ta bushe da dariya ta ce" Agaishat yanzu wannan ne ma.aikatar? Ba na ce da ke ba idan har kin ga waje ki ringa karantawa kar ki yarda ki nuna wani kauyanci ba?

Agaishat ta shafe gaban goshinta ta ce" hm, ke dai bari, yo ni ta karantawana nake? Wajen gadaje kayan katako an saka su a wannan waje an kilace? Lale du abu idan ya kasance yana da daraja zaka ga an kilace shi,

Alhinayett ta zagaya ta bude mata motar tana fadin malama fito kar ya kagauta ya yi mana abinda ba shi ba, mu je mu fito mu yi tafiarmu

Tana fitowa ta gimtse dariar da take yi ta kama kanta ta bi bayan Alhinayett,

Sai da suka je wajen wani madubi da mutun da tsaye ya saka dan injin caje mutun din nan ya caje su kafin suke shiga cikin boutik din,

Gaskiya ne, idan har ba kai din dan gayun bane, toh fa ka san wajen, in ba haka ba kana shiga kana iya faduwa fan kallo,
Wannan shi ake kira murmushin amarya, kukan iyaye kennan,
Tafdi, haduwa, karshen haduwa, tsari, kaya ne na manya,
Chapter 74 · 0% Book details