← Book details Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 110

Sashe 40

Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 7 min read

Wardugu ya ce" ba daga nan take ba, sai ki ga kin auri wanda ba sojan ba kuma ya kasance irin wanda bakya so din, kin gane Alhi ke dai ki yi adu.a , aman na san kina son lieutenant sosai, ke ra.ayinki na ba zaki auri soja ba dan bakya son mai fada, wannan ai shirme ne, ni na fi son ki auri wanda yake na san shi , du ranar da ya taka min ke na nuna masa bashi da wayo!

Murmushi ta yi ta kai hannunta suka cafke ta ce" Wardugu, aa fa, ba zaka dakar min miji ba wollah....

Ido ya zaro ya ce" kai, har kin fi son shi da ni?

Bakinta ta yatsina tana hararsa da wasa ta ce" oyah bude na gaishe da Ayya mu tafi kar yama ta yi sosai ,

Idannuwansa ya kai wajen su, nan ya ga Aghali baya wajen aman ita tana tsaye,
Cikin hijaban da Alhinayet ta kawo mata ne ta saka milk mai haske, hijabin har kasa yake mai hannaye sannan tamkar zubin riga aka yi masa ya dinku ya yi kyau sosai, ta saka takalminta mai dan tsini kadan da igiyoyinsa ta daure abinta das da ita,
Ajiyar zuciya ya sauke ya kai dubansa wajen Alhinayett da ya ga ta tsare shi da ido, sarai ta ga me yake kallo duda ya saka bakin gilas ya tamke kar a gane me yake ciki,

Kuma kallon wajen ta yi ta ga Agaishat ta juya wajen kofar falon ayya tana murmushi,

Wajen ta mayar da dubanta sai ta ga Mu.azam ne ya fito cikin shigarsa ta shada ya yi shar da shi , daga inda yake tsayen sai turo mata irin abin nan na soyaya yake sai yace Muah,

Ita kuwa sai ta rufe ido tana dariya,

Tsaki wardugu ya ja ya ce" ji wani shirme kuma?

Alhinayett da lumshe idannuwanta, ta ce" na me? Ba wani shirme walahi sai soyaya,

Dubanta ya yi kafin ya yi murmushi ya girgiza kansa, motar ya bude ya fita inda itama ta fito,

Tafiya ya fara da sauri sauri kamar yanda yake yi kulun, dakatawa ya yi ya dubota ya ce" kuma na saka ya tura magabatansa wajen Aba ,

Ido ta zaro ta ce" Wardugu, Wardugu,

Ina tuni ya yi tafiarsa,

Murmushi ta yi itama a fili ta ce" Wardugu zai min auren dole da soja.........

Yana zuwa suka gaisa da Mu.azam ya tsare shi da ido ya ce" haka ka koma kan mace? Ka saka yarinya gaba kana abu irin na yara?

Mu.azam ya daga girarsa ya ce" kai raba ni amini, soyaya ce,

Kai ya dafe yana mai jin matsanancin faduwar gaba, juyawa ya yi ya shige ya barshi nan kar ya hadasa masa hawan jini,

Ayya bata falo dan haka ya haye sama dakinta dan ya san Aghali wanka ya shiga .....

Yana zuwa ya gaisheta kamar yanda ya saba sannan ya zauna daf da ita yana dan mamatsa mata kafarta,

Ayya ta ce" Mu.azam ya zo min da maganar yana son auren Agaishat,

Wardugu dake rike da kafar Ayya yana matsawa sai tsayawa ya yi tsam da matsawar yana duban kasa,

Baka ji bane? Ayya ta fada,

A hankali ya dago dubansa ya sauke kanta, idannuwansa ya lumshe dan ji yake har kansa ya fara sara masa sanadiyar faduwar gaban da yake ji, me ke damuna? Ya tambayi kansa, me ya sa da an kirayi sunnan yarinyar nan ko na ganta sai na ji faduwar gaba?

Kansa kawai ya gyadawa Ayya,

Bakinta ta yatsina ta janye kafarta da haushi haushi ta ce" Wardugu bafa na son rainin hankali, ya zan fada maka magana ka wani gyada min kai sai kace inai maka wasiya?

Wardugu ya hadiye yawun bakinsa da kyar ya ce" Ayya, wai ya aka yi bakya yiwa sunana kara irin na d'An farin nan? Sai kawai in ji kin kama sunana kai tsaye wai Wardugu,

Ido ta zaro tana dubansa yanda ya yi maganar walahi sai ta ji wata kunyarsa ta kamata, ai kuwa ta juya ta dauki filo ta juyo dan buga masa sai gani ta yi ya fice da gudu a dakin,

Murmushi ta yi ta ce" ja.iri, ja.iri, ja.iri, !

Zan yi magana da yarinyata , in dai tana son sa, zan baiwa Aghali sako ya je da kansa wajen Mahaifanta idan sun amince ya kai kudin aurenta a daura kawai, Allah ya sa Alhairi ne......

To fa🥴🥴🥴🥴
😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎

🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫

Na *SAJIDA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

4️⃣2️⃣

Alhamdulilah Alla kulli halin...

A wannan rana bayan Wardugu ya ajiye su agaishat saloon dan yin kitso suka zarce park dinsa tare da samarin, inda Aghali ya zabi daleliyar mota irin ta ratsa rairai mai shegen tsada,

Bayan sun gama magana da yaron Wardugu, Mu.azam ya tsaya gurin wata mota mai ruwan ash , karama mai kyan gaske, kallonta yake yana murmushi,

Wardugu ya gama da Aghali yace" ku mu je ....

Mu.azam ya ce" wardugu, wannan motar nake so,

Aghali ya ce" me zaka yi da motar nan kai kuwa? Ta mata ne fa,

Mu.azan zai bashi amsa ya ji lumlumlum lema a hancinsa,
Da sauri ya juya yana mai ciri hankicin a aljihunsa ya goge jinnin da ya zubo masa ta hanci, a hankali ya karasa motar Wardugu ya bude baya ya shiga ya jinginar da kansa jikin kujera,
Ajiyar zuciya yake saukewa yana kara goge jinnin inda wata number ta fara shigowa saman screen dinsa, number saudiya ce,
A kasan zuciyarsa ya ji nutsuwa da number dan haka ya daga ya yi shiru ba tare da ya yi magana ba,

Ajiyar zuciya ta sauke kafin take share dan guntun hawayenta, so take ta yi magana tana tsoron kar ya ji muryarta ya kashe , ta godewa Allah da da ransa, ta godewa Allah da ya daga wayarta duda bai san ko wacece ba,
A hankali ta ce" ina son ka Mu.azam

Sai da ya ji wata kasala, a hankali ya dubi screen din, ya mayar kunnensa, ji ya yi wata nutsuwa na kara ratsa shi, a nitse ya ce" docterna, me kika je yi saudiya a tsakiyar shekara?

Idannuwanta ta lumshe ta ce" na zo rokar Allah ya baka lafia, ya nuna min jininka a duniya,

Murmushi ya yi ya girgiza kai, ya ce" kin ga jini ke zuba a hancina, bayan ina son na yi aure, har na saka a tambaya min auren yar, ina son yarinyar a raina ina son na aureta koda shi kadai zan yi a duniya,

Wani irin faduwar gaba ta ji, jikinta ya dauki rawa, a hankali hawaye ya shiga zarya a idannuwanta, a hankali ta ce" zaka aureta, kar ka damu, zaka rayu Mu.azam,

Shima idannuwansa nasa ya lumshe yana mai jinta gaba daya jikinsa, yana son yarinyar nan fa tamkar ransa, sai dai ba zai yarda haka ta faru da ita ba, ba zai yarda yana ji yana gani ya tsareta haka ba, ya sani ne idan ya nuna mata eh yana so zata sakawa ranta da zata jima da shi bayan yana ji a jikinsa an kusa zare sauran numfashin da ya ragewa gangar jikinsa,
A hankali ya datse kiran inda ya shiga shafa kansa yana mai jin jikinsa ya dauki zafi,, a hankali ya furta Agaishat ki aminta da ni na dan lokaci, ina son ki kema (🙄)

Wardugu da kansa ya fitarwa da Aghali motar nan dan baya so a komawa su yi mota daya, yana gama fitar masa da komai ya bashi hannu ya ce" aboki, ka gama da Muhsin ni sauri nake,

Amanda aghali ya yi inda ya raka Wardugu da kallo yana ayyana a ransa ko lafia?

Wardugu na tafiya yana sake sake a zuciyarsa, yakan tsinci kansa wani sakarai idan ya ganshi gaban wanda yake so a ransa yana cikin wani halin da ba zai iya fitar da shi ba,
Motar ya bude ya shiga, a hankali ya juya fuskarsa gefensa ya ga ya lumshe ido tamkar mai barci,
Motar ya tayar ya juya a hankali ya nufi saloon din da ya ajiye su Alhinayett

Yana zuwa ya yi mata message cewar ta turo masa Agaishat, yana kofa,

Ba tare da ta tambayi komai ba ta dubi Agaishat da aka gama yi mata tsararan kitso a kanta mai dan girma girma aka saka wani dan roba a karshen kitson dan kar ya warware , ta mugun yin kyau tace da ita ta je mota wardugu na kiranta,

Duda gabanta ya fadi, aman sai ta dake ta mike tana tunannin lafia? Domin yace idan sun gama su yi tafiarsu, wani abu ya faru ne?
Bata da amsar da ta fi ta fice a nitse tana mai jin faduwar gaba,
Chapter 40 · 0% Book details