← Book details Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 110

Sashe 35

Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read

Fuuuuuu ya juya ya fice yana jin kamar ya koma ya yi kwalo da ita, sai dai yana tsoron kar a je ciki ne da ita, ta ja ya yi mata lahani bayan adu.arsa kennan shima allah ya azurta shi da haihuwa, yar bakin ciki kawai take jan sa masifa salon ya biye mata idan cikin ne su barar su shiga uku!

Haka ya koma bangarensa ya zube a falon sa ya yi ruf da ciki ya dora hannayen sa saman kansa yana yamutsawa yana tunanukan rayuwa,, walyn ba wayo , haka ya ayyana a ransa kafin ya kuma fadin....ta saka sai na kara zama da wata macen? Walyn shirme shirme🤦‍♀,

*Timiya*

Amai take kwararawa har kamar ta shide, inda *Ba* ke tsaye ya dan duka dan tsayinsa, da rawaninsa yana dubanta,
Gefe guda kuwa su Anna ne da yayanta yauma Gaishat ta kawo mata ziyara da dan cikinta da ya tasa kafan wanda sarki ke mugun zumudi kansa tkar shi ne dansa ma fari,
Suna kasan bishiyar gidan suna zaman su suna yar hirar su , domin yanzu da safiya ta yi Mariama ke fitowa ta gyara wajen ta shinfida tabarmar kabar da Anna ta siyo daga garin agadez ta dauki du abinda zasu bukata su koma can su yini abinsu , nan suke sallah su ci abinci, ta dauki na baba tsofo ta kai masa domin Gaishat na tsaye kan abinda zasu ci, sarki baya wasa da ta nuna tana da bukata ake kwasa a kai mata itama ta kwasa ta kaiwa mahaifiyarta, inda ta saka sarki ya yiwa *Ba* gargadin kar ya kuma kwashe masu abincin su,

Bakinsa yake motsawa ya juya ya karewa Anna kallo da yarenta su uku sun zagayeta, ya juyo wajen amarya dake maida lumfashin kadangare bayan ta gama sheka amanta,
Tabar sansaninsa ce yake gumtsa a bakinsa,
Bakin ya bude ya totofar da yawu, domin du mai shan tabar sansani ya kasance yana tofe tofen yawu, ya juyo wajen amarya ya ce" sannu *Uwar mai uba biyu*,

Kallon kasan ido ta yi masa kafin ta kada kai,

Juya kansa ya yi wajen Anna ya ce" duniya, anai min kallon ina yiwa yarana aure suna tafia birni, ke gashi kin dauki yar santal ki badata yawon kilaki!

Da sauri Anna ta kallo shi, gabanta ya fadi,

Kura mata ido ya yi ya ce" karya na yi? Ke yanzu zaki daki kirjin yarinya na hannun kirki? To ni dai in tana aiko wani abin ake boyewa ana ci Allah ya isa! Dan ko dan ciyar da ita da na yi ya isa a yaga mini wani abin ba a rufe ni da baibai hannu ba!

Gaba dayansu dubansa suke,

Ya tako da fararan kafafuwansa da sukai fari fat na kasar garin ya dubi Gaishat ya ce" ke kuwa fa? Haka zaki saka mini ko? Kin samu na aura maki sarki , ya nada ki sarauniya aman ni kika saka kafa ki ka shure ni sai wannan tsohuwar matar kike baiwa abinki ko? Ai dukan ku Allah na kallon ku! Ko hakin ciyar da ku da na yi zai bi ku,

Ya kara tofar da yawu yana duban Mariama dake bin sa da wani mugun kalli itama da sansanninta a bakinta kamar na sauran yan uwanta da Anna, ya ce" ke kuwa ke ce gagarara ko? Mai tarda ni wajen majalisa ki tirke ni gaban abokaina, ke mai karfi wace ta fi kowa iya rashin kunya, a gaban yan uba kika yi ikirarin zaki ga ubanda zai maki aure ko? Ba laifi, ba laifi Mariama, in sun zo sai mu basu gidan su saya su tafi mu kuwa mu koma zaman titi ,

Mariama ta yatsina bakinta ta kawar da kanta,

Babar rigarsa ya kabe ya ce" kudinku yanzu na fara ci, ni da ku ba shari.a domin ni na haife ku! Dole na yi maku aure na mori kudin ku! ,

Ke kuwa, ya nuna Anna da take jan dan karamin carbinta tana shamaninta ya ce" kin ji kunya, anai maki kallon saliha sai gashi kun hada baki da tsohon can kun tura yarinya nema; ana zaton wuta a makera su Annar yara sun kunata a masaka.

Yana gama fada ya fice a gidan yana ta tofe tofensa,

Mariama ta dantsa yatsarta a bakinta tana yiwa yayarsu kallo mai kama da harara, domin ita ta yi masu kashedin kar ta kuma gannin wani ya biye masa, dan ta lura hakan na masa dadi

Gaishat ta yi murmushi tana dubansu ta ce" baku lura ya fara yin sanyi ba?

Mariama dake hararar Amaryar Ba ta ce" sanyi? A wannan tsohin najad.....

Bige bakinta da Anna ta yi ya saka ta kasa karasawa tana turo baki,

Da yannayin bacin rai ta ce" in kina irin magangannun nan hankalina tashi yake, mahaifin ki ne fa, ko me ta zama adu.a ce tsakanin ki da shi, ya zaki ringa halaya irin na wace bata da tarbiya? Bana so Mariama ,

Aman Anna, kina ganni abinda yake yi fa, ke tsoronsa kike , to ni bana tsoron sa,

Kuma bakya tsoron Allah? Gaishat ta fada tana dubanta, hakin dake tsakanin ki da shi na matsayinsa na uba Allah ba zai bar maki ba, ki bi shi, ki yi masa biyaya, ki bar shi idan shi gobensa bata dame shi ba kai nasa,

Shiru ta yi tana duban fatimata dake dan zane a kasa ta ce" wacen matar ciki ne da ita fa? Kuma kum san ba cikin Ba bane,

Anna ta kwalalo ido tana dubansu, a dan harzuke ta ce" na ga mai isata yau da yaren nan, kun yi da shi ne? Bama wannan ba sa.anku ne? Du wace ta kuma gigin muguwar magana a kan mahaifin ku a gabana zamu bata da ita! Ba ruwana ban koya maku ba, baku ga ina yi ba, kuma idan na ji tsoronsa ai ba laifi ba, shugana ne, wanda aljannata ke karkashin kafafuwansa, a haka ma ya muka kare da shi bare na yi masa gatsali? Ku daina bana so!

Ta karasa tana dan dafe kanta domin har ya sara mata maganar nan da ta yi,

Da dadaya suke bata hakuri suna masu lura da yannayinta.............

Daga inda yake ringeshe yake biya bagara a fili hannunsa a kan zuciyarsa,
Sai da ya kai karshe ya samu ya dan daga ya jingina yana duban hanya dan ya san yanzu Mariama ta zo,

Yana jin dadin lamarin mariama sai dai ita ba.a hira da ita, kimkim take masa har yanzu haushinsa take ji, bata san irin yanda shima hankalinsa ke kan Agaishat ba, adu.arsa a gareta ne, da fatan saduwar fuskokinsu kafin ya koma ga mahalicinsa,

Jama.a Wardugu na neman karin aure🤣, du mai son karya kafa ta shigo layi🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀................... dan Allah aunty Alhinayett kar ki tura masa wannan page din wollah lalla batai kwari ba kar ya karya min kafar nima😟😟😟

🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫

Na *SAJIDA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

3️⃣7️⃣

Yana nan zaunen kuwa sai gata ta shigo da salamarta ciki ciki,

Ajiye masa robar abincin ta yi bayan ta dan jefa masa wani kallo ,

Wajen ruwa ta je ta dibo masa ta zo ta tsuguna ya wanke hannunsa ta kuma cikowa ta ajiye ,

Dakin ta tatare kamar kulun shi kuwa yana cin abincin yana duban yannayinta, Mariama akoy shiru shiru sai dai yannayinta na yau kamar ranta a bace ne,

A hankali ya ce" me ke damun Mariama?

Tana gurza goron hannunta ta dan dago ta dube shi, ta ci gaba da gurzar abinta,

Can ta ce" idan ta zo hankalinta a tashe, ranta a bace, idan ta fada maka ka taba yi mata maganin damuwarta ne sofo?

Baba tsofo da ya gane Agaishat take nufi sai ya girgiza kansa a hankali , kafin ya ce" ban taba magance mata damuwarta ba Mariama, sai dai nakan saurare ta, na ji damuwarta, na yi mata nasiha a musulunce da girma, nakan ji ciwon damuwarta a raina na nuna mata ba dadi, aman kuma sai na nuna mata girman hakuri,

Shiru ta yi tana jinsa, can ta ce" wai dan na kire shi da mumunan sunna Anna ta dake min baki bayan bata taba koda shakunana ba, kana da labarin irin manya manyan munana halayansa, aman sai ta wani tare mashi?

Baba tsoho dai kallonta yake , har ta dasa aya tana hucin bacin rai, a nitse ya ce" su iyaye, sune masu madaukakiyar daraja in kika cire Allah da mazon sa a wajen dan adam, su iyaye Allah ya ce a bi su a yi masu biyaya banda hanyar sabonsa,

Shi abinda yake ba sobon Allahn bane yake?, ta fada tana duban Baba tsofo,

Baba ya gyada kansa yana dubanta ya ce" ya taba daukan y'a ya bayar ba.a daura aure ba?

Mariama ta girgiza kai,

Ya ci gaba da fadin" yana yin aurwn yayansa dan dukiya, adini bai jaramta hakan ba sai dai ta yannayin da yake yi ne,
Yana yi ne tamkar yana siyar da yayan,
Wa ke tafe da duniya da abinda ke cikinta Mariama?
Ya kuma watso mata tambaya,

Mariama ta ce" Allah,

Shin baki da labarin ya fi gannin abinda kike aikatawa? Ya fi ki jin abinda ke wakana a tare da ke?

Na sani , ta fada tana kawar da kanta,

Baba tsofo ya ce" shi zai kare ku!

Yana fadin hakan ya yi shiru tamkar ba shi ba,
Da mamaki take dubansa, bata san lokacin da ta dawo facing dinsa ba ta riko hannunsa tana dubansa ta ce" shikenan? Hukuncinsa kennan?

Baba ya yi mata murmushi ya ce " ke kika halice shi da zaki hukunta shi?

A hankali ta sada kanta, muryarta ne ya yi rauni ta ce" ya cika cin zalinmu, bai san darajar matarsa ba wace take mahaifiya a wajen mu, mu yayansa yakan dauke mu ne ya yi kudin mu, yanzu ya tare da matar da wani ke ziyara a kan idannuwansa, shin yaya ake so dole dole sai na daraja wannan mutun?
Chapter 35 · 0% Book details