← Book details Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 110

Sashe 105

Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read

Ai kuwa ta kwalalo ido cike da murna ta mike ra budi baki ta ce" Fatimata, Fatimata....
Sai kuma ta ji muryar Gaishata,

Ita kam bata taratsinsu, cikin nutsuwa ta ce" Agaishana,

Agaishat ta zauna tama rasa ina zata saka kanta dan dadi, muryarta nitse ta ce" Gaishata, Gaishata ina kuke ne? Gaishata Anna da sauki jikin nata? Kuna Timiya ne?

Gaishata ta girgiza kai tamkar tana gabanta ta ce" aa, muna garin da kike, mijinki ne ma ya kira jiya, Gukunni ya bashi number Anmou,

Agaishat ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Gaishata kin haihu? Me kika samu?

Gaishata ta yi murmushi ta ce" du wannan tambayoyin adana abinki abinda zamu zo? Dama muma zumudin mu ji muryanki ne, aman Anna da sauki sosai alhamdulilah, nima kuma na haihu, Agaishat, lafiarki kalau dai ko? Ba abinda ke damunki gidanki ko? Agaishat amarya, yar Ayyanta aure sai da hakuri kin ji?

Agaishat ta yi murmushi tana ta sauraron muryar yayarsu ta fari, wani dadi take ji na ratsata har suka kashe kiran bayan sun tabatar mata da suna gari da zama , da sun huta zasu zo inda take,

Suna kashewa ta ji wani karfin gwuiwa ya zo mata, hakan ya sa ta zauna ta shiga game d wayar hankalinta kwonce,
Ta so kiran number Ayya, sai dai tunanin kar ta huce gona da iri ya saka ta bari idan ya zo sai ya kira mata kamar yanda ya saba , ta bata albishir,

Fararan hakoranta kawai take yawan washewa,

Ta jima nan kafin ta mike ta nufi kicin dan shi ne kawai aikinta a gidan,

Da yama bayan ta gama salar la.asar ta zauna da wayar da ta wuni game tana jujuya abinda ta rubuta da yarenta, inda ta samu da kyar ta gama message din kamar haka

*Salam*

Ina yini Ya, ya aiki?
Zan kira ayya ne......................na gode

Agaishat

Numbersa da ta shanye tun tana gidan Ayya saboda tarin zero din dake ciki irin number nan mai shige da juna ne ta rubuta ta tura dan ita ta kagauta ta ji muryar Ayya ta fada mata sun yi waya da yan uwanta da Annarta,

Wardugu dake tuki daga justice ya fito ransa a mugun bace sakamakon kiransa da Gukunni ya yi kan case din AISATA matar Marahut, za.a salameta nan da wata biyu domin a lokacin da ake binciken asalin masu shigo da kwayar Niger ta bada hadin kai wajen fadin sunnayen wa.inda ke siyar mata baki daya, ta bada sunnayen wa.inda ta san suna siya a wajensu, sannan ta yarda bata baiwa sharia wahala ba ta hanyar gardana ko kin hada kai, hakan ya sa ta samu sasauci bayan kason da take yi an dankara mata tara ta millioyin kudi sannan wai za.a salameta!
Hakan ne ya kunno shi, ido rufe ya fito ya dauki hanyar neman Marahut, nemansa yake ido rufe, shi ya san koda da haka, to fa da saka hannun Marahut ta hanyar gannin masu Niger din dan a salamo masa matarsa marar mutunci,

Wayar ce a hannunsa yake dannawa yana neman layin Marahut, aman amsar daya ce, number a kashe, layin ba zai shiga ba,

A haka message ya shigo, da yake orange ne yake kiran da shi sai ya yi tunanin ko zasu shaida masa number ta bude ne?

Yana budewa ya ga message din,
Kallon number ya yi ya ga number wayarta ce da ya saka mata layinta cikin wayar nan,

Wai wardugu gatsal tamkar wani sa.anta? Sannn shi zata turowa message da umarni? Me take tunani? A me ta dauki kanta? Ba damuwarta bane da damuwarsa itama ko? Bata damu ba da halin da yake ciki ko?

Wani kuuuuu ya taka birkin motar kafin ya samu ya yi riboss da matsiyacin gudu ya dauki hanyar Aeroport din, ba zai hadiyi cewar, shi yana hana kansa komai idan ya ga koda yannayin fuskarta ya canza ne aman ita bata damu ba, da damuwarta kawai ta damu, zai warware mata rashin mutunci ne ta san cewa bafa shayinta ko taoronta yake ji ba! Zai je gidan ya.......

Wayo yar muleka😕😕😕😕

🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫

Na
*SAJIDA*

8️⃣4️⃣

*KUTKALE* (PRISON)

*AURE YAKIN MATA NE*

*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*

daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA* in sha Allah,

........kar ku bari a baku labari.....

Yana sake saken tarin mugunta ya karasa gidan,
Bai yiwa kowa magana ba, bai shiga hurumin kowa ba kamar yanda ya fita ya nufi hanyar sada shi da ciki, inda kowa ya shiga tatara kafafuwansa yana barin wajen dan ba zai so abinda za.a kula da wani laifi nasa ba,

Bata falo, hakan ya sa ya zarce dakinta na barci,
Nanma bata nan, dan haka ya fito ya nufi kicin,

Dago kan da zata yi ta ganshi ya nufota,
Yannayin fuskarsa ya sakata sakin nade naman da take cikin kabeji zata yi name,

Da sauri ta mike daga kan kujerar mai ruwan silba ta daga kafarta,

Kafin ta shige inda zata shige dan ta san wannan zuwan nata je, dan irin kallon zaki ci yan garinkun da ya yi mata ya saka hanjin cikinta motsewa waje guda,

Rikotan da ya yi da karfi sannan ya fincikota baya ya jefar cikin kicin din,

Yau ta ga rana ta ga tashin hankali domin binta ya yi inda take yaden nan ya wanka mata wani lafiyayen marin da ya dauke jin ta,
Tabas wani dummmm ta ji na lokaci mai dan tsayi domin za.a kai second ashirin hakan ya saka bata ji fadansa na farko farko ba sai da kunnen nata ya dawo ta fara tsintar fadansa kamar haka" *Ba zai yiwu kema ki wulakanta min zuciya kamar yanda ta wulakanta min ba!* ta yayama zan fita daga gidannan raina bace , baki damu da yi min wani abin da zai faranta min ba sai faman ki dura min abinci kafin na fita bayan ina azumi? Ya zan je ma.aikata kin san wani irin aiki nake yi aman ki turon message gatsai gatsai da rashin tauna zance ya zama dadi kamar ke ce gaba da ni ki turo min, oho o na ji abinda zan ji ko? Da wannan dan iskan ne da ya zo wajen diner mai dogon wuyan nan yana launi uwa lagwani da kin zauna kin ware yare kin masa tausasa ko? Da ace tsohon mijinki ne kin iya yi masa kalamai, wanda nima shaidar shi mai daraja ne ana bashi kulawa ne ko? Ni zaki turowa sako da kama sunana kai tsaye tamkar dan gidanki? Sai mutun ya gama mutuwar muku ku wulakanta shi ku zubar da shi ku kara gaba abinku ko? Ku buzayen nan haka halayenku yake? To bari ki ji, a kaina an tsaya, walahil azim Agaishat hanya a bude take, kafarki ke ta taka waje da niyar barina sai na harbe ki! Sai dai a kashe ni! Jarabawata ce soyaya da buzuwa? Na karba, aman kuma rantsuwata ce ke ce buzuwar karshe da zan ringa mafarki ina juyi kanta! Ke ce zan yiwa son karshe a cikin buzaye na wahala dan buzuwa! Ke ce wace zata rayu da ni ko a wani hali, ke rabon haihuwarki da wani namijin sai dai idan ajali ya dauke ni!

Hannunsa ya buga jikin madubin kicin din da aka kafa kato domin ado inda ya fashe dan kuwa mai fashewar ne, ya tako zuwa gaban Agaishat dake zaune, cikin wani irin firgici da bugawar zuciya mai tsanani ya dubeta ido cikin ido ya ce" ke ko mutuwa na yi, Allah ya isanmin idan wani ya shiga gonata (Dankari, ka ji masifa fa, an taba yin haka dama?),

Sai da ya gama tashin hankalin da ya dirmiyar da ita cikin wani yannayi na furgici da tsoro, kara jin shayinsa, tashin hankalin abinda ya ringa maimaitawa a fadansa *ba zata wulakanta masa zuciya kamar yanda Aisata ta wulakanta masa ba,* sannan ya juya ya fita a kicin din,

Kafafuwanta ta hado gaba daya ta hade a jikinta, barin da jikinta yake yi ta samu ta daidaita ta hanyar adu.a,

Mikewa ta yi ta je wajen kayan da take gyarawa ta harhada komai ta kimtsa still jikinta na rawa sannan tana share hawaye ta ajiye komai wajensa ta fito,

Sai da gabanta ya fadi ganninsa a fallon, bai fita ba kennan, yana waya da alama da Ayya yake dan a tubancin da yake tana tsintar yan kalmomi da kuma sunnan Ayyan

So ta yi ta koma kicin din, sai dai wani abin ya hanata dan haka ta taho a hankali ta raba ta nufi dakinta,

Da kallo ya bita ya ci gaba da wayar, sai da ya gama ya taka zuwa dakinta, tun da ya fara fadan nan ko ci kanka bata ce da shi ba, yanzun ma da ya shigo yana ta muzurai ya bala mata harara kafin ya karasa ya tsaya kusa da ita ya ce" wato ga mahaukaci ko Agaishat? Shine kike nufi na yi na gama ko?

Agaishat ta dago da idannuwanta da suka rine dan tsabar shiga tashin hankali ta dube shi,
A hankali ta ce" ka yi hakuri,

Wardugu ya ce" hakuri? Hakurin me zan yi a ciki? Na rashin bani muhali a rayuwarki ko na raina ni da kika yi?

Agaishat ta kuma dago da kanta, wannan karron bata sada duban nata ba ta kafe shi tsai da kallo,
Fitina kawai yake ji, so yake ta biye masa kamar yanda suka saba da matarsa ya tataka banza ya yi gaba abinsa, tabas ta yi rayuwar rashin sannin ciwon kai, aman bata tunanin zata yi rayuwar duka a gidan miji,
A hankali tana dubansa ta ce" menene laifina? Meye na yi mai girma haka? Ka taba nunan baka son sunnan nan? Ince kulunma da shi nake kiran ka kuma ka amsa ba tare da ka nunan bai yi ba, menene? Ganninka a irin halin nan an taba *AISATA!*

ido ya zaro yana dubanta, kai kai kai,
Agaishat ta ci gaba" dan Allah ka yi hakuri, kar ka saka ni a irin wannan rayuwar, ban iya ba, ban iya wannan rigimar ba, idan na bata maka ne ka yafe min, sannan ka daina tuna baya kana hada ni da wasu gardawa da aurena kuma na san darajar auren nawa,
Chapter 105 · 0% Book details