← Book details Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 110

Sashe 15

Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read

Sojan dai bai ce komai ba ya bude ta fita da bindigarsa yana kallon ikon Allah
Wardugu ma ya fito ya rufe ya tafi wajen sojan ya fara tafiya, sojan ya waiwaya ya ga a yanda suka ajiye motar a bakin hanya, bayan wannan matarsa a ciki, sannan tsakanin fadar da hotel din sojojin akoy tazara, kuma idan mutun ya tunkaro wajen haka kai tsaye daga bakin karfe goma na dare ordre da aka baiwa sojojin shine harbi ba ji ba gani in dai ba a mota ko wani abinda yake malakinsu ba wanda da ya tunkaro wajen akoy adadin odar da aka ce su yi dan shaida su ne wada kowace safiya ake canzawa
Shi dai biye yake da shi da sauri yana hadawa da fan gudugudu suna tafiya har suka fita daga gidan suka dauki hanya (🤔 sisi kika ce zaki iya da wardugu ko?🤣)

Walyn wani ihu ta saki a daidai lokacin da ta fahimci wardugu bara mata ya yi motar gaba daya ya tafi a kafa da ya je da ita, Wardugu ita yake wulakantawa? Toh ita kuwa ba zata shiga wajen wannan uwar tasa da wannan yarinyar mai karnin jini ba! Sai dai ta kwana a motar!
Haka ta takure a motar nan ta ki kunna hasken waya dan a gaskiya tsoro take ta kunna waya wani abin ya lura da mutun tun bama dare da ya tsala maguna suka fara kukan jarirai ba,

Kawata, tsakaninki da Allah ke haka rayuwarki wata irin mace ce bahaguma? Yanzu yarinyar nan da kika kwaso kin san asalinta ne?

Ayya ta yi murmushi tana kallon kawarta aminiyarta matar sarki, ta ce" mamanta ta iya tubanci

Anna matar sarki ta dafe kai ta ce" dan ta iya tubanci sai me? Dan ta iya yarenki shikennan sai ki wani kwaso yarta? Kin ce a gidansu kuka daukota

Ayya ta ce" ki gane kawata, lamarin mahaifiyar yarinyar da yarinyar ne akoy sarkakiya, wai kawai dan kalar fatarta shikenan take fuskantar tsangwama, ita kuwa uwar sai kawai ki ji tana yare kuma wai tace itama bata san sunnan yaren ba, kuma ni na yi haka ne dan cika alkawarin bawan Allahnan, baki ga yanda ya tsufa ba aman haka yake nisa lamarinta,

Anna matar sarki ta dafe kanta da hannunta dake cike da zobunnan zinari ta kalota ta ce" ai idan kin lura yanzu wannan matsakar ta zama ruwan dare, a kauye suna kin bakar fata tare da jahilci a birni suna kiyaye bakar mace dan dogon buri irin nasu sannan suna hakan ne da dabara, kina ganni daidaiya zaki ga a yanzu mutun ya tashi ya dauko bakar mace, sai ki ji suna fadin Allah ya basu farar mace koda maya ce, banza idan ta cinye su fa?

Ayya ta dora kafarta daya saman daya tana ajiye tufar da ta gutsura ta ce" ba ko.ina ba, ban ki maganarki ba aman nima nace maki ba ko.ina ba,
Du macen da kika ga ana yi mata duban marar kyau ko anai mata wani gani gani ina mai tabatar maki ita ta saki kanta,
Mace du muninta idan ta iya wanka ta iya kula da jikinta ta iya kwaliya daidai da yannayinta sai ta kara da adu.a kawai
Sannan ita bakar mace da kike ganni baiwa ne da ita, bakar mace tana da kwarjini, bakar mace nada juriya a kowani fani, bakar mace na da kyau mai fuzga, idan bakar mace ta sakar maki tsararen murmushi zaki hangi haske ne a tatare da ita, ke kawata zaki sha mamakin yar amanata in sha Allah

Anna matar sarki ta yi murmushi tana jujuya kanta ta ce" oho dai, kina kare bakar fata dan kina da ita bayan taki mai kyau ce, na rantse maki ko ni na samu taki ina so domin bakinki mai kyau ne, ba gashi ba Wardugu ya samu dan bakinki da farin mahaifinsa sai ya samu kalar fatar nan ta yan ethiopia baki ga yanda fatarsu take ba? To aman wannan yarinyar kina ganni da akace wanka ta saka kuka aman kika biye mata wai kika rakata ta yi baci a haka? Anya kuwa zaki iya wani gyarata?

Ayya ta ce " ki saka ido kawai.....

Sojan nan tafiya dai yake aman ba karamin gajiya ke tatare da shi ba, sai ya ga Wardugu daga kafa kawai yake yana jefawa yana kara kutsawa cikin duhun garin suna ta sauki su karasa hotel din
Ba su su karasa ba sai kusan sha biyu na dare,
Suna karasawa Wardugu ya saka kai kai tsaye ya nufi shiga wajen da idan ka shigo harbi ne zai salamo maka ....................

Kadan ne ku yi maneji😍😍😍😍

🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫

Na *SAJIDA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

1⃣8️⃣

*Godiya ta tabata ga Allah sarkin sarauta ubangijin talikai, godiya mai dumbin yawa gareku da adu.a Allah ya saka da alkhairi ya biya ....*

*Khadijat tawa ta grup BAK'A CE* wannan page din naki ne

Ja sojan ya yi ya tsaya bai san lokacin da ya ce " Oga, zone interdite ce fa

Wardugu ya juyo yana kallonsa, ya yi murmushi ya ce " tsoro kake ka mutu sergent?

Kansa ya dan shafa yana kallo Wardugu,
wardugu ya kara cewa" mutuwa fa ko kana kan gadonka sai ta daukeka sergent ba gwara mu tunkareta ba?

Kara kwalalo idannuwansa ya yi yana kallon wardugu

Wardugu ya matso ya dafa kafadarsa ya yi murmushi ya ce" mu je ......

Haka suka kutsa gaban Sergen din nan tamkar ya bale ya fado dan tsoro,
Sai dai ga mamakinsa sai ya ga sun kama wata yar raga a nan Wardugu ya bude ya shige
Shima shiga ya yi yana ta waige waige yana biye da wardugu nan ya hango ashe har sun shiga balbalin hotel din sun fice hatsarin

Wara wawar ajiyar zuciya ya sauke yana biye da wardugu
Wardugu ya rage sauri ya dan rage sautin muryarsa ya ce" nima bana so na yi mutuwar bindiga fa Sergen, ina so na mutu cikin nutsuwa kai da zabi gareni in mutu ina sallah kuma ranar juma.a,
Aman kawai yau ranar asabar gatsai gatsai sai mu tarbi mutuwa? Da juma.a ne ma,

Ya dan yi murmushi ya yi gaba ya barshi nan tsaye yana murmushin shima, kai ogansa idan ya yi wani abin tamkar ba shi ba, wai shifa a nan wasa ya yi masa da rai🤔

Tun fa wuri ta farka daga bacin da ya saceta, sai dai ta ki motsawa tun a jiya da aka sauketa saman gado ta yi baci ta kasa ta sauko kasa ta kwonta saman farin tls din ta rufa da mayafinta na turkudi tana kallon yanda pankar sama ke juyawa har baci ya dauke, a yanzuma ta farka tun da wuri tana son tashi sai dai tsoro take hakan ya sa ta yi kuri da abin mamaki a fuskarta tana kallon pankar nan, mamaki take menene? Ya aka yi bai daina gudu haka ba? A gaban idannuwanta aka kunna , tunda ya dauki gudu bata ga ya tsaya ba, ita tsoroma take ya yo kasa kasa ya kasheta

Ayya ce ta bude dakin ta shigo da salama a bakinta

Firgigit Bak'a ta tashi ta zauna jikinta jikin garu tana bin Ayya da kallo

Ayya ta yi tsam itama tana karantarta, a kasa ta kwana du sanyin nan na kasa, sannan da alama bata yi sallah ba

Dukawa ta yi kusa da ita tana kallon yanda take jan mayafinta tana lulubawa a jikinta,
Murya a sake ta ce" kin yi sallah?

Da ido kawai Agaishat ke bin Ayya domin bata san me take fada da yaren tubanci ba

Ayya ta yi dabara ta kamo hannun Agaishat ta mikar da ita ta jata suka nufi bayi

Suna shiga Ayya ta dauki butar karfen dake wajen ta kunna ruwa mai dumi dumi ta cika mata ta nuna mata wajen da zata iya dukawa domin ta san ba wani gane lamarin wc zarai ba tukunnan dai, ta yi mata nuni da ta yi dagara ta yi alwallah ta yi sallah , ta yi mata nuni da har rana ta fito

Da kai Agaishat ta amsata tana kallo sai da ta fita ta duka ta yi fitsari nan inda aka nuna mata ta wanke jikinta ta mike ta yi alwallah tana jin dadin yanda ruwan keda dumidumi

Tana gamawa ta fito ta ga salaya aman ba kowa a wajen dan haka ta hau ta tayar da sallah ta yi abinta cikin nutsuwa kamar yanda Baba tsofo ya koya mata

Tana gamawa ta zauna ta hade kanta da gwuiwarta tana zubar da hawaye, tunani take ya Anna ta tashi? Ya yan uwanta? Ya baba sofo? Wa zai kai masa ruwa? Wa zai gurza masa goro? . .....

Buda kofar aka yi aka kuma shigowa ,
Wannan karon matar sarki ce da wata baiwa buzuwa da kuma Ayya

Ayya ta kali matar sarkin ta ce" so nake a fada mata ina so ta yi wanka ta shirya mu tafi garinmu domin Wardugu yace jirgin karfe daya zamu bi

Matar sarki ta yi murmushi har yanzu tana mamakin daukarwa kai irin na aminiyarta, ita da ko hausar juna basu iya ba
Ta kali baiwar nan cikin isa da dakewa ta fada mata abinda zata fadawa Agaishat wace tunda matar sarkin ta fara fadi take kallonta daga zaunen da take tana fahimtar yarenta

Kafin ma baiwar ta fadi Agaishat ta kallo Ayya, a hargitse ta ce" ina zamu tafi kuma? Kar ki kaini wani wajen kin ji? Ki barni a nan ma

Tana fada ne tana dan nufo su Ayya dake tsaye

Baiwar ta yi saurin tareta , da yaren buzanci ta ce" ki tsaya nan, kin san ina ne kike a nan? Kina garin agadez, a garin agadezma kina masautar agadez, a masarautar agadez ma gaki gaban matar sarki uwar gida sarautar mata,
Ki koma baya ki cika umarninta

Rakubewa Agaishat ta yi tana kallonsu, ta shiga ukunta, ya zata yi? Matar sarki kuma? Ko sarkin garinsu talaka bai isa ya yiwa matarsa ko yayansa wargi ba bale na garin Agadez

Kanta a sade ta ce" zan yi wankan
Chapter 15 · 0% Book details