← Book details Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 110

Sashe 76

Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read

Kit ya datse kiran,
Juyawa ya yi wajen da suke, ta daura mayafin a kugunta ta yi tsaye gaban katon madubin dake jikin bed din da Alhinayett ta zama tana juyi suna daria wai ga yanda Alhinayett zatana yi a dakinta ita daya gaban madubi,

Dubansa ya kai wajen Elhaj ya ga yana tsaye shima yana dariar domin tana abin ne gwanin sha.awa,

Ji ya yi ransa ya baci da hakan, dan haka ya karasa wajensu ya ja ya tsaya ya gala mata hararar da ta sakata tsayawa bata shirya ba,

Hankalinsa ya mayar wajen elhajin ya ce" Elhaj sun gama ne?

Elhaj ya ce" sauran su kayan kyale kyalen falon Elhajinmu

Wardugu ya ce" ai su je kawai, sauran a duba tsarin kayanta a hada mata wa.inda zasu yi kyau,

Elhaj ya amsa da an gama ya juya wajen yaransa ya shiga basu umarnin yanda za.a shirya kayan a loda maza a kai adres din Alhinayett wasu cikinsu kuwa ya saka su karasa hada abubuwan da ba.a hada ba,

Alhinayett ta karasa kusan wardugu ta tsaya daf da shi, irin idan tana sin yi masa maganar siri ta ce" War, Mu kam mun yi kasuwa a nan fa,

Wardugu dake dubanta daman ya san magana take da shi, dan haka ya yi mata duban bai fahimta ba,

Alhinayett ta ce" Elhajin nan yana ciki fa,

Wardugu ya gimtse fuska yana dubanta dan ta fara gajiyar da shi sai wana masa magana take, ya ce" cikin ina wai?

Alhinayett ta ce" yaja son Agaishat mana,

Wani irin dago da idannuwansa ya yi ya sauke a kan fuskar Alhinayett dake murmushi tana dubansa irin ta yi da biyu dan ta ga reaction dinsa, aman da yake ya fita iya duniyanci sai ya yatsina fuska ya watsa hannayensa yana mai tausar zuciyarsa ya ce" shi zai iya jimawa da ita ko? Dan kam na gaji da yi mata aure ana sakota ,

Ido Alhinayett ta zari tana rufe bakinta da mamakin Wardugu, ta ce" Wardugu har sau nawa ta yi auren? Ai ko abokin ka da ya sake ta bai ganta a haske ba, sannan bai san ciwonta ba, na tabata du wanda ya dauki Agaishan ayya a yanzu zai yi mata rikon gold ne

Ido ya kankance yana dubanta ya ce" meye zai saka a yi mata rikon hakan? Yarintar? Ko kanantar? Kin san me ke rikita maza kuwa? Mace ginaniya, wace idan ta motsa zata motsa da shi ba yar jaririya ba, shima Elhajin Mubarack din nan nake yi masa duban baban yaro ashe dai yaro ne,

Ido ta kara zarowa tana dubansa yanda ya gama magangannun ya gimtse fuska yana kuma kallonta kafin yake juyawa ya ce" ta yafa mayafin nan a saman kanta,

Tafiya ya yi Alhinayet na kallonsa baki sake, murmushi ta saki kafin take girgiza kanta , ta yiwa Agaishat dake kara kallon kaya magana suka kara gaba,

Ko a wajen gyaran jiki yau da aka fara jika jikin Alhinayett da turare haka ta kara kudin wajen Agaishat itama aka shiga yi mata sak irin gyaran amare,
Tsume tsumen nan da ake basu kansa tana shanye abinta kai tsaye inda Alhinayett ke yi mata kallon ta san ko na meye tunda ta taba aure, hakan ya sa itama ta kama abin da karfi karfi gannin wace ta taba aure batai masa da wasa ita kuwa Agaishat na sha ne dan dadi yake yi mata, ,

Sosai suka wuni cikin farin cikin da Wardugu ya saka su, suna dawowa suka tarar d Ayya a wajen hutunta tana zaune da jarida a hannunta,

Gannin su ya saka ta ajiye jaridar hannunta tana dubansu da yalwatacen murmushi a fuskarta dan yau an yi masu dilka sai sheki suke,

Suna zuwa Alhinayett ta karasa kusa da Agaishat kadan ta duka har kasa kanta na kallon kasa ta ce" Ayya, ina rokon Allah subahanahu wata.ala ya kara rufa maki asiri ke da kika yi silar zuwan Wardugu duniya da mahaifinsa da dukan wani wanda ya shafe shi, ya Allah ya yi maku sakaya da gidan Aljana, Allah ya rabaku da kunyar duniya da ta kiyama, Allah ya.....sai ta yi shiru sanafiyar hawayen dake zubar mata ,

Ayya ta dafe kanta ta ce" ya salam, Ke Alhinayett tashi tashi maza goge hawayen ki, menene haka? Haka Mahaifin ki da da maman ki basu dade da fita a gidannan ba, ke idan bai yi maki haka ba , ni da kaina sai na ga bakinsa irin yanda kuke tare da zuciya daya? Maza daina wani kuka ba yayanki bane?

Alhinayett ta shiga share hawayenta tana duban Ayya,

Ayya ta sauke ajiyar zuciya tana duban Agaishat da ta yi narai narai ta ce" kin ci abinci kuwa?

Agaishat ta daga kanta,

Alhinayett ta dungureta ta ce" ta sha solani dai, bata ci abinci ba,

Ayya ta dafe kai, ta ce" kin ga, frij cike yake da kalolin solani tunda na fadawa Wardugu ta mayar da solani abincinta ya kasance kafin ta gama da ta frij an kawo wasu an cika a frij, du wajen yarar gidannan ki ka duba zaki ga ledojinsu na yawo a ciki, tsorona ya saka mata ciwon ciki gata ba shan maganin zafi ba sai ina tsaye,
Ayya ta karasa tana dafe kanta,

Agaishat ta zauna gefen kujerar da take zaune ta dora kanta saman jikin Ayya ta dora hannunta wajen jaridar da ta ke karantawa ta ce" Ayya, wai mai siyar da kayan gadajen nan ya ce yana so na,

Ayya ta zaro ido tana dagata daga kwonciyar da ta yi kamar mage ta ce" ke kuwa ki ka ce da shi me?

Agaishat ta dubi Alhinayett ta ce" ni kalon sa na yi, kafin nake dan motsa bakina, na kada kaina sai kuma na yi gaba na bude motar Alhinayett na zauna na sada kaina, kin ga ban nuna zumudi ba, ban kuma yi masa rashin kunya ba, ko Alhin

Ayya ta yi murmushi tana duban Alhinayett ta ce" Alhinayett zauna mana,

Alhinayett ta zauna sosai, dan ta lura yau Ayya na yi da ita, ta sake mata fiye da kulun, dubanta ta kai wajen Agaishat ta ce" auta, dauko min faro,

Agaishat ta mike ta nufi ciki

Ayya ta dubi Alhinayett ta ce" Alhinayett, ki yafe ni kan wasu abubuwan da nake nuna maki kin ji? Kin san rayuwa, yau ko Wardugu na dan cikina dole na saka ido a mu.amalarsa da kowa bale mata, gashi a zamanin ku ake kawance mace da namiji, har ga Allah na sha saka shi gaba da fadan ya aure ki sai yace da ni kawarshi ce ba zancen soyaya tsakanin ku, hakan ke saka ni a halin tsoro , idan kika yi duba da tsakanin mace da namiji akoy shedan,

Alhinayett ta gyada kanta tana duban kasa ,

Ayya ta ce " tun yaushe mahaifiyar ki ta rasu?

Alhinayett ta dago da kanta tana duban Ayya, ya aka yi ta ji? Sai dai bata da amsa ta san tunda ta yi mata tambayar toh tana da labarin yanzu, dan haka ta ce" rasuwar mamana , wani soja ne ya kadeta, kuma sojan mahaifinsa ne baban mutun hakan ya saka suka rufe akama ki bin maganar,

Mafarin haduwana da Wardugu kennan, ba wancen labarin ba, domin na je na kai masa kukana, na fada masa komai hakan ya sa ya yi bincike, cikin ikon Allah ya tarbi abin da karfinsa inda ya samu baban Alkalin nan datijo mai sunna *Gukunni* ya zama lauyana a lokacin baban lauya ne da ake shayi , nan ya shige gaba suka hada karfi da karfe cikin ikon Allah suka kada shari.ar , dalilin da ya saka mahaifina ya cirewa Wardugu shamaki da cikin gidan mu, dalilin da ya saka na samu sa.ar zama abokiyar Wardugu, har ake mamakin irin kusancin mu da irin yanda muke hira da Wardugu, kuma duda haka sau biyu yana yi min dukan da ba zan taba mantawa ba , dayan kan karatuna da na so na yi wasa da shi, ya yi magana ya yi magana na kiya har Abana ya bashi damar ya yi maganina, a ranar sai da na kwana asibiti, na biyun da na fara samari masu hatsari, irin yaran nan yayan masu kudi dake hurewa yara kunne, suka so su saka ni a uku a lokacin yana Spain, ya yi min nasiha, ya gwada min ilar abin du na kasa fahimta sai da ya dakar min fata na suma sau biyu , tun daga shi na yi byby da samarinma baki daya sai yanzu Allah ya yi,

Ayya ta girgiza kai tana dubanta kafin ta yi murmushi, ta ce" daga yau ku daina zuwa gyaran jikin, in sha Allah zan karasa maki a gida,

Godiya Alhinayett ta yi ta yiwa Ayya har ta dakatar da ita,

Ayya ta hangi Agaishat tafe da faro ta ce" kin san menene, ina son Agaishat tamkar yar da na haifa a cikina Alhinayett, na yi sake aurenta da na tashi na baiwa yara haka , har ina tuhumar kaina da ni na haifa zan ko yi haka? Ina jin haushin kaina,

Alhinayett ta ce" Ayya, ba maganar sake, abinda Allah ya tsara sai ya kasance a kan bawansa, aure kuma ai lokaci ne , idan ya yi ko a halin yaya sai an yi shi idan kuwa lokacin mutuwarsa ya yo komai so sai an rabu, Agaishat na girmama girmanki a zuci da fili, bata taba nuna laifinki kan komai ba, koda ta san ta yi laifi takan yi murmushi ne tace Ayyana zata min fada, kuma ta je ta kasa barci, kin ga kuwa karara shakuwa ta iyaye ta bayana a lamarin,

Ayya zata yi magana ta karaso dan haka ta yi shiru, ko ba komai bata so ta san irin girman son da take mata dan karta sangarce mata, Agaishat duka duka bata fi 21 ba, har yanzu yarinya ce

Wardugu ne zaune da waya a hannunsa yana amsa kiran Elhaj Mubarack,

Elhaj Mubarak ya ce" Elhaj, nafa ga iri a wajenka,

Wardugu da ya dago zancen , ya gane inda ya nufa sarai, ya san me yake son fada masa , dan haka sai ya dantse lebensa na kasa yana sauraronsa,
Chapter 76 · 0% Book details