Sashe 7
Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi Mahaifiyar Aghali ta yi, Ayya akoy mulki wannan da gidan sarauta take da an ji jiki domin mace ce mai mulki da isa, ga jan aji, da yake an dauko hirar da bata so daga haka ta katse hirar ta mike tana yi masu salama dan tana son shiga ciki ta kirayi number Wardugu rabonta da shi tunfa suka karaso jiya ba shi ba labarinsa
...........rashin Comment ne kawai zai saka ni daukan matakin siyar da novel din nan ko na tsayar da shi, 😊
🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
9⃣
Ayya na zuwa dakin da aka sauketa zauna ta jinginar da bayanta jikin kujera ta daga kanta sama,
Ta jima tana tunani, kafin take sauke ajiyar Zuciya a fili ta ce " *MARAHUT*, ina ka shiga? Ka san komai ka tarwatsa rayuwarmu, Marahut ina tausaya maka sai dai mutuncina darajata ba zan yarda ka zubda mini ba! Ka zabi wancen rayuwar ko? Ba komai ka je sannu duniya zata koya maka hankali,
Ranta ne ta ji yana suya, yama aka yi ta tabo mata wannan mikin, ta sani da gangan ta tuno mata da maganar domin ta fi kowa sannin abinda ya faru, ita kadai sai Wardugu suka san takamaimai abinda ya faru aman zatana tuno mata da shi , ita so take sai ta yi hakuri bata san ta rufe babinsa ba kuma ko da jaraba sai ya saketa dan bata fatan idan ta mutu ya kasance shine alwalin gawarta (Toh fa😳 tubawa akoy zuciya)
Aghali, dan me ba zaka kara aure ba? Matanka biyu yarka daya mace sai matan daki , ko a cikinsu har yanzu ba wace ta samu ciki bayan ina kula da irin zubin da ake maka ana canzawa du wace ta kwana biyu, ko dai baka zuwa inda suken da gaske? Domin na ji kishin kishin cewar wannan matar taka ta shanye min kai,
Mahaifiyar magajin sarki ce ke fada kan ya ki karo aure bayan tana son ya tara yaya
Murmushi ya yi ya ce " zan kara aure, ki kwontar da hankalinki,
Ajiyar zuciya ta sauke kafin take miko masa yar akwati tana murmushi ta ce" ka ga Amynka ta kawowa wannan mumunar ( wato yarsa jikarta)
Hannu ya saka ya bude ya gani, sarka ne da yan kunaye na zinari masu kyau sosai kirar yara, murmushi ya yi ya ce" zata je ta gaisheta sannan ta yi godiya........ wannan kennan
Sai da ta bude lulubarta suka ga mace ce bayan ta fada masu ita mahaifiyar Gaishat ce , suka je suka shaidawa sarki ya bada izinin a shigar da ita bangaren Gaishat din yana mamakin zuwanta da fadawa zuciyarsa ba lafia ba domin shekara kusan takwas da aurensu bata taba takowa ko aiko da kannen Gaishat din ba duda tana yarta ta fari, itama bata wani zuwa gidan du ta takura rayuwarta da tsoronsa ta mayar da kanta ta daki duda kuwa irin yanda yake daukaka martabarta fiye da iyayen yayansa
Tana shiga dakin ta nemi waje nan kasa ta zauna ta sada kanta , da kujeru da komai aman ta fi fanewa zama a kasan nan
Da sauri ta fito jin sakon Sarki wai mamanta ce ta zo
Tana fitowa ta karaso da gudu ta riko hannayenta a rikice ta ce" Anna lafia? Anna wa ya mutu? Anna na shiga uku me yake damunki? Anna me ke faruwa? Me aka maki Anna? Anna.....
Shiiiiit anna ta fada tana dora yatsarta saman leben Gaishat, itama tana kare mata kallo, yarinyar bata wani karu ba a jikinta na da, sai dan girma daga fuska da ta kara, duda jikinta bai nuna alamar wahala ba aman tana da rama, kanta daure ,
Kunyar Gaishat din ta ji ta kamata, dole ta rikice domin bata taba zuwa alkhairi ko tashin hankali ba, itace ma ke yin kokari idan ta san Abansu baya gari ta leko a tsaitsaye ta koma shima ba wani zantawa suke sai dai su bi junna da ita
Tunani ta afka shin fada mata zata yi ko kawai ta yi shiru ta juya
A hankali Gaishat ta dago habar mamanta, dara daran idannuwanta na gado ta saka cikin nata ta ce" Anna, me ke damunki? Ki fada mani kin ji? In sha Allah ko bani da maganin damuwarki zan taya ki da adu.a
Anna ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Gaishat, Algabitt ne....ya samarwa su Mariama mazajen aure wa.inda bama a niger din suke ba, kin san bani da labari tghmass ita a niger din ma aka bayar da ita, jiya Fatimata ta dawo, mariama fatimata ta kamu da cutar rashin rike fitsari , kin san ba maganinsa a kauye sai asibiti, baki ga fatimata ba, ta dawo wata iri,
Ga irin tsanar Agaishat (BAK'A) , ya sako yarinyar a gaba tamkar ya kasheta dan ya san gardawan da yake zuwa da su dan zaben mata ba zasu zabeta ba, shi ya sa nake kara barinta da datinta, mai yiwuwa ita ta tsira daga muguwar rayuwar da yake saka mini yaya
Shiru ta yi kanta sade tana gursheken kuka daga ita har Gaishat din,
Ajiyar zuciya Gaishat ta sauke ta ce" Anna zan zo gidan kin ji? Sai mu samo abinda ya samu mu samu shiga asibitin
Ido Anna ta zaro ta ce" ta yaya zaki fita Gaishat?
Gaishat ta yi murmushi ta ce" Anna, ki daina damuwa da damuwata, ni na dorawa kaina, tabas Aba ya yi auren dole da mutumin da bana so, mai mulkin garina aman shi mutumen jira yake in nuna bukatata a wani abin jiki na rawa yake yi min ko menene , bana tunanin fita zata zama damuwa tsakanina da shi
Anna ta sauke ajiyar zuciya, ta dago habar Gaishat ta ce" me ya sa toh ba zaki kyautata masa ki kontar da hankalinki ba? Shekarunnan ba fa kwanaki bane, ya ci ace kin zubar da komai kun fuskanci juna, ke Allah ya taimake ki kina cikin konciyar hankali kar ki bijirewa Allah mana
Gaishat ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Anna na kara nade jikinta da fuskarta wato dai tafia zata yi, ita ba zata ki su dawama a nan suna hira da mahaifiyarta ba
Tana ji tana gani Anna ta yi mata salama ta fice a gidan tana fatan kar ta hadu da wani a kusan gidan yarta ta fari , haka kawai take jin kunyar haka .......
Da dare, bayan ya gama salama da kowa ya nufo dakin mai motsa zuciyarsa, ya sani ne ta san sarai itace da shi aman taga damar ya tarar da ta rufe kofarta
Ga mamakinsa yana taba kofar ya tarar da ita a bude,
Turawa ya yi a hankali ya shiga da salama a bakinsa
Kanta ta dago duda tana jin kunya , ta yi kokari ta amsa salamarsa cikin nutsuwa tana dubansa
Da sauri ya karasa inda take zaune, da alama har wanka ta yi, na menene? Taba jikinta ya fara yi hankalinsa a dan tashe ya ce" GAISHAT baki da lafia ne? Me ke damun ki?
Dan bakinta ta turo, kafin take dauke hannun nasa ta kara turo bakin, murya a matukar kasalance ta ce" me ya sa ka zabi aurena ta hanyar baiwa Abanna damar ya ci gaba da tafka tsiya a cikin garinka?
Dakatawa ya yi, ya yi tsai yana kallonta, a hankali ya rungumeta a jikinsa ya ce" ba dai za.a yafe min ba du irin hakurin da nake bayarwa? Ki gane dan adam nake mai cike da izgili da sabo a doron kasa,
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce" ina so ka bar ni na je gida
Da sauri ya zabura ya cikata yana kallonta, muryarsa na rawa rawa ya ce" zaki tafi ki barni kennan? Yau kin fitar abinda ke cikinki shine zaki yi nesa da ni? Me yasa ba zaki yi mini adalci ba? Ina sane da du ranar da zan zo gare ki sai kin sha madaciya dan kar ki haihu da ni, na so daukan mataki a kanki aman bana iyawa Gaishat, ki yi mini adalci mana
Dora dan yatsarta ta yi saman lebensa jajaji abinka da jan buzu ruwan sarauta ko na kauye dawisu ne, ta ce" zama da kai yanzu na fara, ina son zuwa gidanmu ne dan kanwata ba lafia, muna son kaita asibiti, ka bani dama da ikon da zan yi bajinta a lamarin
Ajiyar zuciya ya sauke, ya rungumeta sosai har kamar ta yi ihun zafi, ya mikar da ita yana kallonta ya shiga warware lafayar da ta yane jikinta yanai mata kallon maita, haka ya idasa shigar da ita uwar dakanta cike da zumudi, wa ya isa in ba ita ba? Ita kadai yake tardowa har dakinta, hajia Gaishat mai sarkin garin *TIMIYA*
Kamar yanda ya yi alkawari haka ya bayar da rakumi har goma, ya bata kudi masu yawa ya lamunce mata zuwa gari dan kai kanwarta asibiti inda gari ya dauka ana ta lale lale gimbiya ta karbi soyayar sarkinsu, abinka da kauye har yar salah aka yi ta murnar hakan ...................

1⃣1⃣
........Niamey.......
Gidan Wardugu
Kawata, dan Allah wai da gadke kike? Gaki ga yan kaso wa.inda suka aikata mugun laifi? Gaskiya oga ya san kan mugunta
Walyn ta ja tsaki ta ce" ke, a dakin nan a nan suke fitsari, mata sai kawai ki ga an dage buje an tsirara fitsari a tsaye, basa kunya basa kyankyamin wajen , kai gaskiya Wardugu ni da shi akoy tashin hankali, ba ni ya wulakanta ba, walahi sai na rama!
Me zaki yi masa? Wardugu ne fa? Kin manta waye shi? Ko mu da muke gari bama rayuwa da shi mun san waye shi, koda kina kema jinnin tubawa ba lale ki iya da rigimarsa ba, ya hada abubuwa da yawa ne, kin ga shine da daya kwalin kwal a wajen iyayensa, shine Wardugu mai sunnan rikitatu a cikin ku, shi ne Batube, kuma shi ne Soja! Wardugu kakarfa, tsayaye, isashe, hamshakin......