← Book details Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 110

Sashe 38

Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read

Kan Wardugu a kasa a hankali ya dago jajayen idannuwansa ya sauke a fuskar mahaifinsa, Mahaifinsa, ubansa, wanda ya haife shi, a yau ya so a ce wani ne ya kai hannunsa jikinsa, kai kai kai, balaki,
Ido cikin ido suke duban juna, Marahut ya ce" ko me ka zama, ko me kake takama da shi dai haihuwarka aka yi, na yi tunanin rashin mutuncin naka zai saka ka daga hannu ka rama! Ka rama marin mana Wardugu!

Wardugu ya sakar masa murmushi mai ciwo , a hankali ya ce" ko shege mai mutunci ba zai rama ba bare kai da ka haifi dan halal ka bashi tarbiya?, kar ka daga murya yarana su ji, domin ban san in zan iya rike kowa, wai ina gudun ba nan gaban idona ba, ka san soja shegen yawo ne da shi, gashi da ramuwar gaya,
Ka je kawai Marahut.

Jikin Marahut ne ya yi sanyi, ji yake dama da hali da ya rungume shi ya shafa wajen da ya mare shi ya bashi hakuri,
A hankali zuciyarsa ke sauka har ya ji dumbin kaunar dan ta kuma mamaye khalbinsa bashi da wani , baya tunanin zai samu daga shi, fatansa su sauko daga dokin zuciyar da suka hau bisa gangancinsa, sai dai ya rasa yaya zai yi, shi ba zai duka gabansu ya basu hakuri dan ya kara aure ba, su ya dace su yi hankali su zubar da makaman yakin su, yanzuma ba wai ya zo ne dan Wardugu ya yi magana harkar Aisata ba, shima yana iya sakawa a saketa aman ya barta ta je ta yi kasonta kawai domin ta taka doka, ciki harda ta musulunci , da aurensa a kanta take bin wasu mazan.
Ya zo me dan ya kara ganninsa su sami hira ta kusanci na da da uba, sai dai ga yanda ta kare,

A hankali ya juya dan barin Office din,
Ja ya yi ya tsaya, a hankali ya dawo ya dube shi, hularsa da ta dage ya janyo ya gyara masa a kansa, ya gyara masa gaban rigarsa da kyau ya ce" Allah ya yi maka albarka, na yafe maka dukan abinda ka yi min wanda na sani da wanda ban sani ba, Allah ya kare gabanka da bayanka!

Yana gama fadar haka ya juya ya fice a office din,

Ran Wardugu a cakule ya hade takardun ya fito gaba dayansa a haukace ya mikawa Lieutenan Jalo takardun bai masa magana ba yana kallon mashin dinsa ya fice ya bar shi a wajen aikin ya kama tafia a kafarsa cikin sauri, ya yi niya a kafa zai je gidansa ba zai hau mota ko mashin ba, ya ki din , kai bama zai kuma hawa ba! Zai je a kafarsa , du wanda ya fasa kawo masa wargi ya ki Allah! (🥴 wani da laifi , wani da shan duka? Tap🤔),

Bayan kwana biyu, fitina ta dan lafa gefen Wardugu,

Juma.a ce yau, ranar da ake bada damar shiga gannin yan gidan kaso harma a dan jima a wajen su,
A wannan ranar ne mutane ke cika prison dan gannin nasu,

Wannan damar Walyn ta rike ta yi shiga irin ta larabawa ta yane kanta da dan kwalin bakar abayar da ta saka ta yane har habarta sannan ta saka bakin gilas,

A kafa ta samu ta fito bakin titi nan ta ja ta tsayar da mai taxi ta yi shatar ita daya.

Basu zame ko.ina ba sai justice ta ciri takardar gannin dan prison ya dauketa ya sadata da gidan kason,

A hankali ta cire gilas din idonta, sannan ta dan ja mayafin dan bude habarta dan kar ta jawa kanta matsala da masu tsaron gidan kason

Takarda ta nuna, ta je saman kuje ta zauna inda aka shiga aka kirawo mata wanda ta zo nema,

A hankali take takowa har ta karaso wajen warda aka nuna mata a matsayin uta ke nemanta,

Kallonta take, irin kallon san sannin wacece? Hakan ya sa Walyn ta bude rufarta dan ta shaida ta,

Murmushi Aisata ta yi tana dubanta, aman a kasan zuciyarta mugun kishin Walyn take, kai da tana da dama da ita ce ajalin yarinyar da ta auri gwarzonta!

Walyn ta kare mata kallo sama da kasa, cike da yanka da jan aji ta ce" *wanene shi*?

Bata amsa ba , sai da girarta irin na rikakun yan duniya da suka san kansu ta yi mata tambayar *Wane?*

Walyn ta fara shaka ta dubeta da kyau ta ce" *waye malamin da ya miki aiki kan Wardugu da mahaifinsa?* waye shi?, idan kika fada mani komai, zan saka a fitar da ke daga wajen nan.

Murmushin rainin hankali ta yi tana dubanta, cikin kissa ta ce" kina da damar sakawa a fitar da ni din ne kika shigo cikin gidan kaso dan samu adress din malamina?
Kina son samun kanki ne a wajen Gwarzona?

.........

🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫

Na *SAJIDA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

4️⃣0️⃣

*Walahi ni ba kowa bace, ni ba komai bace, Allah ne gatana👏🏻😕👏🏻*

Walyn ta zaro ido, rai bace ta ce" zan datse harshen ki idan kika kuma kiran mijina da gwarzon ki!

Aisata ta ce" da kuwa na ji dadin yin makota da ke, da zan gani idan kema da ya kilace zai saka ki a kaso dan kin zalinci wani!

Walyn ta tsareta da ido, a hankali ta ce" zan biya ki, ki fada min kar lokacin da aka bamu ya kare ,

Aisata ta ce" na sani kina da damar iya biyana aiki, dan ni mai nema ce, ina nema kamar me, kudi baya isata, da yana isata da na tsaya da sirikin ki kawai!

Walyn ta ja tsaki ta ce" lokaci!

Aisata ta ce" kar ki damu, yau ai akoy lokaci isashe ,

Walyn ta kuma tsareta da ido, ta ce" me zai rage ki dan kin fada mani? Kin san dai kin haramta wa wardugu tunda kika kwonta da ubansa!

Aisata ta lumshe idannuwanta, a hankali ta lashe lebenta na kasa, rage murya ta yi kamar zataiwa Walyn rada ta ce" *Ke ba fa kowa ke da haram ba*,

Walyn ta daki table din ta ce" zaki fada mani ko ba zaki fada mani ba?
Har sai da hankali ya kawo kansu inda wani soja ya karaso yana tambayar lafia?
Nan Aisata ta kalamance shi da"Oga ba komai,

Juyawa ya yi ya koma, Aisata ta dubeta da kyau ta ce" kina tunanin na taka farar kafata na je wajen Boka dan tsibu dan ya malaka min saurayi? Kina tunanin aikin boka ya malaka min mazaje biyu ?

Walyn ta ce" kin gane, ni fa ba yarinya karama bace, kuma na san bariki ki ka yi ! Dan haka kar ki bi min ta wannan hanyar ba gyara mu zata yi ba.

Aisata ta ja rigarta kadan, hakan ya baiwa saman mamarta damar fitowa sosai, ta ce" *kin ga malamaina*

Walyn dake kallonta ta yi dariya tana girgiza kai ta ce" ba dai Warsuguna ba, Wannan abin bai isa ya ja ra.ayin namiji mai sunna namiji ba!

Aisata ta ce" haka ya fada maki? Ko irin zaman da kike yi da shi?

Walyn ta ce" ba sai ya fada mani ba, haka ne, Wardugu kamili ne, girman kansa ba zai bar shi bama ya lura da wani abin jikin yar bariki!

Aisata ta bushe da dariya har tana rike ciki, nunata ta yi da yatsa ta kuma kecewa da dariya, sai da ta yi mai isarta ta ce" lale kin rako mata, ina mai baki albishir din in dai kallon da kike masa kennan ki farka tun kafin ki kuma jaza mana wata yar balakin da ta fi mu ta karbe mana Gwarzon mu!

Walyn bata ce mata komai ba, sai duban kin raina min wayo da take mata,

Aisata ta tsagaita tana duban Walyn ta ce" Walyn Wardugu, ba kowace mace ce ta san kofar boka ba, koda kina jidana da na yi bariki dan na fita da d'a na kuma dawo kan uba , ina mai tabatar maki ba boka ne ya tsaya min ba.

Ya zan zo cikin wannan wajen mai fitar da wari ki saka ni gaba kina yi min rainin wayo? Walyn ta fada,

Aisata ta juya idannuwanta ta ce" kar ki yi garaje, zuwa gidan yari rubutu ne wanda Allah ke kadara shi, diyawa a wajen nan basu taka basu karya ba....
Walyn bara ki ji wani abu....: du namiji na duniya yana da abinda idan ya ganshi a gabansa yakan ji ya rasa dabararsa,
Wani namijin mace mai kissa, mai kisisina, mace mai kyan dan maciji ke tafia da imaninsa, wani namijin mace mai adini mai rufe jikinta, mai mutunta kanta ke tafia da imaninsa, wani namijin yana son mace mai halaya irin na yan bariki ce zabinsa, wanin mace mai kyau ko muguwa ce zasu taka rawar, wanin yana son mace mai shiru shiru, wanin yana son mace mai kamar maza irin mai kafkaf da ita, wani baya jure gannin mace a cikin yannayi na abin tausayi...zaki ga ya fada tarkon kaunarta, wani farar mace ce zabinsa, wani kuwa *bak'a*, ke wani duka biyun yana so....tambayar a nan shi ne *Sai ka karanci mutun kake gane waye shi harma ka tabo wajen da ba zai jure ba, da kansa zai nuna shi sai kai*,

Walyn kallonta kawai take,
Chapter 38 · 0% Book details