← Book details Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 110

Sashe 8

Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read

Ke meye haka? Walyn ta fada tana kallon kawar tata,
Ta ce" ya zaki tsaya kina koda min miji sai kace wata mai son min miji? Toh bara ki ji mu a yarenmu ba.a yiwa mace kishiya sai ta cika wa.adin yin hakan, duka duka shekarana biyu da aure da mijina, ko na kai shekarun da yana iya kara wata Wardugu haramiyar wata mace ce a nan duniya, ban ki ba lahira idan ya dace da aljanna!

Murmushi ta yi tana kallonta ta ce" dadina da ke saurin hawa , toh yi hakuri ni ban kai abin can ba ..........

Bakinta ta tabe ta ci gaba da shafa cream dinta kan kurajen cizon sauron da suka yi mata cin balaki a cikin cel din nan, rabonta da ta saka kafarta kofa tunda abin nan ya faru, gashi ta rasa Wardugu a waya kwata kwata, !

Dogo ne fari kar, datijo ne christa sunansa Docter Lucien, kwararen likitan mata kennan wanda ya karanci abin kuma ya lakanta,

Allah ya taimaki su Anna sun samu gannin Docter Lucien a dasha kuma tausayin irin ciwon da ya gani bayan ya sha fada ya karbe su ya shirya shiga tiyata da ita a washe gari wanda cikin ikon Allah sai da ya dauki awa shida kafin yake fitowa daga dakin tiyatar da ita shi ya hada zufa hakama masu kama masa wanda ba.a jima sosai ba aka gurgurota a gadon mararsa lafia aka kaita dakin da ake kontar da masu yoyon fitsari

Jigum suke zaune suna mamakin wai asibiti ce haka, su kam tunda suka shigo garin a tsorace suke da yannayin tsarin gari, gini ne kala daban daban bene kai kasa na cin kudin masu kudin birni ....

A hankali ta shiga bukar tana dube dube kafin take kallo shi, a kwonce yake , idannuwansa a rufe kamar marar lafia

Da sauri ta karasa ta ce " Sofo?

Firgigit ya buda idannuwansa ya sauke saman kanta,

Kokarin tashi yake wanda da kyar abin tsufa ya samu ya zauna yana kallonta, murya na rawa irin ta tsufa ya ce" ina kika shiga? AGAISHAT zuciyata ta rikice na rashin gannin ki, na damu na kasa baci, kin ji har zazabi nake dan bana ganninki yata, ina kika je kwana biyu? Kin san ke nake gani ina jin dadi, kece mai daukana tamkar mahaifi, zo zo na ji me akai maki? Wa ya taba min ke ?

Karasawa ta yi tana sakar masa murmushi ta kamo hannunsa ta damka masa goron da ta siyo masa tun wancen ranar, murya a nitse ta ce" mun fuskanci matsaloli ne a gida Sofo, aman yanzu alhamdulilah mun gode Allah, Su Anna sun tafi birni Sofo, muma watarana zamu je? Zaka tafi da ni nima na ga birni?

Ajiyar zuciya ya yi jin ba abinda ya sameta na tashin hankali, ya lalubo karfen gurza goronsa ya mika mata ta mike ta darwaye ta dawo ta raba goron hudu ta maida hankali ta gurje masa shi tas ta mika masa ai kuwa ya hambuda yana tsotsa yana dan juya kai irin ya ji dadin goron

Can ya ce" Birni garuruwa,
A birnima akoy garin da dadi ne da shi sannan akoy wanda sam ba zaka so rayuwa ciki ba indai kai din bako ne
Birni tana tatare da abubuwan firgitarwa, murane sun yiwa abin hawa irin mashin mota yarda, sun yarda da su suna halaka su

Tagumi ta yi ta ce" suna halaka su kamar yaya?

Ido ya dan zaro ya ce" zaki ga dan birni idan zai yi tafiyar da ba wata nisa ba, ba jeji ba, ba abin tsoro a hanya ba, dan tsabar sangarta da son jiki sai ya dare abin hawa abinsa ya tafi a dan kankanin lokaci in abin ya zo da karar kwana sai ya juyeka tamkar tuwon masara nan zigib ka mace shikennan sai kiyama

Murmushi ta yi ta ce" toh ba kace ajali na tarda mutun du inda yake ba? Mutuwa ai kai ka fada min ba.a gudunta kuma ba.a boye mata, kuna Anna ta ce ita mutuwa lokaci ne idan lokacinka ya yi ba tsumi ba dabara zata daukeka ne ko waye kai ko me kake , kai ka ce min mutuwa mai yanke kauna, takan raba da da uwa, miji da mata, kuma kace min kowani bawa da ajalinsa a duniya

Tsofo yama ta murmushi yana dan barin jikin nan na tsofafi ya dungure kanta ya ce" haka ne Agaishat, Mutuwa gaskiya ce, Allah ya sa mu cika da imani
Ta amsa da amin...., ta ci gaba da fadin " ka ce a birni suna da wata kalar madara banda irin wannan tamu ta rakumi ko shanu? Ina so idan ka je birni ka kawo mini in kaiwa Anna ta sha ta ji itama

Kansa ya girgiza kawai, domin ya lura yau du labari ne a kunshe a bakin Agaishat, wai shi zuwa birni, shi da a yanzu salarma baya iya zuwa masalaci kafafuwa sun kiya, ga tsufa me zai je nema birni? Sai dai idan har kadarar makwoncinsa a can wannan kuwa ya san ko ta wani hali Allah zai kai shi..............

Dago kanta ta yi ta ce " ka san me?

Ya gorgiza kai alamar aa

Ta ce" wankana sau biyu, su Mariama sun bani kaya suka saka na yi wanka

Murmushi yake na jin dadi, bai taba yarda a duniya Allah na hada jinnin mutun da mutun haka kawai sai a kan yar yarinyar nan,
Jinta yake tamkar jinninsa, sonta yake har bargonsa, baya son damuwarta, fatansa Allah ya bata miji na gari komai talaucinsa domin ba zata kasa ratuwa da talaka ba, a hakan rayuwarta ta ginu, gidansu ba laifi su ba talakawanan tukuf bane domin dadaya ne gidajensu ke zagaye a garin aman ita rayuwarta irin ta yayan talakawan nan tukuf ce masu wadatar zuciya,

Tana ta zubar ta mike ta shiga dan totona dakin kamar yanda ta saba dan dudubawa da kyau ta kashe kunama, domin kunamu na cikin kasa bakaken nan wa.inda idan sukai cizo in ba.a yi gagawar shan magani ba dafin na saurin kashe mutun , sune a cikin kasar garin kamar me, yan garin sun iya rayuwa da su, domin sun san inda zasu same su sun iya kashe su tamkar yanda ake kashe cirnaku,
Ta samu ta kashe wajen hudu ta cilar waje ta dauku tulu ta ce" sai na dawo

Hannu ya daga mata yana murmushi ya ce" Allah ya tsare ki

Yana kallonta har ta fice , ya samu kansa da zirarar hawaye, ya ce" ya Allah baka barin wani dan wani ya ji dadi, Allah ka sa , ka yarda, ka aminta , ka bani ikon gannin ta shiga hannu mai kyau kafin na koma gareka .......

*Niamey*

Kan Anna kasa take tafiya domin bata son gannin irin yanda mutanen ke cuwa cuwa, a can kauye shiru ne, ba hayaniya , ba komai, sannan mutanen basu fi a kirga ba, hakan ya sa du idan ta fito daga dakin da Fatimata take koda dan ta leka ta ga safiya ce rana ne ko dare ne? Sai ta rikice

Ji ta yi ta ci karo da mutun, da sauri ta dago dan bayar da hakuri sai dai me, gani ta yi ya zaro idannuwansa yana kallonta, a hankali ya nunota da yatsarsa sai dai wani abin ya ce masa Haba docter, haba docter, wacen koda jikin manyanta ya kamata ba zata koma haka ba, kuma ita batuba ce ba buzuwa ba, wannan kuwa buzuwa ce ta sha bakaken kayanta, kai bama zai yiwu ace ita bace,

Da sauri ya ce" yi hakuri baiwar Allah

Bata san ta ina ta iya hausa ba, bata san ya aka yi ta ce" Ba komai yi hakuri kaima

Gaba ya yi yana dan waiwayenta, shi dai rabinsa da wancen dama familynta tunda aka hana masa aurenta, tun suna saurayi da budurwa, muryar wancen da wannan ba daya ba, sannan kai ka daina tunani kan matar nan mai yiwuwa matar aure ce
Da sauri ya kawar da maganar a ransa ya nufi office dinsa yana dafe kansa a fili ya furta" ya dace na ajiye aikin nan, na jima ina fama har jikin tsufa ya zo....

Tunda ta koma dakin ta yi shiru tana tunani,

Gaishat ce ta salame sallah ta juyo tana kallon maman nata ta ce" Anna me ke damunki ne??

Anna ta dan yi jim ta dago ta ce" wani yare na yi yanzu Gaishat, wanni mutun na kade ya min yare na bashi amsa tartar tamkar na iya yaren

Da mamaki Gaishat ta taso ta zauna kusa da ita ta ce" me kuka ce?????????

🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫

Na *SAJIDA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

1⃣2⃣

Cikin yaren buzanci Anna ta maimaita mata abinda suka ce

Da mamaki take kara kallon Anna ta ce" kuma baki san sunnan yaren ba?

Anna ta girgiza kai, da yannayin damuwa a fuskarta ta ce" ban sani ba, kuma da dukan alama ba yaren faransanci bane domin likita ya yi ta yinsa a gabana ba wani fahimta nake ba, sannan ba yaren nan da muke ji wajen masu siyar da abinci a garinnan bane wato Zabarmanci, wannan yaren shima daban yake

Gaishat ta mike tana kallon ledar fitsarin fatimata ta ga bata cika ba ta ce" Anna, ko mu koma wajen mutumen ku kara yin yaren? Anna ko haka na da nasaba da asalinki?

Nan da nan Anna ta ji ranta ya baci, asalinta? Kennan dai yayanta ba zasu daina daga mata hankali da wannan kalmar ba, rai a bace ta ce" ina ruwanki da asalina Gaishat? Ina ruwanki? Tana gama fada ta fice a dakin don ji take zuciyarta sai tukuki take mata na bacin rai
Chapter 8 · 0% Book details