Sashe 25
Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read
Da mamaki take kallonsa, ranta ne ya baci ta ce" aman baka ji wace nace maka tana jira ba?,
Domin ta sani ne, yana mugun daraja mahaifiyarya, ko gaisar da ita zai yi sai ya dan duka, aman yanzu ta fada masa ta ga ya wani kwonta abinsa,
Wardugu ta kara kiransa tun karfi,
A fusace ya dago zaune , murya a bace ya ce" ba zan je na gaisar da mamanki ba, na gaji baci nake son yi ki fice mani a daki!
Ido ta kwalalo tana kallonsa, kafin take juyawa ranta in yayi dubu a bace yake, tana son tsayawa ta ja maganar aman wani abin na hanata, dan kuwa dukan alamu sun nuna idan ta yarda ta kawo masa raini komai na iya faruwa ,
Juyawa ta yi tamkar zata tashi sama ta fita a dakin,
Karamar wayarsa ya bude,
Sheik ibrahim ya danawa kira,
An jima tana ringin kafin yake dagawa da salama,
Wardugu ya gaisar da shi da tambayarsa jama.a,
Sheik ya amsa yana mai tambayar Wardugu Aiki,
Wardugu ya amsa shi a nitse ya ce" Malan, a kara saka mu a adu.a,
Sheik ya yi murmushi ya ce" Wardugu , na ganka a tv, fatan Allah ya tayaka, Allah ya baka ikon yin aikin kirki, sai dai zan kara fada maka, a duniya karka ce sai ka birge kowa, ka yi lamarinka domin Allah, kar ka saka fushi ko gaba dan Allah ya baka dama mai girma ta jan wanda ka yi niya, ka ci gaba da kawar da kanka a kwadayi , sannan ka ci gaba da jan istighfari kana kaiwa allah kukanka ka ji?
Wardugu ya amsa a mutunce sukai salama,
A hankali ya lalubo cazbaharsa fara kar tana ta kanshin turaren ruwa ya shiga ja daga kwoncen yana ta jan astghfari,
Me mijinki ke takama da shi a duniya Walyn? Ya rasa wa zai rufe sai aban iman? Ko dan yana auren yar yayata ai sai ya daga masa kafa, dan kawai ya kama da shi a wannan wajen, wajen ba na ubansa bane? Zance wajen sunnansa ma gare shi! Me yake tunani? Dan yana sanye da rigar iko shikennan ? Ai idan shine yau gobe ba shi bane zai ringa yiwa mutane rashin mutunci! Tunda haka ta faru muke gidannan aman ya zo ki wani zo ki ce wai ya gaji? Gajiyar kaniyarsa, mu da muke nan bamu gajin bane? To idan mijina ya kwana a cel nima na dauki alkawain sai na tozarta Wardugu sai na saka wardugu ya shiga uku, sai na
Aunty! Walyn ta fada tana daga murya sosai,
Da yatsarta daya ta ce" ke a wa? Wacece ke? Kike ikirarin tozarta Wardugu bayan Allah ya rike? Ke kin san da za.a shige shi da an shige shi ba yau ba Aunty! Wardugu baya zuwa maula, hukunci kuwa idan ya kama zai yiwa ko wani dan buro........ba, meye? Takamarki ki yi masa shari, ki hada shi da malame, ko ki same shi ta hanyar abin duniya?
Ban ce sihiri ba zai kama shi ba domin wanene shi, sai dai na miki alkwarin tunda kika fadi haka , sai dai mu mutu baki daya,!
Mahaifiyarta ce ta kasheta da mari, rai bace ta ce" kan namiji? Kan namiji zaki ciwa kanwata mutunci? Namijin ne ya kai dan goyo har haka? Ke Wardugun da kafin aurenku ma sai da ya karya maki hannu sau biyu shine kike daga jijiyoyin wuya dan ance za.a taba lafiarsa? Kin manta dan ya kauce ki malaki wannan daula na yarda yake tata maki rashin mutunci? Idan kin canza ra.ayi na sani da wuri dan Ubanki!
Wakyn dake yashe tun marin magaifiyarta, jikinta a mace, takan mance du wani kudirinsu idan tana tsaye gaban gwarzonta, namiji ne Wardugu, can dama tana sonsa sosai, damuwar kuna tana son kudi sosai!
Mu.azam, tashi ka kai ni ya sha maganin bakin nan ,
Ayya ta fada tana nuno masa wani dan kuli wai maganin baki ne dan kar baki ya fada masa
Mu.azam dake zaune kafa tankwashe Agaishat na koyar da shi bakara ya dago da mamaki yana kallo Ayya,
A hankali ya ce" Ayya, idan muka yarda muka fita a yau fa kama mu za.a yi a rufe, sai karfe takwas na safe za.a tsayar da kamen nan, ki rufa mana asiri Ayya kin j?
Ayya ta zaro ido ta ce" dan ubansa a rufe mun, bafa zai yi baci ba sai ya sha maganin bakin nan yau yanzu yanzu dan haka tashi mu je Mu.azam,
Mu.azam ya mike yana ayyana ta faru ta kare a ransa, dan ya san in dai suka fita titi za.a kama su ne, za.a rufe su, daga shi har Ayya har Agaishat din,
...........to fah🤣🤪🤪🤪🤪✌🏼
🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
2️⃣7️⃣
Mu.azam ya ce" Ayya, ki bani na je na kai masa, kin ga ko an kama ni kadai ne za.a kama,
Ayya ta ce" yo kai na d'a bane, a hada har mu a rufe, ba yace doka ta hau kowa ba? Na tabata an hada da iyayen mutane a wajen,
Mu.azam kam ya rasa ya zai yi da Ayya , ta kuwa coge kofar daki inda Agaishat ma ta fito tace ba zai yiwu Ayya ta tafi ta barta ba,
Kallon agaishat yake kasa kasa, a hankali ya ce" idan aka rufe ki Agaishana, ba zan iya hakura ba, kar ki biyo mu na roke ki,
Irin na yara ta yi masa da kafadarta irin ta kiya, tama rigayi kowa karasawa wajen motar bayan ta amshi maganin bakin na hannun Ayya,
Haka Mu.azam ya fitar da motar dake da lambar Wardugu, ya dauko carte dinsa ta shaidar shi likita ne, da carte didentité dinsa,
Fitowa ya yi da motar Ayya ta shige baya ta hakimce, Agaishat ta shiga gaba aman a ranta a tsorace take, tana tsoron sojojin garinnan, daman ba.a saka soja a lamari a niger sai abin ya baci, su fa ba ruwansu hade kowa suke, idan ka yi masu gardama su tataka banza su barka nan zubde tamkar kayan wanki,
Tuki yake zuciyarsa kuwa sai adu.a yake, Agaishat ma adu.ar kawai take inda Ayya ke kara buga lambar wardugu aman a kashe, bata shigama bale a dauka,
Danja na tsayar da su aka haske su da cocila dall a idannuwansu,, gaba da baya sojoji suka zagaye su har mutun uku,
Na kusa da direba ne ya kwonkwasa kofa,
Mu.azam ya bude yana dubansa,
Mutumen ya ce" motar Gn ce Oga,
Ya ce" eh na gane ai,
Ya ce" malan daga ina , kuma ina zaka je? Wa ka dauko? Sannan ka bude mana bayan mota zamu yi bincike,
Mu.azam ya fara bude masu motar, sannan cikin nutsuwa ya ce" ina tare da mamanmu ne, mahaifiyar Wardugu da kanwarmu Agaishat sai ni kuma amininsa ne, daga gida muka fito zamu je gida wajensa bisa umarnin mamansa,
Menene shaidarka? Sojan ya tambaya ba alamun wasa,
Mu.azam ya mika masa cartocinsa, sannan ya sauke madubin bayan ya dayan ya leka wajen Ayya,
Kwarai kuwa itace, waye bai san Ayya ba? Mahaifiyar General,
Gaishe da ita ya yi cikin mutuntawa ya ce" yi hakuri mama muna bisa aikin mu ne, ki tabatar mana da abinda ya fada,
Ayya ta ce" eh haka ne, ina son gannin Wardugu me yanzu yanzu,
Sojan ya gyada kai yana kallonta,
Wanda ke bincika cikin motar ya shaida masu ba komai cikin motar, dan haka ya mika masa takardarsa ya basu damar su fice
Cikin ikon Allah haka sukai ta haduwa da sojojin nan suna kara titsiye su ,
Harda wanda bayan dukan bayannan nan yace ai shi bai wani san Ayyar ba a bashi shaidar da ta fi haka,
Nan fa aka sha rigima da kyar masu taya shi suka tsawatar masa ya batsu suka tafi,
Tun abin karfe tara sai kusan sha daya suka karasa gidan Wardugu nanma suka tarar da wani balakin an hana iyayen Walyn fita sai dai su kwana a nan in kuwa suka fita aka kama su toh su suka gano, sun izata sai balaki take kan wardugu ya fito ya raka su ko ya basu shaidar da zata sakasu su tafi har gida lafia,
Suma su Mu.azam sai da aka titsiye su kafin suke samun shiga gidan,
Mu.azam na tsayawa ya sauke ajiyar zuciya yana kallon hajia rigima, domin Ayya ta hade rai ta yi kicin kicin da fuska tana kallon yanda suke tsatsaye suna ta magana suna tafa hannu suna balaki,
Mu.azam ya ce" Ayya, kar ki kula koya na roke ki,
Ayya ta yi murmushi ta ce" oh yarona, yanzu kai ke yi min gargadin kar na kula kowa, ai ka san bana kula mutumen da bai iya tsawatarwa zuciyarsa ba!
Bude motar ta yi ta sauka,
Ai kuwa tunkarar wajensu ta yi direct ba wani tsaye tsaye,
Tana zuwa ta ja ta tsaya itama tana yi masu kallon da suke mata,
Da yake akoy wuta ko.ina haske ya garwaye gidan kowa na gannin kowa ne,
Ayya bata fita sai ta shirya ko fitar da a rikice take ne, dan haka yanzuma sai baza kanshi take, ga lufayarta ta nada mai ruwan ja da baki, ta sha awarwarenta na zinariya,
Walyn ce ta ce" ina yini,
Ayya ta kai dubanta wajenta ta ce" lafia, sannan ta mayar da dubanta wajen iyayen Walyn din tanai masu kallon ido cikin ido,
Mahaifiyar walyn ta miko mata hannu ta ce" Hajaju ne, uwar gidan *MARAHUT* ke ce da tsakiyar daren nan??
Ayya ta sakar mata murmushi ta mika mata hannun itama ta ce" wa.alaiki salam maman Walyn, ke ce a gidan Wardugu da wurin nan haka,
Kanwar maman Walyn ta kali Walyn ta kuma kallon sirikan biyu, ta juya bangaren Walyn tana ayyana taf, lale ana cakwakiya a gidan nan,
Ita kuwa walyn kitson kanta kawai take sosawa, susar da bata san ko ta meye ba,
Ayya ce ta fara cika hannunta ta kuma kallon Walyn ta ce" Aa, Walyn yaron nan yana nan ne dai ko? Bara na shiga na gani Wardugu sarkin aiki!