Sashe 33
Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read
Dago da idannuwanta ta yi ta ce" baba tsofo ya ce shi ne ya fara kiran sallah , ya ce mutun ne mai daraja, makusancin fiyayen halita,
Mu.azam ya gyada mata kai kafin yake ciro wayarsa ya samo hoton ka.aba ya ce" zo ki ga ka.aba a hoto Agaishat, zo ki gani...
A hankali ta matsa tana kallo, kalar bakin ya tafi da imaninta, abin ya yi mata kyau a ido, a hankali ta kai yatsarta ta dan shafa hoton,
A hankali ya ce" ba wani bawan da ya fi daraja, ya fi kusanci fa ubangijinsa sai mai yi masa biyaya, mai tsoron shi, mai kiyaye dokokinsa, a cikin nan kin ji an ce *Farar fata ta fi bak'a?*
Agaishat da take jin wani yamyamyam a jikinta na dadi ta girgiza kanta,
Mu.azam ya ce" makafi ne ko kwakwaluwar su bata ja? Ya aka yi basu yiwa abin kaunata wawa ba?
Da sauri ta kallo shi,
Kansa ya dan sada ya ce" kina da tsararen kyau, fitinanan kyau, baki da tsayi Agaishat...baki da kiba har can, yannayin jikin ki ya tafi da yannayin tsayin ki,
Bakin ki ba mai tabo bane bare shaida, gaba daya ya tafi iri daya ne baki mai haske mai nutsuwa, agaishat, fuskar ki yar doguwa ce mai dauke da dara daran idannuwan da a kowani yannayi kike su kadai sun ishi mutun, Agaishat Allah ya tsara ki da hanci mai tsayi mai yan kofofi wanda ya yi das da dan madaidaicin bakin ki,
Rashin hayanniyar ki ya hadu ya kara kawata halitar ki, ke da ba dan kar na kauce hanya ba da na fada maki sauran tsaruwar ki,
Dan dakatawa ya yi gannin yanda ta zuba masa ido, sai a lokacin ya tuna ya saki baki sai zuba yake mata,
Dan kimtsa kansa ya yi a hankali ya ce" Agaishat arrrakam (Agaishat ina son ki),
Wata irin faduwa gabanta ya yi, da wani irin firgici ta akle shi, tsoro, mamaki, surprise, murna suka hade suka saka jikinta ya dan fara rawa, So na? Ji ta yi wani nauyinsa ya diri mata,da sauri ta sada kanta kasa, kafin take mikewa da wani irin sauri ta jua inda Mu.azam ya mike yana kiran sunnanta daidai Wardugu ya yi kokarin kawar da kansa dan kar su ganshi bayan ya jima wajen,
Ganninsa ta yi yana ta faman taba labulen ayya wanda ke gyare tsaf a wajen aman kamar wanda yake gyara shi,
Kanta ta shiga sosawa kafin take dan rabar gefensa ta shige ta taka matatakalar da gudu gudu ta nufi dakin ta,
Da ido ya bita, da wani irin kallo, a hankali ya lumshe idannuwansa ya juya ya fice a dakin ya nufi wajen mu.azam da ya koma ya zauna ya dan dafe kansa da hannunsa cike da tsoron kar a je ta ki karbar sa,
Gaban wardugu ya ji na wani irin gudu wanda har ya ji wata yar zufa ta karyo masa,
A dan hanzarce ya karasa wajen amininsa yana mai cike da zulumin yannayinsa, a nitse ya kai hannunsa ya ce" Mu.azam?
Agaishat na shiga dakinta ta karasa da sauri wajen madubi, lufayar jikinta ta warware ta tsurawa kanta ido, du abinda ya fada take son gani sai dai ita bata wani gannin kyanta, , .....
A hankali ta kai zaune ta cuje abinda ta daure gashinta da shi wanda hakan ya baiwa gashin damar zubowa baki dayansa ya yi lumbuk a jikinta, hannayenta ta cusa ta fashe da wani kuka mai zafi, a hankali, muryarta na rawa ta ce" Anna, ina kike? Anna wai yana so na? Ashe nima mutun ce Anna? Anna wai ina da kyau, wai nima mai daraja ce, Anna nima na yi saurayi...........tana kukan kuma ta shiga dariya a hankali ta furta" Mu.azam, nawa😌😌😌😌😊😊😊😊😊😊😊
I.m sowi fans , jiki da jinni ne 🤦♀
🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
3️⃣5️⃣
A hankali Wardugu ya kai hannunsa ya taba Mu.azam, murya a sanyaye ya ce" Mu.azam?
Da sauri ya dago da kansa daga yannayin da ya afka, ya kali Wardugu da kyau kafin yake sakar masa murmushi,
Wardugu ya ce" me me ke damun ka?
Mu.azam dake dubansa ya dan sada kai, ya kuma dagowa yana dubansa ya ce" jinta nake a raina har jikina Wardugu, sai dai ban san ba ko zata aminta ta aure ni a dan kankanin lokaci kafin mai yiwuwa ta yiwu da ni?
Wardugu ya ji gabansa ya fadi, Allah yana ganni idan da abinda ke tayar masa da hankali a yanzu bai fi rashin lafiar Mu.Azam ba, lamarin na girgiza shi in ya tuna, yakan tsinci kansa ba karfi bare laka a jikinsa idan ya tuna, .......
Duk da ya fahimci wa yake nufi aman sai ya kashe ido guda yana kallon Mu.azam ya ce" kai, soyaya ka afka daga zuwa garin mu? Fada mini wacece mai sa.ar samun abokina ?
Mu.azam ya lumshe idannuwansa ya ce" Wardugu, na kan ji wani iri idan muna hira da kai a yanzu, domin du ka canza min kan da, a da idan muna hira tamkar yaki muke, ka warto ni na tsokaneka mu yi ta shirirta har sai an shiga tsakanin mu, aman a yanzu du abinda zan maka sai na ga ka wani yi shiru ka kyale ni ko kuwa ka wani lalaba ni, malan matarka ne ni? Ko dan bani da lafia? Ni irin yanda muke da ya fi birge ni, sai ka wani dawo ladabi?
Wardugu dake kallonsa ya ji zuciyarsa ta mugun karye, hakan ya saka wata zufa ta karyo masa, a yanzu da suke zaune a haka ba mamakin shi wardugun shi ne gawar fari, aman kuma rashin lafiar Mu.azam da ta bayana kanta ne ake kiran kisan mumuke, domin dai ta hana kowa walwala tsakanin mutane ukun nan, Mu.azan din, docternsa, sai Wardugu da ya sani shima,
Wardugu ya saka hannunsa ya share gumin da yake , ya miko hannunsa kusan na Mu.azam ya ce" wa kake so? Ko yar gidan waye, ko wa take takama da shi nan duniya sai ta aure ka, kuma dole ta so ka!
Mu.azam ya kwace hannunsa yana dubansa da yannayin tausayi, ya san waye Wardugu farin sani, wannan yannayin da yake ciki yayi imanin da ace zai samu kuka da ya koka tun karfinsa ko zai samu sauki,
Goshinsa ya dafe yana dubansa, ya ce" ka daina damuwa da lafiata Wardugu,
Wardugu ya katse shi da fadin" idan muka gwada aikin nan fa?
Mu.azam ya ce" bayan ka tirsasa ni shan lemun tsami cikin ruwa masu zafi, kana tirsasani cin tafarnuwa, kuma zaka bijiro da maganar aikin da na guduwa ? Wardugu aikin nan fa mai yiwuwa shigar da za.a yi da ni a fitar maku da gawata,
Wardugu ya ce" kuma tana iya yiwuwa a fitar mana da kai ras ka sami lafia,
Mu.azam ya ce" mafi akasari idan Allah ya yi an sami lafiar ma kwakwaluwa na tabuwa, ko a samu shafewar tunani, cikin kaso dari bai fi 2/100 suke mikewa garas ba Wardugu, na fi son idan ta Allahn ce zata kasance da ni nan kusa ya kasance ina kusa da mutanen da nake so suke so na,
Wardugu ya kura masa ido, kallon cikin ido, ya ce" ba zan iya ba, zuciyata mai mugun rauni ce a kanka, ina jin rashin karfi a abinda ya shafe ka, baka yi min adalci ba idan har ka yi min haka, !
Ya mike ya dauki kys dinsa, ya dora hanayensa saman table din yana dubansa ya ce" baka isa ka min haka ba, ba zan taba barinka ka yi min haka ba! Zan nemi karin bayani ......
Juyawa ya yi ya fice inda yake jin kansa na mugun sara masa,
Mu.azam ya girgiza kansa bayan ya bi shi da kallo, a hankali ya furta" ban so ka ji ba, sai dai rigumarka ta saka ka tankalo abinda zai hana maka nutsuwa!, ya hana maka jin dadi!
Tukin garari ya yi wanda ikon Allah kawai ya kai shi gidansa lafia,
Yana zuwa ya sauka daga motar ya rufe ya nufi bangarensa kansa duke yana mai jin yanda yake sara masa,
Har zai bude ya shiga, sai ya fasa ya dubi bangaren Walyn,
A hankali ya juya akalar tafiar tasa ya nufi bangarenta yana wata irin tafia wace da ka gani zaka fahimci da karfi ne ake yinta ba dan ana jin dadinta ba,
Wardugu na shiga ya zarce falonta baba inda kamshin turaren da aka turara ya yi masa salama.
A hankali ya shige yana hangenta kwonce saman doguwar kujerar falon nata tana danna waya ranta da yannayin bace, sannan da maganin zazabi mai tafasa a gefe da alama dai ita ta sha bata jin jikinta,
Da sauri sauri ya karasa gareta yana mai cire rigar tasa ta sama ko zai ji dan sanyi sanyi ya karasa wajen Walyn da ta zabura ta mike tana dubansa da wani irin yannayi mai fasara abu uku, na farko ganninsa a bangarenta, na biyu yannayinsa ya firgitata, na uku mugun haushinsa da take ji domin yanzun ma a cikin grup dinsu na manyan mata ne ake tatauna maganar har wata na ikirarin ita walahi a duniya ba wanda ya yi mata irin wardugu halayensa na kasheta da dadi, idan ta kali hotonsa takan jita a wata duniya, tunani take wannan mutumen ya kasance hazarsa a gabanta kadai ya isheta, duda an kwabeta cewar da matarsa a gidan fa , kamar an zungureta ne an tirata domin a lokacin ne ma ta ce" Wardugu ai mijin mace hudu ne wanda Allah ya halita masa ba wani shege ba, duniya kuwa idan takamarka sauko wani a can ya kwana,
Tana wannan tunanin wardugu ya karaso jikinta, batai tunani ba ta ji ya rungumeta da karfi wanda sai da ta ji kamar numfashinta zai tsaya dan ya kanainayeta ya hana ta motsi,