← Book details Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 110

Sashe 110

Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 3 min read

Wajen karfe biyu ake walima, dan haka du aka taru ana gabatarwa,
Nan Agaishat ta fito, cikin shirinta na doguwar rigar lesh mai ruwan golden,
Ta sha sarka da yan kunaye da awarwaraye sa agogo da abin hancinta kowane na zinare ,
Kwaliya yar daidai ce a fuskarta wace ta kara fitar da tsararen kuma nitsatsen kwaliyarta wace sai da Wardugu ya duba da kansa cewar babu kowa sannan ya yarda da ta fita a haka domin kuwa ta jima da aka yi mata tana son fita sai jaje yake wai ta yi kyau sai binta yake da kallo,

Ba kwaliyarta ta girgiza walyn ba, domin kwaliyarta nitsatsiya ce duda tsadar leshen da kuma su sarkar, ta san wardugu ne ya siya mata dan haka bata wani damu ba saima hura hanci da ta ringa yi ta biya marokiya na yi mata kirarin uwar gida,

A lokacin da aka fara rabon kyauta wa du wanda ya zo , a lokacin ta haukace da mamaki, kyautar daga kakar Agaishat, bata ifasa sarewa ba sai da ta ga wacece kakar ta agaishat, Matar GUKUNNI? ita ta haifi mahaifiyar Agaishat,
Ambulop ce ake baiwa mutane dauke da kudi, sai ka buda ka ga adadin abi da aka baka, nan da nan wajen ya kara rikicewa da murna da shewa, kamar da wasa aka fasa zuzuta walyn din , kudi ya karbe hasken nata, nan da nan maroka sai suka gane bikin wanda suka zo suka juyar da akalar wasawar zuwa ga amarya shalele,

Basu kara sarewa ba sai da garar amarya ta shigo, wace iyayenta sukaiwa ango,
Ba wai wani abinda ba.a taba gani bane aa, abin ne ba.a yi zaton za.a yi shi haka daga wajen amaryar ba, inda Ayya ta zagime itama ta bada kyauta wa yaron da ya ci sunna *ABDALLAH* Bawon Allah, da kuma mahaifiyarsa,
Haka aka gabatar da kyautar da Wardugu ya dankara mata, aman bai yiwa yaronsa kyautar komai ba, ya dai yi dogon rubutu na saka albarka,
Kai bude bude ne ya cike gidan, inda ba wanda ya san fitar Walyn sai kofa...

Bayan wata bakwai.....

Rarafowa ya yi ya karaso kusan kafarsa,
Ya kama kafar ya mike ya rike kafar da kyau sannan ya washkale da dariya yana duban Wardugu dake zaune yana kada kafa ya gama tashin hankalin ba zata je wajen sunnan matar Mu.azam ba, ita kuwa tace a na me? Ba.a zumunci su ke kai kawo hanya?
Ai kuwa ya hayayako yana fadin" Orronur ni ne sai me? Ni ne sai me? Bara na gwada maki sai me!
Da gudu ta afka dakinta ta dani kofar tana kilkila dariya ta kuga ta ce" Wardugu bana son duka

Shi kuwa daga zaunan da yake ya saki murmushi ya dauki yaronsa dake ta bangalar masa dariya ji yake wasa ne ake masa ya rungume a jikinsa kafin ya ce" ORRONUR, BA DAI NI NE WARDUGUN BA KO? KUMA NI NE SAI AN JE DIN KO? BA ZAN DAKE KI BA, AMAN WALAHI CIKI ZAN JARA MAKI!

IDO ta zaro kafin ta shiga kiciniyar bude kofarta dan zuwa ta baiwa mijinta, amininta, yayanta, ubanta, masoyinta, abokin wasanta hakuri ta rarashi abinta cikin hikima....

Tamat bi hamdika👏🏻👏🏻👏🏻
Chapter 110 · 0% Book details