← Book details Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 110

Sashe 83

Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read

🐫🐫🐫 *BAK'A CE*

https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp

*☀IDAN RANA TA FITO WRITER'S ASSO🌤* ____________________________________________

*Fad'akar da al'umma tare da nishad'antar da masoya shine fatanmu*😘🤝🏻😘

7️⃣0️⃣

Barkan mu da sallah jama.a,

*KUTKALE*

*Aure yakin mata ne*

*Kamarta bata da niyar cutarwa*

Kar ku bari a baku labari.....

Mikewa ta yi tsaye, nan doguwar rigar da ta saka wace ta bi jikinta ta sauka kasa ta kara ainahin fitar da surar jikinta da wani tsararen kyau mai fizga,

Lafayar ta dauko da niyar sakawa sai dai me, tana dubawa da kyau ta ga ai wannan ta ranar dinern da aka shirya ce,

Juyowa ta yi wajen Alhinayet dake zaune cikin shigar turkudi riga da zani sannan ta yaye kanta da shi ta fiti fit Buzuwarta ta ce" Alhi, dan Allah ki saka a kaini gida na dauko Lafayata, wannan ta gobe ce na dauko ashe,

Alhinayet ta ce " Ohk ki je wajen Salisu motar a hannunsa dan tun jiya colonel ya hana na kuma fita da ita ,

Agaishat ta amsa inda ta dauki Abayarta ja mai adon baki baki a jiki mai mabalai ta saka sannan ta yane kanta da mayafin abayar,
Kai Agaishat fa ta gama haduwa, dogon hancin nan nata ya zo har kusan bakinta mai dan girma kadan, gashin girarta kuwa ta caje shi ta daidaita shi ya yi tsaf da shi ya bada kala, tsarin fuskarta kyauta ce daga Allah, gashi kuma ya hadu da nutsuwar yannayi,

Cikin nutsuwa take takawa har ta samu fitowa inda ta hange shi domin an saka fitilu ko.ina,

Tana zuwa da muradinta ya mike ya tafi wajen motar suka shiga ya jata sai gidan Ayya, wato mahaifiyar ogansu,

Suna shiga gidan Agaishat ta ga motoci har shida,
Biyar din kalarsu daya, sannan ga sojoji tsatsaye du sun hade fuska tamkar an zage su,

Tsayar da ita aka yi sai da aka cajeta dan kuwa ogansu na ciki ko wa bai isa ya shiga kansa tsaye ba,

Ji ta yi kafafuwanta na rawa, dan ba alamar sasauci a fuskokin su, dan haka a hankali ta samu ta raba ta haye inda ta fura kofar falon ta shiga da salama murya a dan dage kadan dan mutanen dake ciki su ji ta,

Salamar ce ta katse, a daidai lokacin da idannuwanta sukai mata arba da su,
Da Farko dai Wardugu ne da kakin soja sai dai botiraan rigar a bale inda rigar shi ta ciki fara kar ta samu damar bayana kanta da pecto dinsa,
Kafarsa daya kan daya ya dora, yana danna waya aman salamarta ya saka shi dago kansa da sauri tare da bugawar zuciyar da ta saka shi lumshe dara daran idannuwansa,

Gefe kuwa mijinta ne, uhum ba mijinta ba, tsohon mijinta, wato Mu.azam, docter Mu.azam ne zaune sanye da costume bakake da cravate dinsa ya daure cif da shi, duda kansa a aske kwal aman bai hanna bayanar kyansa ba,

Sai Ayya dake zaune cikin lafayarta , daga kasa kuwa Khadija ce ta duka da alama neman gafara take,

Idannuwanta ta lumshe, ta kara,lumshewa, dukan wata jarumta da take tunanin tana da ne take gayatowa , sai dai ina, gaba daya jikinta ne ya kwashi rawa wanda hakan ya yi sanadiyar sakin dankareriyar samsung dinta kasa inda ta bada Pats screen ya mutu🤦‍♀,
Dubanta ta kai wajen wayar , ta yi azamar dukawa dan dauka, sai dai gaba daya ta shiga raruma tana saki, ta kasa daukan!
Dan haka ta mike ta tsalaka wayar ta juya da gudu gudu ta shiga hawan bene dan neman dakinta tana kokarin dane wani katoton kuka dake taso mata da karfin tsiya,

Ayya ce ta mike da sauri, inda ta ga gilmawarsa kawai, da karfinsa yake taka matatakalar yana nufar inda take inda idannuwansa suka rufe hankalinsa ya tashi,

Ayya ta ce" Wardugu,

Ina baya jinta, shima adu.a yake, fata yake na Allah ya sa ba kukan abinda yake tunani take yi ba,

Dakinta ya tura ya shiga,

Idannuwansa kyam saman kanta inda ya ga ta cire abayar jikinta sauran doguwar rigar nan ta cire dan kwali ta yar , ta kifa kanta saman abin bed, kuka take har tana jijiga,

Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, shi ne abinda ya iya furtawa kafin yake karasawa inda take,

Hannayensa ya saka wajen kafadunta ya dagota tsaye gaba dayanta,

Kokarin bude jikakun idannuwanta take , sannan zufa ta jike gashinta daga gaba tamkar ta watsa ruwa, fuskar nata ta jike jagab tana hakin kuka,

Bai bari ta karasa bude idannuwan nata ba ya janyota gaba dayanta cikin ni.imtacen jikinsa, wani irin riko ya yi mata gaba dayanta tamkar sabon babyn da baya so a kwace masa,

Kamshinsa, da wani irin bugawar da zuciyarsa ke yi wada tana iya ji a irin rikon da ya yi mata, da kuma bakon lamarin wai ita Agaishat kwonce a kirjin Wardugu, namiji daya ya daya, Wardugu zaki, wardugu guguwa lahaula wala kuwata, wani juuu ta ji wata juwa na neman debarta ita dake kwonce luf a saman kirjinsa, kukan ta nema ta rasa, hasalima mantawa ta yi ta yanda ake rera wakar kukan, sai wani ajiyar zuciya da take zaukewa mai dumin gaske saman kirjinsa dake bude,

Hannunsa dake rawa ya dago a hankali ya dora saman gashin kanta dake malale saman gadon bayanta ya dora ya dan ja hannunsa kasa sannan ya maido sama,

Tsayar da hannun ya yi yana kokarin bude idannuwansa da ya rufe ruf,
Muryarsa na rawan da bai taba yi ba, hannunsa na rawa ya ce" menene? Mu.azam ne?

Shiru ta yi bata iya bashi amsa ba, hasalima kokowa take da numfashinta domin yana buda baki maganarsa na watso mata kanshin turaran baki da yake anfani da shi mai kanshin banana

A hankali ya dora hancinsa saman goshinta, hakan ya baiwa bakinsa damar zuwa wajen jikakun idannuwanta,
Ji ta yi ya damki hannunta na dama da dan karfi kadan, sannan ya ce" *Son shi ki ke yi ko?*, *KUKAN SON TSOHON MIJINKI KI KE?*

masha Allah, Alhamdulilah, barkan mu da sallah yan uwa. ALLAH ya karba mana .....Amen

*TALLAH TALLAH TALLAH*,

*KUTKALE*

*PRISON KUTKALE*

Kwonce take inda aka gama jibgarta dan ta yiwa Eliz gardama, wani bacin wahala me ya kwasheta inda kamar daga sama ta ji ana lalubarta,,
Hannu ne, kokarin kai hannun ake cikin dadaudan sqet dinta wanda ko karamin wando babu a ciki, wato dai malan shigo...........

Domin karin bayani ka tumtubi +22791466605

Labaru masu zuwa in sha Allah

*AURE....YAKIN MATA NE*

*KAMARTA BATA DA NIYAR CUTARWA*

DAGA ALKALAMIN *SAJIDA* YAR MUTAN NIGER MARUBUCIYAR

*DUK KARYAR KADA*,

*YAR MAHAUKACIYA*

*DAGA TAFIA DAUKAR SOJA*

*BANI DA ZABI*

*NEMAN NA KAINA*

*BAK'A......*

Fan's barka da sallahna🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔😢😢🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔😢🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔😢🤔😢😢😢😢😢😢😢😢

🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫

https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp

*☀IDAN RANA TA FITO WRITER'S ASSO🌤* ____________________________________________

*Fad'akar da al'umma tare da nishad'antar da masoya shine fatanmu*😘🤝🏻😘

Na
*SAJIDA*

6️⃣8️⃣

Asalamu alaikum
*Allah ya kawo mu wata mai albarka, banban wata mai tare da lada ,wata mai cinye zunubi, RAMADAN, ALLAH KA KARAWA ANNABI DARAJA TARE DA WASILA DA FARILLAH A ALJANAR FIRDAUS Allah ka jikan magabatan mu, ka sa sun huta, idan tamu ta zo ka sa mu cika da imani ka sa mu tarda alkhairi 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻 Ya Allah, muna rokon ka, ka shirye mu, ka inta mu, ya ubangiji ka yafe mana zunubanmu, Allah ka hane mu saba maka,Ya Allah ka dora mu a hanyar bautarka, ka karbi ibadunmu, Ya Allah ka sa mu bayansa lafia ka maimaita mana, ni sajida ina mai yi mana fatan Alkhairi da fatan Allah ya kai.mu rai da lafia bayan sallah*

Algabitt ya dago da dubansa ya sauke kan Gaishata dake wani irin numfarfashi gabanta na faduwa tana duban mahaifin nata,

Algabitt ya kauda kansa yana bin mutanen dake zaune daya bayan daya da ido,
Kansa ya girgiza kafin ya kai dubansa wajen sarki ya ya buda bakinsa zai yi magana sarki ya mike tsaye ya ce" ya isa, kar ka fadi komai,

Muryar uwar gidansa ne ta ce " sarkina, talakawa na zaune suna jiran hukunci,

Amaryarsa ce ta gyara zama ta saki murmushi ta ce" sarkina, muna masu neman alfarmar a yi hukunci yanda aka saba yiwa sauran talakawa,

Gaishata dake bin su da kallo su duka biyu ta maido dubanta wajen Sarki da ya tsurawa matan nasa ido cike da takaici,

Gaishata ta share hawayenta ta sada kanta kasa,

Sarki ya koma ya zauna yana duban dogarai dake muzurai , sun so su tsawatarwa da matan sarki sai dai gannin matan sarkin ne tsoro ya hana su su yi masu magana domin ba wanda yake da hurumin yin magana idan sarki da kansa na shari.a duda kauye ne, idan baya nan akoy mai wakiltarsa ,

Hade rai ya yi ya ce" du wanda ya kara buda baki ya yi magana a wajen nan zai karbi hukunci komai kusancinsa da Sarki!

Idan Dogarai suka ga abin tsawatarwa basu tsawatarba zasu fuskanci fuahina!

Ji kake suna fadin" tuba muke sarkin talakawa,

Sarki ya maida hankalinsa wajen Algabittt ya ce" tabas ka kasance mutun mai son kansa, ka yi rayuwa bisa umarnin zuciyarka, tabas munada muradin jin bukatar wace aka fi cuta duda ta bada amanar yarta ta wakilce ta, dan haka zamu iya sauraron zuwanta ko maganarta a waya,

Magana yake hankalinsa ba a kwonce ba domin tunda Gaishata ta sada kanta bata dago ba,

Mikewa ya yi ya danna kira kan number Gukunni ,
Bayani ya kora masa na komai cikin nutsuwa , yana gamawa Gukunni ya tarda matarsa da y'arsa, cikin hikima ta manya ya zayane masu komai wanda ya saka Anna fashewa da wani irin kuka har tana dukewa tana dafe cikinta da dukan hannayenta,
Chapter 83 · 0% Book details