← Book details Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 110

Sashe 58

Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read

A kofar asibitin aka hana shi shiga, domin dare ya ratsa har wajen karfe biyun dare,
Ba yanda bai yi ba, da kwatance da komai aman masu tsaron kofar suka kiya dan su basu sanshi ba, gashi mushulmi, su kam aa yama bar masu kofar asibiti
Gashi bai san numbersa na garin ba,

Waje ya samu dan nesa da asibitin ya shiga kai kawo, dare ne ba damar ya sayi wata wayar du an rufe, gashi ba wata takarda ya zo da ita ba ko tiket ciran kudi muraran ya yi masa sun san shi a yanda yake da yawo kasashe ya shige abinsa idan ya so ya san yanda zai yi,

Kansa ya shafa a lokacin da ya tuno da whatsupp, duda ya san abune mai wuya wai ya duba whatsupp , aman sai ya shiga ya aniya kiran number Wardugu baya dagawa,
Ya yi masa kira ya fi a kirga, dan haka ya nemi guri ya zauna hankali kwonce dan waje ne mai tsaro, kuma da garaje ba za.a kama mutun ba duda suna da tsarguwa da musulmi suna tsoron yan jihad,

Daga nesa yake hangen tafiyarsa, da kyar yake daga kafarsa,
Ido ya tsura masa, daga ina yake?
Wani tausayinsa ne ya lulube shi, dan kuwa Wardugu in dai hankalinsa a tashe toh baya zama, zai yi ta yawo ne a kafa, idan wani abin fada ne ya hada shi da wani toh a hanyar yawon nan nasa kan mai tsautsayi zai kare ne,
Aman yanzu yana hangensa a wani yannayi na rashin karfi, har ya karaso inda yake zaune,

Dama Wardugu na hangensa, tun zuwansa har artabun da suka sha da masu tsaron asibitin da kiran da ya yi ta faman yi,

Yana zuwa tsaye ya yi gabansa yana dubansa,

A nitse ya mike shima yana dubansa,
Hannu ya mika masa da nufin su yi musabaha,
Wardugu ya miko masa nasa hannun shima, nan ya ji wani irin zafi hannun nasa,
Hankali tashe ya ce" aman Wardugu me kake yi haka? Yau ka fara yin rashi ne ko yau ka fara shiga tashin hankali mai tsanani? Ka tina wannan lamari gaban wanda baka da ikon motsi, jan numfashi sai ya umarta ne, kaima lokacinka na nan tafe, dan kulu nafsin za.ikatul maut,
Ba wanda ya isa, ba wanda zai iya, ba wanda zai yi in ba shi ba, kar ka manta ya rasa iyayensa a lokacin da yake saurayi, ya karba da hannu bibiyu ya rayu a cikin duniyarnan mai cike da rudani,
Idan Allah ya karbe mana shi a yau sai mu yi masa biyaya , mutuwa ta zama rigar kowa, mutuwa mai yankan kauna ne, mutuwa ba ruwanta da baba ko yaro, itace mai dauke uwa a lokacin da ta sako dan jariri, itace mai dauke jariri daga hannun mahaifiyarsa ta mika shi a kaishi wajen wanda ya fita son sa, mutuwa mai raba miji da mata, ta raba abokai, ita ba inda bata ratsawa da lokaci ya yi ya dauka ta yi gaba abinta, a halin arziki ko talauci, birni ko kauye,
Ka yiwa amininka gata mafi girma wato adu.a da kyakyawan sutura,

Wardugu ya zube kasa nan wajen kasa zaune,
Bakinsa na rawa dan ciro magana , da kyar ya iya samu bakin ya bude masa ya ce" ya ya ya bar wasiyun da sukai min tsauri da yawa, *MARAHUT* na tsinci kaina a halin da bana iya aiwatar da komai, karfin ikon Allah dole na karba, na kasa kuka, na kasa saka hannun, ana min ikirarin ni jarumi ne? Na gwada jarumta ta hanyar sadaukar masa da abinda nake so a nan gidan duniya aman yau an wayi gari na kasa daukan jarumtar saka hannu a bakar takardar da za.a cire masa abin numfashi,

Marahut ya zauna shima kusa da shi ya daga kansa sama ya ce" kalu *INNALILAHI WA INA ILAIHI RAJ.UNE*, innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, innalilahi wa.ina ilaihi raj.une.......
Haka Murahut ya yi ta maimaita masa har shima ya karba sukai ta yi , sukai ta yi , sukai ta yi,

Can Wardugu ya shiga ajiye zuciya, a hankali ya dora kansa saman kafadar Murahuttt,

Murahutt ya yi shiru na dan Lokaci kafin ya ce" ka san cirewar ko shi ne samun rahama a gare shi? Idan ka yi duba da musulunci ya zo mana da idan mutun ya rasu a yi gagawar yi masa sutura?
Shin wace hikima ce a boye a nan? Allah baya abu kawai,
Idanfa an jima da zare ransa kune ke gannin yana numfashi? Idanda gawar ce kwonce kuke kallo?

Wardugu ya rintse idannuwansa da karfi ya ce" mai yiwuwa kuma likacin ya buda idannuwan nasa ne basu yi ba?

Kennan dai ba zaka hakura ba ? Marahut ya tambaye shi,

Wardugu ya ce" bani da karfi, ban isa na ja ba,

Marahut ya gyada kai, sukai shiru su duka

Can Marahut ya ce" ina Agaishat?

Wardugu ya dago da sauri ya dubi Marahut, shi sai yanzu suka fado masa a ransa, mikewa ya yi zurbat ya yi gaba da sauri inda Marahut ya bishi da kallo, bai yi wani gigin binsa ba dan tuni ya yi nisa a tafiar sai ido da ya zuba masa har aka barshi ya shiga asibitin,

Yana shiga ya zarce wajen da ya tabata suna nan wato wajen dakin Mu.azam,
Bayin Allah sun dunkule waje guda sun rufa da hijabin Agaishat sai sauke ajiyar zuciya suke su duka,

Tausayinsu ya kara karyar masa da zuciya, tun ranar da Khadija ta je gidansa ya gama gane ba wai kawance ne kawai ya hada su da Mu.azam ba, duda ya ga irin yanda Agaishatma ke son Mu.azam din, aman yayi imanin da wuya in ta kai khadijar dan kuwa Khadija ta jima a soyayarsa, wa.innan bayin Allahn biyu su ne marayu kan rasuwar Mu.azam, shi kuwa ya rasa amini, aboki, dan uwan shawara, dan uwa na jini

A hankali ya raba su ya nufi wajen hangen Mu.azam din,

Ja ya yi ya tsaya ya tsura masa ido, irin kallon nan na kurullah,

Idannuwansa ya lumshe yana kada kai, dan kuwa idonsa nuna masa yake ya motsa yatsarsa manuniya,

Da yake kafafuwansa rufe suke da bargo ba.a gannin motsinsu, sai da ya kara motsa yatsar nan, a hankali fatar idonsa ta dan fara rawa, bugawar zuciyarsa ya fara karuwa kan na da da ya yi kasa sosai ya yi nisa,
A hankali bugawar zuciyar ke dan karuwa wanda ya saka injin dake sasarkafe jikinsa suka kwashi kuka,

Zabura Wardugu ya yi ya kara kurawa Mu.azam ido,

Tun karfinsa ya ce" MU.AZAM, MU.AZAM, MU.AZAM!

Ba.a jin komai daga ciki, sai su Agaishat ne suka mike a firgice, daidai nan likita ya shigo da gudu ana biye da shi ana taya shi daura rigar aikinsa da safar hannu da na rufe hanci,
Wata na tura abinda ke dauke da kayan aiki,
Ai kuwa sai gasu suna ta bilowa da gudu gudu , nanfa aka shiga kokowar fitar da su Wardugu daga nan din ma ,
Da kyar aka fitar da su waje inda du suka haukace sai tambaya suke jefo masa wai ya farka ne ? Farkawa ya yi ne?

Wardugu kam bai iya amsawa ba sai kai kawo yake yana kama sunnayen Allah a zuciyarsa , baya so ya amsa masu dan bazai so ya basu espoir kuma abin ya kasance ba haka ba,

A kadan sun dauki minti arba.in, lokaci lokaci zaka ga wani ya fito da gudu ya nufi can wajen dakin kayan aiki ya dawo da wani abin da gudu ya shige, koda sun tarye shi baya bada amsa har suka hakura suka dawo bin mutane da kallo. ( ya Allah ka jikan mama da gafara, wannan ciwo da ya kaita Allah ka sa bakin wahalarta kennan alfarmar annabi muhamadu sallalahu alaihi wa salam)

Ba su su gama kimtsa komai ba sai da aka dauki wajen awa da minti talatin kafin kake gannin sun fara fitowa suna tafia makwoncinsu,

Su kam sun zama tamkar mararsa wayo,
Can sai ga docter Rogger da Elizabeth sun fito,
Murmushi kwonce saman fuskarsu,

Hannu suka shiga mikawa su Wardugu, harda Agaishat dake binsu da kallo aman ta kasa karbar hannun ko daya dan ta kagauta ta ji halin da yake ciki

Wani murmushi ne Wardugu ya saki, wanda gaba daya hakoransa suka bayana,
Da sauri ya juya ya nufi bayi dan dauro alwallah, domin lokacin nafilfilu bai shige ba, tabas zai raya wannan dare wajen godewa Allah,

Khadija ta rungume Agaishat tana murna ga hawaye na malala a idannuwanta ta ce " Agaishat, ya farka, kuma ya yi kyakyawan farkawa, dan ya gane su su duka, yanzu an ce a barshi ya huta zuwa safe mu shiga mu ganshi, Agaishat *Mu.azam dinmu ya farka*

Agaishat ta saki murmushi itama ta ce" Alhamdulilah, Allah mun gode maka, Allah ka bashi lafia mai anfani

Da amen take amsawa,
A haka Wardugu ya fito da tapis a hannunsa ya saci kallonsu kadan ya sauke ajiyar zuciya ya fice a asibitin,

Inda ya barshi nan ya same shi,
Goron ruwa ya mika masa bai masa magana ba ya samu waje ya shinfida dardumar ya tayar da sallah,

A sujadarsa ta karshe, Wardugu ya jima yanaiwa Allah kirari, ya gode masa bila adadin,
Bai tashi daga saman salayarsa ba sai da rana ta fara fitowa, dadaykun mutanen da suke fitowa motsa jiki na safe har sun fara tsayawa daga nesa suna kallon su Wardugu suna mamakin musulmai ne suna masu sallah a wuri,

Bai wani damu ba sai da ya gama jan carbinsa ya shafa fatiyarsa , ya kai dubansa wajen Mahaifinsa,
Fuska ya hade ya yi kicin kicin da fuska ya ce" ya farka a jiya,

Marahutt ya ce" na gane tun jiyan a yannayinka,

Wardugu ya dan tabe baki ya mike ya dauke abin salayar ya kai dubansa wajen asibitin ya ga an bude an fara shiga, dubansa ya kai wajen Marahutt ,
Kafin ya yi magana Marahut ya ce" na san hanya

Kansa ya juyar ya ajiye salayar nan kusa da mahaifin nasa ya juya yana neman taxi dan ba zai koma ciki daukan mota ba gaskiya.
Chapter 58 · 0% Book details