← Book details Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 110

Sashe 39

Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read

Aisata ta ci gaba" mijin ki dan ra.ayi ne, gwarzona ya bani wahalar da wani namijin bai bani ba , kyauna, zubina, yannayin rayuwana na saka shi fadin"Aisata ke matar kilacewa ce, ki yi zamanki a gida zan zo na dauke ki na mayar da ke matata. kafin na samu kansa na jigata.da kuka da komai ya furtan kalmar so, domin na kai karar tsohon saurayina wajensa inda na biya mutumin ya yi min dukan tsiya, ke dai na takaita maki sai da na zama tamkar kaska, du inda wardugu yake ina nan, da naci da taimakon aminiyarsa ya furtan kalmar so...
Sai dai abin haushi du irin yanda muke soyaya da shi idan na nuna koda shan minti ne a dan zaga sai ya fatatake ni,
A ranar da na tube zindir a gabansa sosai na kusa cin masa wani tsinanan abokinsa ya shigo dakin domin ke shaidan ba abinda baya hasawa , kwana dakin wardugu na kusan cinma burina nan na fahinci irin zaman da ake tsakanin matar Marahut da shi,

Ayya ta kasance mace mai tsafta, ta iya girki, tana yiwa mijinta biyaya ....sai dai na sha na fito tsakiyar dare falon su na kunnuwana su tsinkayo min rigimar ba zata bashi ba, ta gaji da ayyuka ya bari sai da safe!

Wani wal wal wal ta yi da idannuwanta ta ce" *Walyn ba.a matsa lamarin nan, idan aka tashi a yi kawai!*,

A lokacin da na gama gane Ayya ba zata aminta na auri farin cikina ba, na dauki damarar itama sai na cusa mata bakin ciki , kuma ko da kwaya sai na kwonta da d'anta!

Walyn ta ce" shi Marahut din asiri ki kai masa ko?

Aisata ta ce" na fada maki ban san wannan ba!

Walyn ta rafka tagumi ta ce" fada mani yanda kika tarwatsa su , mai yiwuwa na yarda da labarin wai Wardugu ba asiri ki kai masa ba.

Aisata ta buda bakinta zata fada mata kennan aka zo aka ce ya isa haka sun jima suna hira domin dai Aisata harkar kwaya ya kaita kaso, ido a kanta yake dan kar a kawo mata har gidan kaso...

Haka Walyn na ji na gani ta fito ta kama hanyar gidanta ba tare da ta samu komai ba!

Alhinayet ce zaune tare da saurayinta, malamin university ne, saurayi ne domin bai taba aure ba, bazabarme ne baki dogo , hira suke cikin nishadi nan yake shaida mata yana son turowa,

Alhinayet ta fada masa zata fadawa abanta tukunnan , abinda ya ce in sha Allah.

Haka suka gama hirar su ya mike ya yi mata salama ya shige motarsa ya tafi,

Mikewa ta yi ta je cikin gidansu ,
Shiryawa ta yi ta saka dogon hijab dinta blue, ta dauki bakar leda ta je wajen mamansu , wato matar mahaifin su ta shaida mata zata je ta kaiwa Agaishat hijaban

Adu.a ta yi mata kafin take fita ta shiga motarta ta tayar ta nufi gidan Ayya.............

Aghali ya zo garin Niamey ne dan duba gininsu da ake yi a unguwar cité laraba,
Ya gama abinda ya kawo shi aman ya ki tafia bisa bukatarsa na Wardugu ya siyar masa da mota , sun tsayar zai shigo ranar lahadi wato gobe baya aiki sai su fita su je ya gani......

Soyaya suke a nitse, a hankali yake koya mata mecece soyayar ma wace a kulun sai sun gama bitar zai jefo mata tambayar" Agaishana, shin kina jin du abubuwan da na zana maki a kaina?

Dariya take yi a fili sai tace" ni yaya Mu.azam gudun fankan dakin Hane mai aiki kawai ke saka zuciyata gudu, ka ci gaba da koya mani na san zata yi gudun wata rana idan na ganka

Yakan tsareta da ido ne kawai , bai san me zai da ita ba, soyaya ai shigar farat daya take yi, shi da yake so ya kai kudirinsa wajen Ayya kan a aura masa ita da wuri? Kai ba zai wani jira har ta kamu da sonsa ba, zata so shi a zaman da zasu yi, shi kam yana kwadayin zama da ita a rayuwa....

Docter Mariam ce tsaye tare da shugabansu ta asibiti, kanta duke kuka ne take har jikinta na bari ta ce" nima marainiya ce docter, a lokacin da na zo wajen nan shi ya tarbe ni, ya ciyar da ni da aljihunsa, kafin na tsaya da kafafuwana shi ne komaina, tun a lokacin nake mugun son sa, ba zan yafewa kaina idan ban je na dawo da shi ba, ki taimaka mani ki sama mani takardar nan na roke ki,

Cike da tausayi take dubanta, su musulmai haka suke ko kuwa wasu da wasu ne? Tana jinjina girman son da Mariama ke yiwa docter mu.azam, in sha Allah zata sama mata takardar su biyu wace zata bata damar zuwa ta zo da shi su shiga aiki, koda bai tashi ba , ba zata tsangwami kanta ba,

A hankali ta dafa kanta ta ce" kar ki damu Docter, ki je zan neme ki, zan nema maki takardar

Da murnarta ta yi godiya ta fito ta shiga office dinta, hotonsu ta kaiwa duba kafin a fili ta ce" wai baka son farar mace ko? Dole ka so ni docter, ni ina son ka😭😭😭

Wayo hanuna😕😕😕😕😕😕

🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫

Na *SAJIDA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

4️⃣1️⃣

Ayya ki duba lamarina na roke ki,
Mu.azan ya fada kansa a kasa, kunya ta hana shi dago da kansa ya dubi Ayya domin ya fadi abu mafi nauyi a bakinsa

Da mamaki take kallonsa, so? Aure? Yana son Auren Agaishat? Aman yaushe suka yi wata soyaya da fahimta har za.a kai ga aure?

A nitse ta ce" Mu.azam, aman me ya sa kake sauri haka?

Mu.azam dake kallin kasa ya ce" Ayya , ina so ne a yi mu juya tare da ita.

Aman ai ka san sha.anin aure na bukatar nutsuwa ko? Sannan yarinyar nan amana na daukota daga garin su, eh lale mahaifiyarta ta bani damar ko aure ya tashi na yi mata aman da ransu da lafiarsu ba zan yanke hukunci irin na aure ba tare da yawun iyayen yarinyar ba ko? .... Ayya ta fada jikinta sanyaye tana dubansa

Mu.azam ya gyada kansa, hankalinsa ya dan fara tashi ya ce" Ayya, ki tura ni wajen dagin nata, na je na nemi a bani aurenta, bana son jan abin ne

Ayya ta kuma kale shi da mamaki, bai taba naci kan abu irin wannan ba, jikinta ta ji ya kara yin sanyi, aman Agaishat dinta dukanta ma nawa take da har za.a yi gagawa a lamarinta haka? Sai dai kuma bata tunanin Mu.azam zai wulakanta mata yarinya, duda haka tana son bin hanyar da kakarta ta bi da ita, zasu kai kulansu wajen Allah, a hankali ta ce" yarona, na ji, kuma zan fi kowa farin cikin sannin tana hannu mai kyau, kar ka damu zan san abin yi nan kusa in sha Allah, in dai Agaishat matarka ce zaka aureta kisa ba da jimawa ba.

Cike da murna ya yi mata godiya ya mike ya nufi dakinsa dan yin wanka,

Tsaye take a tsakiyar gidan tana kallon manyan tantabarun gidan dake kiwo nan balbalin gidan , tana yi tana duba kofa domin ranar juma.a da alhinayet ta zo tace zata dawo ranar lahadi su je gidan kitso Ayya sai fadan kitso take,

Kallonta yake daga inda yake tsaye, inda ya shiga takowa a hankali har ya karaso inda take tsaye, ma.ana suka jera,

A hankali ta dago da kanta daga kallon tantabarar ta kai dubanta wajensa , nan da nan ta matsa gaba sannan ta sada kanta kasa cikin yanayi na bawa wanda ke kusa girma.

Aghali ya ce" a garinku ke yar gidan waye?

Agaishat ta dube shi, ta kuma sada kanta, sarkinta ne, ita talakarsa ce, sarkinta ma talakansa ne, dan haka cikin yannayi na girmamawa ta ce" sunnan mahaifina *Ba*,

Ba , ai sunnan du uba ne a garin buzaye! Aghali ya fada yana kara tsareta da ido,

Agaishat ta ce" ka yi hakuri,

Aghali ya ce" baki min laifi ba,
Soyaya kike da shi? Kina tunanin zai mutunta ki zai so ki da zuciya daya?

Kallonta ta dago wannan karon ta sauke kan nasa,,

Bata kai ga bashi amsa ba Wardugu ya shigo da wata galeliyar mota fara kar, kusa da shi Alhinayet ce da ya dauko zai ajiye su wajen kitso wai🤦‍♀,

Birki ya ja irin na ka taka baka shiryan nan ba, da bakin gilas dinsa ya dan kale su kafin yake taka motar ya karasa wajen da ya dace a ajiye motar.

Yana tsayawa ya kai dubansa wajensu, gani ya yi aghali na magana, yar gidan Ayya kuwa na kallon kasa, kansa ya girgiza kafin ya maida dubansa wajen Alhinayett ya ce" Alhi, Aba ya saka na yi bincike a kansa, yace bai yarda da adinninsa ba , hakan ne kuwa ba musulmi bane yace shi musulmi ne dan ya saje da jama.ar garin nan,

Alhinayett ta ce" General ya kuke so na yi ne? Ina zan shiga na samo wanda ya yi 100/100? Wannan na uku kennan yana zuwa da niyar aure abin na watsewa tun kafin a je ko.ina, Wardugu bana son auren Lieutenan na fada maka bana son auren soja.

Wardugu ya yi musrmushi yana dubanta ya ce" kuma ki ce ke aminiyata ce, a gabana kina fadin bakya son auren mai sana.ata, me zamu yi maki ne? Me muke yi?

Alhinayet ta girgiza kanta ta ce" Wardugu, bana iya zama da namiji mai mugun karfi, ba zan iya rigimar sojoji ba, ba zan iya firirita irin ta matan sojoji ba, ka san ko ni wacece ban iya fada ba, ban iya ihu ba Wardugu ina son namiji mai sanyin hali ne,
Chapter 39 · 0% Book details