← Book details Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 110

Sashe 104

Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read

Walyn ta kifta ido tana du dubansa ta ce" da ka yi aure kafin lokacin ka yin ya yi, da ka yi aure baka sanar mon ba kafin ka yi, da ka auri wannan yar yarinyar har ka juya min baya tsayin sati uku, da ka dauketa ka kaita gidanka na aeroport ni ka barni a nan ana ci min amana,

Wardugu ya sakar mata murmushi, ya kawar da kansa, can ya ce" adinina bai zo min da salon al.adata ba, dan na yi ban yi sabo ba,
Sannan da na yi ban sanar maki ba uwata ce ke? Nan ana daura aurena ban je na ga kowa ba sai ke, aman kika take ni!
Dubanta ya yi cikin ido ya ce" Agaishat kuwa, Wollah sonta nake!

Kyam ta yi tana dubansa,
Kanta ta kawar ta ce" ba zaka huce ba kennan?

Mikewa ya yi ya dauki ky dinsa ya juya da niyar tafiarsa,

Da sauri ta mike ta ce" Wardugu tafia zaka yi?

Juyowa ya yo yana dubanta kafin ya tako zuwa inda take tsaye ya dubeta da kyau ya ce" ban tsara saki wa mace ba, da na jima da rabuwa da ke bisa rashin hankalin da kike tafka min na yau da kulun Walyn,
Ban waiwaye ki yau ba dan isarki, kyanki, ko farin ki kamar yanda kike takama sai dan tsoron Allah da tunanin ko kin nutsu ne ?
Baki nutsu ba, har yanzu baki sauka daga inda kika hau ba,
Allah kawai nake tsoro, ina jin tsoron haduwata da shi da laifin wani a kaina, idan kika cire wannan, ki je du abinda zaki yi ki yi!
Yana gama fadar haka ya juya ya fice tana kugin kiran sunnansa ya yi mata banza,
Tsaki ta ja kafin ta wurgawa hanyar da ya bi harara ta yi kwafa ta ce" in dai rawar kan amarci ne, zaka yi ka kare, ba wani ka waiwaye ni dan wani abin face kana so na, ba zaka iya ba sai da ni! Wannan bakar ba zata girgiza ni ba!

Barci Agaishat take saman kujera a takure, da alama tsoro take ita daya,
Haka ya shigo dakin ya kai dubansa inda take,
Bai tasheta ba, bai yi mata magana ba ya fice ciki ya duba wajen abinci ya ga bata ci ba,
Bai tasheta ba ya fito ya nufi bangarensa ya kwonta domin ransa a bace yake, indai zai tasheta ne dalilin bata ci abinci ta kwonta ba yana iya bata mata rai,

Kamar yanda ta saba kiraye kirayen sallah suka farkar da ita, da kyar ta iya mikewa domin kwoncib da ta yi du jikinta ya yi tsami,
Dakinta ta zarce ta je ta kimtsa dan yin sallah,
Koda ta gama sallah zama ta yi ta tsurawa waje guda ido, zuciyarta ke mata fada, ba na komai ba sai na ta yi sabko, ya zata damu haka da son ganninsa bayan ta san ba ita daya gareshi ba?
Ita fa zuwa ta yi ta tarar da wata, idan ta tsiri damuwa da jinsa a kusa bata so kanta da yawa ba kuwa?

To aman ai sai ya min bankwana ko? Wayar da ya yi ita kawai ta shaidan inda zai je, daga shi bai ce min komai ba,

To meye dan wannan a halayan wardugu? Ke dai ki kiyaye,
Wata zuciyar ta bata amsa,
Dan haka a hankali ta mike ta ninke salayar, yau kam sai ta ga masu gyara gidan nan, a kulun kafin ta fito daga sallah an yi komai an gama, har kulun mamaki take, danma ita ke shiga kicin abinta, aman tana kyautata zaton da masu aiki a gidan, dan kuwa har yanzu tunda ta shigo bangaren nan nata kafarta bata fita ba, du sati Ayya ke turo mai kitso ta zo ko ta yi mata kitso ko ta mata gyaran kai, kunshin kafarta da hannayenta kuwa da sun fita ake dora wasu domin wannan lanlan ne na zamani mai saurin fita,

Labule ta dage ta leka sosai,
Ai kuwa sai shige da fice suke kowa da abubuwan aikinsa, hakan ya tabatar mata da har cikin ma da masu gyarawar kennan, ita dai abinda take yi da kanta saka turaran wuta, wanda take yin garwashin a kicin ta saka da toka mai zafi ta saka dan turaranta ya game dakunan da kamshi,

Murmushi ta yi ta je ta salo wankanta,

Tana gama shiryawa cikin doguwar atamparta an yi mata dinki simple, sai hannayen ne kawai akaiwa ado , ta daura dan kwalin atampar ta tsaya gaban madubi tana kallo,

A hankali ta sauke ajiyar zuciya a fili ta ce" Ba sofona, ina yawan mafarkinka, Allah ya sa lafiarka kalau ka ji? Zan so ka ganni Ba, tabas maganarka haka ne, birni ga girma ga abubuwan girma, birni mai dauke da wardugu da Ayya da kuma Walyn,
Birni mai mota mai jirgi,
Birni mai kalolin fata ba biyu kawai ba,

Sai da ta gama kalon kanta kafin ta yafa mayafi saman shigarta ta fito a hankali ta nufi wajen abin turaran wutarta ta dauka ta nufi kicin,
Sai da ta hada shayi ta zuba a dan cofi ta dauko biredi mai beurre sannan ta kuna garwashin ta hado turaran wutar ta fito da su a hannunta ta dorashi wajen da yake gana dakin sannan ta je saman cafet ta zauna ta yaye mayafin ta ajiye ta zauna ta fara karyawa,

Tana tsaka da ci ta ji kanshin turaransa hakan ya sa ta yi dan tsai kafin ta dago da dubanta,
Cikin shirin zuwa aiki yake, yannayin fuskarsa ba fara.a hakan ya sa ya shaida mata da ransa a bace yake,

A hankali ta kawar da dubanta daga fuskar tasa ta ajiye kofin glass dun dake hannunta ta mike daga zaman da ta yi tana goge hannunta da tissu duda ba abinda ya yi, ta kai dubanta wajensa,
Tsaye yake kikam yana dubanta,
A hankali ta mike ta karasa dan kusa da shi kadan kafin ta duka ta gaishe shi,

Mutanen kam a kusa suke yau, domin gaisuwarma da kai aka amsa mata, dan haka ta mike da niyar shiga kicin ta hado masa abin karyawa kafin ya fita,

Hannunta ya riko da hannunsa na dama ya dawo da ita gabansa,
Hannayenta ya kamo baki daya ya kai wajen botiran rigarsa dake bude ba.a bala ba,
A hankali ta shiga bala masa tana duban kasa ,
Sai da ta bala masa har daidai wanda yake tsayarwa sannan ya zauna saman kujera ,
Cikin nutsuwa ta juya ta shiga daki ta dauko kumb,
Dawowa ta yi ta caje masa sumar kansa da kyau ta juya ta mayar ta dawo da niyar shiga kicin din dai,

Rikota ya yi , ya juyo da ita suna kallon juna,
Kansa ya girgiza mata a hankali sannan ya mike ya dauki ky dinsa ya juyo ya mika mata wata dankareriyar samsung bai mata bayanin komai ba ya fice a gidan,

Ta jima tsaye cikin yannayin damuwa, me ke damunsa? Me ya bata masa rai haka?
A hankali ta zauna bakin kujera tana duban hanyar da ya bi ya fita,
Ya Allah, shi ne abinda ta fada a fili, azumi yake ko kuwa cin abincin ne ba zai yi ba? Yaushe ya shigo gidan ma ni ban ji ba?
Idannuwanta ta lumshe tana tuna maganar Ayya cewar wani lokacin zaka rasa gane kansa, zai dulmiyar da kai cikin tunanin waye shi? Dan haka ki yi ta hakuri Agaishat!

Wardugu, ka taimaka, ka bani hanyar da zan fahimce ka, ka taimaka ka ringa fara.a tare da ni ba sai ranar da ka yi niya ba, ka taimaka na zama wace ke gane du wani motsinka!

Wayar da ya ajiye mata ne ta shiga kuka ta hanyar salama da muryar mace zazaka tana karawa,
Sai da ta zabura dan ta zurfafa a tunani, kukan ya ankarar da ita dan haka da sauri ta dauko wayar tana duba sunnan wanda ke kiran, Anmou, waye Anmou????
Dagawa ta yi da salama sannan ta yi shiru,

Daga can kuwa sai da aka daga ta mika mata wayar tana dubanta da murmushi inda ita kuwa ta karba ta dan yi tsai , bata san da me zata fara ba, bata san me zata ce da ita ba, marabinta da ita tun kanta na cikin duhu,
Dan haka a hankali ta ce' Agaishat!

Tsai Agaishat ta yi, lokaci guda zuciyarta ta buga,
Wayar ta cire ta kali numbobin sannan ta mayar a kunnenta,
Muryar matar ta kara cewa " Agaishat, kina ji na kuwa? Da yaren buzanci, da irin yanda take rrrrrrrr dinta sak irin na Agaishat din,

Da sauri Agaishat ta kai zaune muryarta na rawa ta ce" Anna? ANNA ke ce?

Anna ta lumshe idannuwanta ta amsa da " Eh Agaishat,

Ai kuwa Agaishat ta fashe da kuka tana sauraron limfashin mahaifiyarta,
A hankali ta ce" Anna, ina kike? Kun dawo ne? Kin warke Anna? Anna ina yan uwana? Ayya ina Ba Sofona? Annata kin kama sunana sak Annata kin kama sunnana,

Anna ta lumshe idannuwanta tana mai jin nauyin yar da ta haifa da cikinta, tabas ta saki rayuwar Agaishat dandaja, Allah ne kawai ya zama gatanta, ita yanzu haka bata wani hadiye maganar wai dan amininsa na sonta ya saketa, ita fa tsoro take ko bai sameta daidai bane ya saketa? Sakin yaro karami na kutse kutse kofa kofa waje waje dan neman gurin da zai ji sanyin rayuwa , neman abinda zai saka a bakinsa, a haka har ta rago ta kawowa baba sofo da kuma Anna, a haka ta iya tatalin dan kudin da ta samu ta kawo masu, a haka take zuwa ta rabu tana tsoron wani abin ya faru ko mahaifinta ya zo ya karta mata abin wulakanci dan kawai kalar fatarta na da duhu? Tausayin yar ne ya saka Anna kasa yin magana, dan haka Mariama dake tsaye tana ta so a bata wayar ta yi dabara ta karbi wayar ta bushe da dariya ta ce" Agaishat, Agaishat din Ba Sofo, Agaishat an girma?

Kafin ta amsawa Mariama Fatimata ta sabce wayar ta tsere kusa da Gaishata ta ce" Agaishat, Agaishat din Ayya Agaishat kina ina, ina ne gidanki?
Chapter 104 · 0% Book details