← Book details Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 110

Sashe 54

Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read

Da kai ya amsa masa cewa shi ne, dan haka likitan ya mika masa wata takarda kafin yake kara masa bayani kamar haka" Docter Mu.azam ya bar maganar cewa idan za.a shiga aikinsa a baka wannan takarda ka saka hannu, takardar na nufin idan Har Allah bai yi ya fito kalau ba kai za.a ba gawarsa ba likita zata birne shi ba,

Wani irin sarawa kan Wardugu ya yi, Wardugu dai soja ne, sojan ma baba, wanda ya shiga gwagwarmaya da manyan yan ta.ada, wanda ya kwana cikin rami, wanda ya shiga hatsari kala daban daban na rayuwar yau da kulun, yau gashi gaban ikon mai duka, yana ji yana gani ya karbi biro ya saka hannun idan amininsa ya mutu a dakin tiyata a bashi gawarsa,

Yana saka hannun suka karba suka juya da Mu.azam dake sheme tamkar gawa,

A hankali wardugu ya kai wajen garu ya silale dan baki daya kafafuwansa rawa suke masa,

Agaishat da ta bi su da kallo sun fice mata da miji ta juyo da sauri wajen Wardugu ta karasa ta duka daidai inda yake yana kallon waje guda , murya a rikice ta ce" Ina zasu kai shi? Ina zasu kai min shi? Ina zasu kai min mijina? Ya mutu ne? Me ya sa suka tafi da shi? Wayyo Allahna, Wayo Allahna ,
Ta fada tana karasa zubewa kasan ta fashe da wani irin kukan da ya jima yana cin zuciyarta,

Wardugu dake kallonta ya lumshe idannuwansa kafin yake budewa,
Hannunsa dake rawa ya mika ya janyo hannunta kusa da shi sosai,
Murya can kasan makoshi ya ce" ba mutuwa ya yi ba Agaishat, aikin ne aka shiga da shi, ki daina kukan nan na tuba ki rufa min asiri ki yi shiru👏🏻,

Maimakun ta yi shirun sai kara kukanta da ta yi tana ta rike hannunsa tana kiran ya kaita wajensa, ya kaita ta ganshi, kar ya mutu ya barta, tana son sa!

Ido kawai ya lumshe ya yi shiru ya damke hannun nata, bai kuma yi mata magana ba sai sauraron sambatunta da yake tamkar ta zauce ,

Wasa wasa awa daya, awa biyu awa uku, awa hudu, awa biyar, awa shida ba.a fitar da Mu.azam ba, daga dakin sun canza waje ya fi a kirga inda karshe suka dangana dan nesa da dakin tiyatar kusa da Khadija dake zaune tana wani irin numfashi tamkar mai athsma, da kyar aka barsu suka tsaya nan din sai da aka kusan kwasar rashin mutunci da Wardugu kafin masu tsaron asibitin su bar shi,

Agaishat zaune take jikinta hade da garu itama tana rawar sanyi, zazabi ne jikinta inda Wardugu ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kai kawo yake hankalinsa ba a kololuwar tashe.

Suna haka baban likitan asibitin ya fara fitowa, nasara ne mai sunna,Roger , shi ya jagoranci aikin inda likitoci kamarsa biyar suka taya shi,

Khadija ce ta fara mikewa ta nufe shi jikinta na rawa baki daya,

Daidai nan wasu uku suka fito suma suka tsaya kusan docter Roger,

Tambaya ya yi cewar" ina Wardugu?

Wardugu da ya tsaya yana hangensu ya ji gabansa ya fadi, a hankali ya shiga takowa inda wata zazafar zufa ke karyo masa, du takunsa guda daidai da mutuwar tunaninsa yake har ya karaso kusa da likitocin,

Likitan ya dago kansa cikin wani yannayi ya ce""".......

😳

🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫

https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp

*☀IDAN RANA TA FITO WRITER'S ASSO🌤* ____________________________________________

*Fad'akar da al'umma tare da nishad'antar da masoya shine fatanmu*😘🤝🏻😘

Na
*SAJIDA*

5️⃣4️⃣

Likitan ya dago kansa cikin wani yannayi ya dubi Wardugu kafin ya dubi Khadija, ya ce" mun fito aiki, za.a fitar da shi a saka shi dakin observation na sati biyu, komai nasa zai dawo hannunmu na tsayin wannan lokacin, cinsa , tsaftarsa, komansa, tsakaninku da shi sai dai ku ringa hango shi ta jikin madubin dake makale da dakin, ni kadai zan iya shiga in daidaita komai in fito, za.a baku takardar magani da kuma irin abincin da za.a ringa saka masa ta mesa ta hancinsa, fatan ka fahimta idan baka gane wani abin ba sai ka tambaye ni ko ka tambayi matar tasa *Docter Khadija* ai ta san komai itama zata kara maku haske,

A hankali ya karkata dubansa wajen Khadija inda Docter Rogger ya raba ya fice, sauran docters din suka shiga bata hannu sunai mata murnar an samu nasarar aikin ciki sai fatan ya farka daga dogon barcin da aka luluka shi wanda farkawar shi ne zai shaida aiki ya yi ko bai yi ba wanda a kala zai iya kai sati biyun idan komai ya je daidai ko sama da haka abinda ba.a fata , sannan aka bata abinda aka cire a cikin kan , du suna yi suna nuna itace matarsa suna tayata murna wardugu na tsaye a wajen kuma da yarwn French ne ba abinda baya ji

Dubanta dai kawai yake uwa ya samu tv, ita kuwa ta ki yarda su hada ido da shi ko su samu zama daga ita sai shi,
Tana gannin likitocin samu tafi ta dan dubo shi a yannayin daburce ta ce" zan zan je na karbo takardun,

Bai bata amsa ba har ta bacewa ganninsa tana sauri tamkar zata fadi,

Juyawa ya yi yana kallon Agaishat da itama tunda suka nufi wajen likitocin take kallon su, bata san abinda ake ciki ba, bata iya yaren su ba, sai ta zama bakon Tv, dan dukan idannuwanta ta bude tana bin kowa da kallo ko zata fahimci wani abin,

Yana nan tsaye yana hangenta yana tunanin me zai ce mata Khadija ta dawo ,
Kanta take dan sosawa irin na mai laifi wand Wardugu ya gama karantarta watsi ne ya yi da lamarin da baya son shiga abinda bai shafe shi ba,

Rakardun ta mika masa ta shiga masa bayani kamar haka" kasancewarsa ma.aikacin asibitin nan wanda suka dauka da kansu yake karkashinsu zai biya rabin kudin aikin wanda ya kama millions 3 da dari takwas, sai riko gado kulawa shima tabin kudin ne ya kama jika dari bakwai namu na cefa,
Sai takardun magungunna da za.a ringa karbo masa a nan cikin pharmacy na asibitin shima yanzu zan je na karbo takardar da zata bamu damar biyan rabin kudadan magungunnan du zamuna karbowa ,

Sai da ta gama yi masa bayannin du yana karbar takardun kafin take miko masa carte din Mu.azam da kuma tata ta banki ta ce" ga carte din mu na banki, ga takarda mai dauke da code din mu wato reference din mu, idan aka hada na mu biyun na tabata kudin zasu isa har a salame mu,

Da yake du bayannan nan da take idannuwanta basa kallonsa dan mugun kwarjini yake mata sai da ta ji bai karbi takardar da carte din ba ta dago da dubanta a hankali ta dube shi,
Fuskarsa ya yatsina ya juya ya barta nan tsaye da takardar da kuma carte din, aman ya karbi baki daya na asibiti da za.a biya, na magungunnan,

Tana nan tsaye tana kallon sa ya fice ya tafi infa Agaishat ta bishi da kallo,

Kanta ta daga sama ta lumshe idannuwanta, a yau ta ji wani irin takaicin da bata ji ba na rashin karatun zamani da basu samu ba, ta zama tamkar kurma marar wayo a cikin mutane, bata gane yaren su , sun zame mata sababin mutane sun zame mata sabin halitu, gashi wanda ya kawota kasar take zaune dominsa kansa ake bayani aman bata san komai ba, yau kam ta yarda da maganar Ayya inda take ce mata" Agaishat, ban ki maganar baba tsofo fannin karatun zamani ba, aman ina son ki sani a rayuwa komai yana da anfani, karatun adini, karatun bokon ne , neman sani kan abubuwa ne, shi dan adam ana so ya zama mai yawan bincike kan lamarin zaman yau da gobe, neman ilimi ba laifi bane, jahilci baban ciwo ne wanda bashi da magani, idan aka ce jahilci kuwa ba ana nufin mutun jahili ba, ana nufin abinda baka sani ba yake a cikin duhu gareka .

Idannuwanta ta dan bude gannin Khadija ta koma wajenta na da ta zauna, bata ko nemi zuwa wajen da Agaishat take ba bare ta kwatanta mata wani abin,
Tabas hasashen Agaishat ya gama tabata a kan Khadijar da mijinta,
Dan ka fito daga birni, baka yi karatun boko ba, ba ana nufin kai din wawa sakarai bane, kana hankalce da komai, hasalima ka fi wasu yan birnin lura da gane lamura a kallo kawai bama sai an fada maka ba,
Ji ta yi an shiga hakkinta da yawa, ji ta yi ba.a mata adalci ba, zuciyarta ke ingizata da ta mike ta tarar da khadijan ta fada mata ta gane soyaya suke da mijinta, aman tana so ta fada mata halin da yake ciki, ko ba komai a tunaninta kusancinta da shi zai fi da kowa duba da itace matarsa, wada ya dace ta zama sirinsa, aman sai ya kasance itace wace bata san komai game da shi ba, wata zuciyar ta ce" ki ce da ita me? Wato ke mai hayagaga ko? To dan ya mayar da ke baya cikin komai nasa sai me? Me kika sani , ina kika sani, me zaki iya yi masa a cikin lamarin? Ke ko a kauye kin zama koma baya cikin y'ayan Ba bale a birni, birni mai abin mamaki, birni mai mota mai jirgi mai kalolin fata? Birni mai madafi a daki? Birni mai tv mai abin allo? Ke kama kanki a hakama ya isa, ki saka ido ki yi adu.a, ki godewa Allah hakama ai ci gaba ne!

Idannuwanta ta yiwa wal wal wal irin ta harari kantan nan, ta dafe gaban goshinta da hannunta na hagu sannan ta dafe daidai zuciyarta da hannunta na dama, ji take zuciyarta na doka mata da sauri, takan shiga irin yannayin nan idan tana cikin yannayi na tsoro,

Ya kai minti talatin da fita kafin yake dawowa shi da wasu mutane biyu , dayan ya girmanta dayan kuwa shima saurayi ne mai jini a jika,
Su duka hannayensu da wasu manyan takardu masu dauke da tambarin asibitin wa.inda a cikinsu ne aka zuba magungunnan da take a way,
Chapter 54 · 0% Book details