← Book details Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 110

Sashe 3

Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read

Kansa ya dafe, ya kai dubansa kan agogon hannunsa, kallota ya yi ya yatsina fuska, can ya ce "Ayya (wato mama), Ayya inda medi mundu tam (wato mama ke rigimarki ta yi maki yawa)

Hannunta ta dora a goshinta ta shiga kai kawo, kai take tana kawowa, can ta dauki wani ihu ihu tamkar tana buda, ta je ta dawo ta je ta dawo, ta kallo shi cikin yaren hausarta da bata fita da kyau ta ce" shikennan rayuwar bariki (gayu) ta lalata min kai, shikennan na zama uwar da ina fadi ba.a saurarena, ko nima zaka kula zazafar gabar da ni ne kamar yanda ka kula da Abbanka (mahaifi)?

Hannayensa ya jimke ya daki garu da su, kafin yake juyowa wajen mahaifiyarsa,
Taku ya yi zuwa gabanta kafin yake sada kansa, shima cikin yaren hausar sai dai tashi ta fi dan goguwa ya ce" Ayya ba dai saboda wajen wannan bugudin (tsofo) ne kike daga hankalinki harda hada kanki kike min da wannan Bugudin (wato mahaifinsa)?

Kanta ta kawar ta ki bashi amsa hakan ya sa ya mike ya fito daga falon

Yana fitowa ya nufi wani dankareran mashin *ROUTIER* jibga jigban nan masu shegen tsada domin daga million daya abinda ya kai har million shida ne, kuma mashin ne ba mota ba...gudunsu ma daban yake da kananun mashin

Bakin gilas dinsa ya fitar ya saka ya tayar da mashin din ya yi masa wani irin ja wanda kana ganni tamkar dambe ake da mai jan da mashin din domin mugun karfi ne da shi ga kyau

Hangame gate mai gadi yayi don kar ya jawa kansa bali wajen Wardugu

Yana fitowa daga anguwa *Plateau* a birnin Niamey ya nufi *Francophoni* inda gidansa yake

Yana karasawa shima tuni an hangame kofar ya shige da gudun tsiya ya silala wani waje da nan ne ma.ajiyar abinda ya shafi mashin da motoci

Dira yayi ya juya da sauri sauri ya shiga hawa matatakalar bangarensa domin bangare daban daban ne da matarsa mai sunna *GALayn*

Wata yar karamar carte ce ya dora mai dauke da hotonsa ya dora daidai wani detecteur ya bada dan kara titeeee kofar ta bude
Caicaicaicaicaicaicai wash, gidan tubawa kamshi, wayo gidan batube ni.ima, bale mai auren gimbiya hajiar hajia, sarkin tsafta, sarkin ado, kwaliya ba dai a nuna mata ba, ta kasance cikin kamshi wanda indai kai ka ce zaka kwaikwaya sai dai ka tashi da mura (gaisuwa yar baba)

Sanyi mai hade da kamshi ne ya buso shi, sanyi mai sanyaya zuciya
Terrace din dakin fara kal kal kal haka take daukan ido ta sha guga,
Tafka tafkan salon ( kujeru) ne irin na zamani masu kalar fari kal kal sai dan coussin kananuwa sosai su kuwa masu kalar baki kamar yanda mauquette (capet)
Rido (wato labulaye) yen dakin suma kalar fari ne, sai dai farin ba kar ba kamar yanda kujerun suke , shi ya fi ruwa da kalar peinture (colern) dakin, shima an saka abinnan na daure labule baki wanda kana ganninsa ka san ba karamin kudi bane dakin ba wani tarkace aman komai ka kai dubanka ka san karshe ne sannan ya bada kala ta mamaki,

Nan ya yada zango, ya daga kansa sama ,
Iska ya furzar yana jin yanda takalmin matarsa ke tahowa kwaskwaskwaskwas
Kamshin da take fitarwa shima na daban ne, ta shafa turaruka har ta gaji,

Tunda ta fito take kallon yannayin fuskarsa, a cikin ranta ta ayanna" wani masifafe kuma ya hargitsa min yannayin miji?

Bata yi kasa da gwuiwa ba ta karaso kusa da shi ta daga damatsunnan hannayensa ta shiga masaging a hankali tana kara kallon yannayinsa

Murya can kasa ya ce" *ADIBIRA* (Matata)

Tsai ta yi tana kallonsa kafin ta ce" qu'est-ce qui ne va pas mon Bb? (Me ke faruwa Baby?)

Kansa ya kawar gefe kafin ya janye hannunta a hankali ya mike ya nufi uwar dakansa

Bakinta ta tabe, Galayn akoy saurin fushi, mace ce iya mace aman bata tunnanin zata tsaya tana wani bibiyar namiji ko waye shi balatanna wardugu? Wardugu zuma ne ga zaki ga halbi, wardugu ko a cikin tubawa tsoronsa ake, mutumin da idan ransa ya baci idan bai samu ya damki mutun ba yake suma? Mutumin da ya wawuri ogansa ya daga sama ya nana da kasa ogan nasa bama na niger ba domin a niger ba marichal, bako ne da kowa ke tsoro yana shayi, gardama kadan ta hada su General Wardugu ya daga shi ya nana shi kasa a gaban yaransa da kuma yaran general, wannan abin ya jaza masa da mukaminsa da komai shugaban kasa ya tsaya kai da fata aka tura shi daji can wajen mali sai da ya yi wata hudu ya sauko, aman maimakun abin ya yi sauki sai kara gaba da yayi, mutumin dake gaba tukura da mahaifinsa , fada yayi gwa da gwa cewa abansa ya kiyayi hanyarsa kan laifin da ya boyewa kansa sai shi sai mahaifiyarsa suka sani, ita a wa zata tsaya ta bi bayan wardugu da idan ransa a bace ka bashi hakuri yake hucewa kanka? Du irin yanda yake ikirarin shi yanzu ba ruwansa da fada da mutun na gugar jiki karya ne ! Ka yarda ka yi gigin kai masa wargin baya ce masa komai ya ciro daya daga cikin wukaken dake jikinsa ya burma maka idan ya so a kashe shi, Wardugu nada zuciya ta ainahin tubawa....

Mu je zuwa labarin *BAK'A CE*

🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫

Na *SAJIDA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

5⃣

Mikewa Galyn ta yi ta fice itama ta bi ta babar kofar danma ya san ta yi tafiyarta ta je ta kara bada turaren ruwa a jikinta ta fito ta je wajen da kys din motoci suke ta dauki guda ba tare da ta tsaya zabe ba domin kuwa kaf ciki manya ne

Tana fitowa ta shige motar ta tayar ta fice abinta wajen auren kanwar kawarta tana mai duba carte dinta ta bank dan ta tsaya ta ciro yayan banki na kari a wajen wasa....
Wannan kennan

Ya yi kai kawo ya fi a kirga, ya dafe kansa yana tunanin irin nacin mamansa kan abu, ita yanzu dan wani tsoho can daban zata dame shi kan sai ya kaita, shi ya san wani bai isa ya bashi lafiya ba aman har fadi take shi ya taimake shi yana yaro, an dai dudura masa itatuwa haka kawai za.a kashe masa kwayoyin jiki

Tsaki ya ja mai karfi, ya mike ya shiga cire kayan jikinsa masu nauyi ya rage masa culotte kawai
Da dan gudugudu yake kara taka matatakalar benen bangarensa har ya karasa bangaren da piscine dinsa take

Ba tare da wani tsaye tsaye ba ya fada cikin ruwan nan ya shiga iyo tamkar wani kifi yana kai yana kawowa ba wani alamun gajiyawa a tatare da shi

Ba ita ta kai gidansu ba sai can dare har wajen karfe tara abinka da jeji shiru garin sai kukan tsuntsaye sai jefi jefin samari da yan mata ana tadi domin sukan kai har goma suna tadinsu

A hankali ta shige gidan nasu ta samu ta leka kanta
Fitilar kwai a kunne, sai dai tana jiyo minsharin Abansu dan haka a hankali ta kutsa ta nufi dakinsu yan matan gidan

Mahaifiyarta ta gani zaune saman abin sallah, da alama ita take jira duba da irin yanda ta tsareta da ido

Jiki a sanyaye ta karasa kusa da ita kanta duke ta ce" ANNA

Bata amsata ba sai kureta da ta yi da kallo,

Ta jima duken nan, aman bata mike ba domin ta san wani abu guda da mahaifiyarta keda na buzaye tamkar wata yar gidan sarauta koda yake du buzuwa ko buzu haka ne dadaya ne basu da shi wanda mutane ke jifansu da sun cika *Ashak* ,

Can kamar ba zatai magana ba ta ce" kin ga, ko wani hali zaki shiga, ko wace rayuwa zaki fuskanta *AGAISHAT*, ki guji sabawa mahalicin ki, ki rike mutuncin ki , ki ci gaba da hakuri watarana sai labari

Kanta take gyadawa, kuma wani dadi ta ji har cikin ranta, ko ba komai ta san a duniya bayan baba Sofo Annartama bata kyamatarta, tana kawar da kai a lamuranta ne dan gudun fitina, irin yanda Abanta ke binta da shari kwararo kwararo ya sa mutanen garima haka, ba mai kulata da daraja, ko magana za.ai mata ba.a mata ita a mutunce, ya kasance ko gaishe da mutun ta yo sai ya yi mata yatsina domin Abanta bai barta haka ba har shari ya yiwa annarta kan cewa ko dai wajen baba Sofo take zagayawa gannin irin yanda ya damu da ita ?
Wannan wutar kafin ta mutu sai da aka sha tashin hankali, baba tsoho ya yi kuka sosai aman bai daina kula Bak'a ba domin tana da mutunci yarinyar, shi Allah bai azurtashi da yin auren bama domin bashi da lafia ko ya yi ba anfani hakan ya sa yake jin yarinyar tamkar yar da ya haifa, itama tana mutunta shi tamkar mahaifinta

Mamanta na gama fadar haka ta yi shiru kanta itana a saden tamkar tana gaban sarakuwarta

A hankali ta mike ta nufi dakin su

Tana zuwa ta tarar du sun yi baci abinsu dan haka ta dauro alwallah ta shige ciki ta tayar da sallah ta shiga ramuwar wa.inda batai ba , tana so du rintsi ta ringa samun gurin sallah sai dai tana tsoron mutane da kwagirar su, yanzu za.a wulakantata dan haka take bari idan ta zi gida sai ta yi wanda bata samu ta yi ba

Tun karfe takwas na safe Aba ya fice bayan ya canza rawaninsa daga baki zuwa maroon turkudi sabo fil, ya sayi tufafi ya sayi rawanininka harda waya, ya fito sabo kudi sun fado shikennan a haka zai fada su tamkar wuta shima ya dankaro aure daga an cinye kudin shikennan ta gudu abinta

Bai jima sosai a wajen ba ya dawo,
Daidai lokacin Anna na fitar da dawar masararsa a ruwa wace ra jika dan tana son yin garin tuwo
Chapter 3 · 0% Book details