Sashe 4
Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read
Bai yi mata magana ba ya zarce dakinta dake baban daki idan ka cire nasa a gidan, daman dakuna uku ne, da nasa da na Anna da na yan matan gidan
Bai yi wata wata ba ya shiga kwasar kayanta yana kaiwa dakin yan matan yana jibgewa gefe guda,
Ba wanda ya tanka shi ko ya yi mamakin lamarinsa domin sun san halinsa, haka yake du idan zai yi aure dakin mahaifiyar su yake fitar da ita ya hadeta da su ya kawo amarya, bama zai barta a dakinta ba sai dai ya hade su ya kawo amarya su sha shagalinsu ba wanda ya isa ya yi magana yanzu zai cici masa uwa ko waye
Ko kallo bai isheta ba, don ta daukarwa kanta alkawarin in dai ba mutunci ne lamarinsa toh ba zatana kai kanta yana wulakantata ba gaban yayanta.
Sai da ya gama fitar da komai kafin yake fita ya shigo da magini
Sosai aka gyara dakin ya yi tas da shi
Tare suka fita , sun jima sosai kAfin yake dawowa
Wannan karon kuwa masu shigo da kaya ne
Mariama dake wanke fuskarta bayan ta shafa kurkum ta yi tsai tana bin kayan da kallo,
A gaskiya siyayar idan ka yita a kauyen ka isa ne, tun daga gado har kayan abinci na gayu ya kwaso abinsa sai dai abin haushin babu rabonsu a ciki na amarya ne, domin idan ka auri jar buzuwa ko duniya zaka kai gidansu nasu ne ba za.ai mata komai ba sai dai a kawo maka ita daga ita sai butarta (a kauye fa kar a ce inji sajida🤣)
Sai da suka gama kawo kayan tsaf Mariama ta je faban mahaifinta ta tsaya masa kerere a gabansa, somin kuwa in dai haihuwar rashin mutunci ne ya haifa Mariama ta isa ta iya tsayaya tamkar mahaifinta
Ido tar cikin nasa da yaran buzanci ta ce" Aba ya haka? Na ga ka fara kwaso kaya alamun aure zaka yi? Ya baka fitar da mu ba? Baka ba anna kudin siyayar kayanmu ba?
Kun san wasu iyayen sun fi son yaya masu tsayayar nan, domin Aba yana dan shayin lamarin yar tasa domin a yanda yake gani tama fi shi rashin mutunci dan haka ya dan gyara rawaninsa irin zai yi magana ya ce" wani siyaya kuma? A sanina cikakiyar buzuwa ba.a yi mata kayan daki?
Ta yatsina bakinta ta ce" sai kuma cikakiyar buzuwa ana yi mata sutura
Karya ne Mariama, ya fada yana matsowa kamar zai doke ta, ya ce" ku ne yayan zamani kuke zuwar mana da abubuwan da suke neman fin karfin tunanin mu, ko uwarki haka aka bani ita, haka ake kai ku daga ku sai turkudin amarci da buta, kudin auren ku kuwa mu iyayen ku ke siyan maku kadara mu ajiye maku a nan wanda idan kun waiwaya zaku ji dadin su
Wani malalacin murmushi ta saki tana kallonsa
Ya ci gaba da fadin" ke da kin ga minister ne ya turo a nemi aurenki, ya saya maki komai, sannan ke da auren wata shida ne zaki yi ki kwashe komai ki dawo mini mu more da kudi?
Tar ta kara saka idannuwanta cikin nasa kafib take juyowa ta ga mahaifiyarta ta fara daka dawar da ta wanke ta baza a rana ta sha iska tana so ta mayar da ita gari kennan , ta kuma kai dubanta wajen yayarta *BAK'A* dake ta dirzar wankin yan matan gidan harda na su kanenta ita dai burinta idan sun tashi su bata konce, ta kuma kallon mahaifinta dake kokarin shi dole sai ya yi mata wayo, wai wani harda cewa wai ya siyar masu kadara, shi? Kudin aurwnsu bai taba wata a hannunsa ba komin yawansu zai kashe su ne ya dawo talakansa marar mutunci, yan yatsunta biyu ta hade ta yi tap tap da su suka bada dan sauti kafin ta ce" ka kirga kudi, ina so ka bawa Anna kudi har million shida a cikin kudin da ka karba na auren mu domin na sani cinikinmu kake tamkar abin siyarwa baka amsan kasa da goma, ka bamu shida mu je birni tare da Anna mu siyo kaya mu dawo idan baka yi haka ba zan shiga duniya na saka ka a matsala kai da wanda ya kawo kudin aurena, ka san ni horonka ce
Yana tsaye bami bude har ta fice a gidan, kallonsa ya dawo wajen Anna, da sauri ya karaso ya ce" kina jinta kika yi tamkar baki gani bayan kin san tana jin nauyin zuciyarki? Ko ke kika kitsa mata a taru a cuce ni? Har million shida? Ai kudin sun kusa karewa idan na baku haka!
Bata bashi amsa ba ta ci gaba da dakanta , nan ya juya wajen Agaishat ya ga shi take kallo
Ke dan ubanki daina kallona da wasu tula tulan idannuwanki masu kama da na mayu, shegiya da aka kwaso cikin ki a waje aka yayaba min, dan bakin jini ko almajiri na yiwa tayi guduwa yake, zan zo in kwakwale miki idannuwan nan in baki a hannayen ki ki je ki kaiwa tsohon dan iskan nan da kike zuwa kina wuni wajen shi wama ya san ko me yake maki a bukar nan
Da sauri Annan ta juyo wajen shi, ta kai dubanta wajen Agaishat da ta sada kanta jikinta na bari, tausayin yarinyar ya kara dirar mata, nan ta kara gane shi ya sa idan ta fice take cika dare dan kar ta hadu da mutumin dake mahaifinta aman ya zamo makiyinta , ta rasa da wata kalma zata kirayi mutumin dake miji a gareta, ta san ya yi karatu, sai dai son kudinsa ya fi imaninsa yawa
A hankali ta ce" ki je kawai zan idasa maki aikin
Da sauri ta ajiye wankin ta warware mayafinta na bakin turkudi butubutu da shi ta yane jikinta gaba daya ta fice har tana hardewa tana waiwayen gidan nasa
Bakin wata bishiyar mangwaro ta zauna ta fashe da wani matsanancin kuka mai karfin gaske
Ku mu je a labarin Bak'a ce na sajida
🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
6⃣
Kuka take tana murza goshinta a kan cinyarta dake lulube da turkudi, hawayen nan ya jika turkudin ya yayakune sannan ya gogun mata a fuska ya kara rinar da fuskar ya kasance wani waje ya fi wani wajen duhu sosai fuskar du ta yi jirwayi da ita
Sai da ta ci kukanta har kanta ya fara ciwo kafin take yin shiru, mangwaron nan ta kuma kallo gannin du ya yi jajajir ya nuna ya saka ta mike ta gyara zaninta da kyau ta kama kokarin hawa ,
Da kyar ta hau bakibakin ta kamo wa.inda ke kusa ta tsintsinka ta diro ta zauna nan tana gogewa da hannunta sai kuma ta sha abinta, yau bama zata iya zuwa wajen tsoho ba ta san yana da ruwa goronsa kuwa ta kai masa gobe sai ta yi safiya ta je wajen shi
Wardugu, yanzu yanzu?
Kansa ya dafe ya ce" Ayya ko kin fasa tafiyar ne?
Da sauri ta mike ta nufi dakinta tana dafe kanta, yaron nan akoy kagauta , bashi da hakuri yanzu in ba rigima ba a kai tsayen nan ya zo yace su yi tafiyar da a yanda ake bata labari garin can cikin jeji ne? Aman ba komai irin yanda take mafarkin mutumin nan abin ya tsaye mata a rai, tana tune sun yi da shi idan yaro ya samu lafiya sai ta bashi salama da abinda ya sawaka sai dai ta zo tana yiwa Wardugu magani da magungunnan aka tashe su daga garin aka maido su Capital tun daga shi bata kara ganninsa ba domin ta neme shi sosai, sai kwanan nan take jin lanarin yanzu tsufa ya kama shi sosai baya yawo yana garinsa na haihuwa harma an fada mata sunnan garin , tana son sauke nauyi domin kuwa tun daga kan maganin wajensa Allah ya aminta wardugu bai kuma Huka ba sai tana gannin haki ne ta je ta sauke ba wanda ya san gawar fari
Nade ta fito da lifaya mai ruwan ja da kyalkyalin zaiba, lifayar sai baza kanshi take , Ayya ta kwana biyu a duniya aman karshe ce, akoy iya ado da sannin hakin turare, idan ka ganta sai ta birge ka gata da saka zinare tamkar ba da kudi take siya ba, danta ya bata damar murza mulkin da ta ga dama
Tafiyar manya ba.a kwasan tufafi, mai aikinta baturiya ce ta fito da wata yar valise (yar akwati) yar karama wace a ciki ta saka du wani abin bukatarta ta nufi kofa dan kaiwa cikin mota
Gaba ya yi yana amsa waya da aminiyarsa, kawarsa, wace du duniya itace babar kawarsa sai wa.inda ba za.a rasa ba, itace basa fada, ta iya tafiyar da lamarinsa ta iya zama da shi , sannan du irin yanda ya ki jinnin jajayen buzaye ita wannan baya iya kyamatarta , ba.a shaifar mutun aman shi zai bigi kirji da halayen *ALHINAYETT*
Kana nufin yanzu yanzu? Bama zan yi maku bankwana ba?
Wardugu ya ce" Alhinayettt bafa wani jimawa zamu yi ba, ke dai ki yi mana adu.a
Yana fadin haka daidai yana zama cikin motar Hilux tamkar wani daki tana fa fadin waje,
Sai fa ya gama wayar ya dubo AYYA da ta tsura masa ido
Kallonta yake da alamar mamakin kallon domin irin kallon nan ne na tsare mutun idan ya yi karya
Bakinta ta dan turo ta ce" kuma ka ce ba budurwarka bace, mutunci ne bakwa wata soyaya da ita,
Murmushi ya yi do.in daman ya saka a ransa wannan ne, ya dan sasauto ya riko hannunta ya ce" Anna, aa, Alhinayett aminiyata ce, wace bani da amini ko aminiyar da ta kai ta
Yatsina fuska ta yi ta ce" karyar banza wai aminci mace da namiji ? Ai ba shi sai idan soyaya ake
Kawar da kansa ya yi ya ce" kin ce a lokacin da ya baki magungunnan da aka dura min ma tsofo ne, kuma har yanzu kina da tabacin yana raye? Ni din ma fa na jima a duniya