← Book details Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 110

Sashe 62

Bak'a Ce Part 1 Complet Hausa Novel · about 8 min read

Sarki dake dan nesa ya yi gyaran murya ya ce" ai mai yiwuwa sunma taso, duda na fada masa kar yayi tafiar gagawa aman fir ya kiya,

Anna ta kale shi da sauri ta ce" aa, kar su taso a mota bayan har dare yayi, dan Allah su bari mu mu tarar da su,

Sarki ya yi murmushi ya ce" mota fa, aa, ai yanada jirginsa da ya malaka wato ket privé, sannan yanada damar tashi a lokacin da ta kama dan sune hukumar.

Wani sanyi ta kara ji a ranta a yau yau kennan idan Allah ya yarje mata zata ga mahaifanta? Kai Allah da girma yake, Allah da jinkan bayi yake.

Paris

Wardugu na kowama Hotel ya fice a motar ba tare da ya cewa Agaishat ta fito ba, hasalima kule motar ya yi tana ciki ya shige hotel din

Yana zuwa dakin da ya dauka ya dauki jakarsa ya zuba abinda yake iya dauka ya goya ya dauki echarp na maza na wuya ya rike a hannunsa ya fito ya basu kys dinsu ya fice abinsa

Yana zuwa motar ya ga ta kara volume din kukanta aman yana zuwa ta yi dif tana kikifta ido,

Motar ya bude ya shiga ya ja,
Bai zame ko.ina ba sai butik,
Yana zuwa ya fada masu kaya yake so a zaba mata cikin gagawa da dan kwali,

Abinka da kasar ......, sai ya kasance suturun da ake nuno masa du daga dogon damamen wando, sai yan bintiyalan riguna, sai dogayen riguna aman masu mugun bin jiki,
Kansa ya dafe gannin lokaci na neman yi ba damar ya je wani butik din sai jirgi ya barsu, ransa ne ya kara baci wai su basu da Abaya ne?

Basu da Abaya, sai da babarsu ta mike da kyar ta zakulo cikin kayansu masu tsadar gaske wa.inda sai wane da wane suke nunawa su ko a kasar, ta cirota wata riga blue mai hasken sama ta kawo masa tana tunanin bama zai iya ba dandai idan batai masa ba ya dauki wata ne dan tsadarta

Dagata ta yi inda suka bita da kallo, doguwar riga ce itama mai rike jiki bale daga sama, aman tanada dogon hannu daya kwal, sai dan siriri tamkar na shimi da akai masa wani irin kwana aka malaka shi jikin rigar daga sama,
Sai dan kwali irin kananuwan nan sosai shima mai sharashara mai ruwan fari fari da blue blue din

Kansa ya dafe yana duban kayan, ba kudin da aka fada masa bane damuwarsa dan kudin sun kai jika dari hudu, aa, yannayin rigar ne, aman gannin ya yi rantsuwa, sai kawai ya bata umarnin ta shiga wajen saka kayan ta saka su fice,

Da sauri mai butik din ta nuna mata ta bita ta tsaya daga kofa ta saka kayan sannan ta shiga ta gyara mata sosai, ta saka dan kum ta dan cacaje mata lalausan gashin kanta ta dora mata dan kwalin ya nadu ya yi kyau a fuskarta,
Wani irin kyau kayan sukai mata sannan suka fitar da kirar jikinta inda cikarta ta bayanna ,

Waouh macen ta fada kafin su fito tana nunawa Wardugu,

Mikewa ya yi bai kaleta ba dan shi ba dan hakan ya zo siyen kayan ba ya karbi jakar takalmin ya mikawa macen sannan ya juya bayan ya cewa Agaishat idan ta saka takalmin ta dauko wa.inda ta cire din maza su tafi

Da sauri ta saka takalmin, Allah ya taimaketa bai daukar mata mai tsini ba, plat ne mai igiya dan haka ta daura igiyar ta dauki wa.inda ta cire ta fito da sauri sauri ta nufi motar

Ja yayi suka tafi, tana ji tana ganni ya tsaya kofar gidan da bada jimawa ba yake gidan mijinta ya jefa kayan da ta cire ya dawo ya shiga motar yana tafe yana waya da yaronsa har suka karasa aeroport din

Nan suka iske shi har ya karaso dan haka wardugu ya bashi ky din motar sukai salama suma suka daga sai Niger Garin taraya Niamey garin zabarmawa, garin ka zo na zo

*Niamey*

Mota na tsayawa na fice da gudu daga motar inda sai a lokacin ya bita da kallo, yanda ta kwasa a gujen har dan kwalin kanta ya sulube daga saman kan nata ga yanda jikinta ya jijiga ya jijigo ne ya saka shi kawar da kai yana astagafari dan kuwa matar da batai idar sakin mijinta ba kalonta haka ai ba kyau🤨

Dan zama ya yi yana tunanin ya shiga ne ko kawai ya yi tafiarsa?
Wata zuciyar ta fada masa Wardugu Ayya fa mahaifiyarka ce, kuma indai kere na yawo, zabo na yawo watarana an hade, dan haka ka je!

Ayya dake zaune tana kallon tv, a lokacin wajen karfe takwas da rabi na dare ne,
Sai jin kukan y'arta ta yi da ganinta ta fado da gudu ta fada jikinta ta kankameta tana rizgar kuka,

A rikice Ayya ta shiga kokarin tashi da ita tana fadin" Agaishat? Agaishat? Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, Agaishat ke ce? Lafia ? Ke da wa kuka zo? Me aka yi? Ina mijin naki? Ina wardugun? Ke?

A daidai lokacin Wardugu ya shigo yana tafia a hankali ya karasa saman kujerar zaman mutun guda ya zauna yana dubansu yanda ta makalkale Ayya da irin yanda Ayya ta rikice sai tambayoyi take tana duban wardugun,

Kamar daga sama ta tsinci maganarsa, koma tace kamar saukar mari, ya dan ja iska yana duban Ayya ya ce" *Ya saketa ne*,

Dif Ayya ta yi da tambayoyinta tana duban Wardugu, saki? Abinda kunnayenta suka jiyo mata kennan?

A hankali ta kankace idannuwanta tana duban Wardugu zatai magana kennan ta ji Agaishat ta ce" Ayya wai ya sake ni, Ayya ban san laifin da na yi masa ba,

Ayya ta kallo wardugu ta ce" Saki,? Aka yiwa y'ata? Shin ciwon nasa haukata shi yayi kafin a gane har na dauki y'a na bashi ? Mahaukaci ne da riga?

Wardugu ya dago yana duban Ayya da auna yannayinta, daga muryarta ya fara dauko cewa Ayya ta fara hawa, wato tana harhada dukan abinda gareta na tashin hankali wanda yayi imanin zata saki a yanzu yanzu,

Ajiyar zuciya ya saki ya ce" da hankalinsa

Ayya ta zabura ta mike tsaye, idannuwanta ta karasa kankancewa ta nuno wardugu da dan karamin yatsarta ta ce" ni? Ni zaku yiwa wulakanci? Ni zaku tozarta? Ni zaku watsawa kasa a ido? Ni zaku tonawa asiri? Ni zan dauki yarinya na baku ko wata batai ba ku sako mini bayan ba kangarariya na baku ba kuma ba hujajen buhu na baku ba? Ba nakasashiya na baku ba kuma ba neman kai nake da ita ba na dauka na baku ba? Gaskiyar Aghali, a lokacin da ya zo min bankwana nake fada masa maganar kun tafi neman aurwn yarinyata yace da ni haba Ayya, ai da ni zan ce ina so, na yi mata dukan abinda za.a yiwa yar gata na aureta a kaita gidana na kula maki da yarinya, aman yanzu kika baiwa abokin Wardugu kin tabata zai rike maki y'a?

Wardugu ya dago kansa da sauri, dan tunda ta fara maganar kansa ke sade, bai yi niya ba, bai so tanka Ayya ko daya ba, dan an bata mata tanada damar yin fada ta yi abinda take so, shine mai laifi dan shi ya uzurata , ya lalabata har ta aminta da a je a dauro auren, ya so yin shiru ta kare kansa, shi kuwa tasu shi da Mu.azam ne, Takunsu na gogagu ne, zasu goga ! Sai dai ji yayi bakinsa ya ce" Haka yace kennan?

Ayya ta ce" Ubanka yace Wardugu, nace Uban nan naka yace! Ba gashi ba ya nuna halin ba.a je ko.ina ba? Sai na yi shara.a da shi! Ba zan barku ba ku duka! Wato an baku y'ar a saukin kudi ko? Baku yi tade tadensu na buzaye ba kun samu abin a bagas ko?

Agaishat dake kallon Ayya, ta ce" Ayya, dan Allah a bashi hakuri ya mayar da ni , walahi ba zan kara yi masa koma mene yace na yi masa ba,

Ayya ta juyo da mamaki ta rike habarta ta yi tsai tana kallon Agaishat inda dakin ya dauki wani dan shiru, can ta ce" kina ji? Ki tashi, ki je dakinki ki cire mini wannan rigar ki yi mini wanka ki wanke ruwan gidan wannan banzan, ki yi sallah ki kwonta ki yi baci tun kafin na yi baja baja da ke a gidannan! Ka ji rashin sannin ciwon kai? Namijin zaki turani lalabo shi? To ko ku haka kuka a tadanku na buzaye na soke maki hakan a rayuwarki na haramta maki hakan! Walahi walahi walahi ni Ayya in dai na rike ki ko na kwana daya ne karya ne ki kuma waiwayar wani Mu.zzam koda shi daya kwal ya rage a duniya! Agaishat bace min da ganni kafin na maki marin da zai kufumta maki kunne!

Da sauri ta mike tana karkarwa ta shiga taka matatakalar benen ta haye da gudu ta nufi dakinta tana waiwayen Ayya dake tsaye sai da ta bacewa ganninta ta juyo wajen wardugu,
Takowa ta yi har gabansa ta tsaya ta ce" in sha Allah na dauki alwashin sai ta zama abin hangensa daga nesa, sai ya yi dan daman bai sakar min y'a ba, ubankuma bai isa ba bale ku (wato Marahut), wasan kuke so bugawa da ni ko? Ni zaku kawowa wargi a wannan lamarin ko? Na gode , aman ka fada masa gidana da gaishe da ni sun haramta a gare shi! Yarinyata nada gatanta, in da hakinta kuma ban yafe ba!

Shi dai Wardugu kansa na kallon kasa, shi ganima yake da sauki tunda bata kai ga kifa masa mariba, sannan a haramtawar tata banda shi, dan haka ya sada kai sai da ta kare fadanta ta juya ta haye sama ya samu wuf ya fice a gidan,
Chapter 62 · 0% Book details