← Book details Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 90

Sashe 9

Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda ya yafito falonsa yaga mutun zaune shi duk tunaninsa FK ne ko cikin abokan aikinsa kallo daya Yayi mata ya dauke idanunsa daga kanta "yi yayi tamkar bai ganta ya nufi hanyar fita. ta taso da sauri tana kiran sunanshi " cigaba yayi da tafiyarsa danshi a ganinsa bai ga abinda zai sa ya tsaya ba ,.
ganin saurin bazai mata ba , dan haka ta kara da dan gudu da sassarfa har ta cimmasa ,a daidai cona da zata kai mutun main parlour din gidan tasha gabansa da sauri tana sauke ajiyar zuciya hade da cewa dan Allah yaya katsaya magana nake son yi dakai .
dubanta yayi tamkar bazaiyi magana sai Kuma yace meyye matsalarki dani ? Dan ji Yayi kmr ya dauketa da maruka " Kalmar daya fada ne yasa taji zuciyarta ta tsinke " Tayi wani irin tsalle kmr zata tafasa kirjinta ,.
Tayi shiru tana tattaro kalmar dazatayi amfani wajen fahimtar dashi abinda ke ranta .
cikin sanyi murya yace ina zaton kin manta ko ni wanene shiyasa kika tareni , sai da ta saita kanta sosai, ta'aro jarumta takara akan wanda take da" sannan tasamu kwarin gwiwa. cikin marairaicewa murya irin ta masu neman taimako tace dan Allah yaya" kadan bani aron lokacin uziri ne dani.
yamata wani irin duban dayasa yanhanji cikinta kadawa sannan yace uhmm ina jinki kuma ki tabbatar da uzirinnaki mai ma'ana ne .
"da idanunta ta amsa masa dan gabadaya ilahirin jikinta kirma yake tsabar rudewa datayi har wani gumi take fitarwa na wahala.
tun ba yau ba DEENi yasan shemah nason furta wani abu gareshi Amman rashin ganin fuskarsa yasa taki tunkarsa shi bema san dalilinsa na tsayawa ba .
Shi kansa yasan dole wannan ranar zata zo komai daren dadewa ".

ahankali take sauke ajiyar zuciya saboda fargaban da tashin hankali , abinda zai biyo baya " numfashi taja hade dayin kasa da kanta dan sam bazata iya kallon kwayar idanunshi a wannan lokacin .
Ahankali tasoma magana muryata kasa kasa cikin in...inna ,tace daman ..daman..ina son sanar dakai " ina..ina so.....da hannushi ya dakatar daita" tun bata kai ga karasa maganarta ba tare da buga mata wata irin razananniyar tsawa wanda yasa ba shemah ba ,har zeenat dake kokarin fitowa daga dakin ummi zuwa parlour "ta koma cikin daki da sauri " ta manne da jikin kofar hade da cewa wayyo... Allahna me Kuma yasame sa haka cikin tashin hankali ta sake mannewa da jikin kofar . , hatta ummi dake zaune a falo say da taji amon muryasa ,wani irin kallo yake jifarta dashi yace kina.... me uhmm repeat what u say , lip's dinshi cikin bakinsa yana cizawa sannna yace what ar u try to say ,ya sake jiho mata wata tambaya, still shr kake jin shemah ba bakin magana Amman gabadaya ilahirin jikinta ya dauki kirma .
Cikin isa da takama yace u better keep what'ever you won't say before I sikater you now jikin shemah yacigaba rawa kafafuwanta suka Gaza daukarta dana sani kuwa tayishi yafi cikin buhu , ya tsareta da mayatattun idanunsa " murya a kwasashe yace na sake jin kin Kuma furtamin wannan bazar kalmar wlh azim zakiga yadda zanyi da namanki stupid girl kawai.
ya ja tsaki ya wuce abinsa ta tsaya nan tana bin bayansa da kallo ranta a bace batasan lokacin da Hawaye yasoma zubo mata tana tunanin yaushe ne zata daina kuka akan son DEENi mutumin da take matukar so tamkar ranta mutumin da mata ke rububin son shi mutumin dayake jama mata aji ga shegen kyau da kwarjini " nan ta zube kasa ta risgar kuka ahankali hade da sa hunnta duka ta toshe bakinta dasu .

Zeenat dake tsaye jikin byn kofar dakin ,banda kirma bbu abinda jikinta keyi , tsabar frigice jin abinda shemah ke kokarin yi' domin taji duk abinda ya faru tsakanin yaya DEENi da shemah tsabar tsoro ne ya hanata fitowa ,wani irin kishi ne taji yana taso mata tun daga kan tsintsiyar kafarta yana bin ilahirin jikinta hade da kashe mata duk wani gabobin dake jikinta , taji a ranta da tana iya fitowa,. tabbas da ita kadai tasan yadda zatayi da shemah, tsinuwa kuwa iri iri bbu wanda zeenat bata aikawa shemah ba .

, ahankali zeenat ta sulale kasa ta dora hannuwanta duka bisa kanta.cikin kuka take cewa Shikenan ummi tacuce ni zata kai ni tabaro "gashi taki yarda da aurena ,da yaya DEENi ga wasu can suna neman farautarsa .
,ba tasan tana shirin jefa diyarta cikin halaka bane akan tilon danta.
dan ita yanzu ji take zata iya yin komai akan DEENI .
Ahankali Tace ita yanzu yazatayi da ranta , idan Kuma yace hakura daita fa ? Taji gabanta fadi
Da sauri tasoma girgiza kanta tace hakan ma bazai taba faruwa ba inshallahu sai ta aure yaya DEENi mijinta ne ita kadai , .
dan ita yanzu wani irin son DEENi din ne yashigeta na farat daya ,kmr kar taji ya furta yana sonta ...itama taji tana maseefar kaunarsa , Ita taji ta Gani zata iya rayuwa dashi akowani irin hali.
kawai,a hankali ta sake ta saki wani irin marayar kuka mai ban tausayi tana furta ummi karkimin haka dan Allah ..kar min haka ummi ke uwace gareni har da rabi .
dan Allah karki rabani yaya DEENi wlh zan iya zama dashi a haka , duk munin halinsa ina son shi " tunda harshi ne ya furta yana sona ...
gabadaya ta rikece da wani sabon kuka tana sambatu .
kuka tayi sosai har da shesheka ahankali ta sauko da hannuta bisa kirjinta" ta dafe kirjinta dataji yana mata wani irin ciwo zuciyarta na dokowa da sauri da sauri zeenat ta runtse idanunta dan ita kadai tasan yadda take ji.....

ta ciki dakin zeenat ke rizgar nata kukan ,yayinda shemah da ke waje durkushe ta nata .

Taku yake cikin izza da jin kai da jin shi wani ne yake takunsa har yakaraso ya zauna kujerar da umminsa ke zaune ya dora kansa kan cinyarta "ita Kuma ta'ajiye jaridar dake hannuta tun soma jin amon muryasa ta daina karatu datake "ya sakar mata murmushi gafen baki tamkar bbu abinda ke damunsa ,yace gud morning my first lov ....
ta daura hannuta bisa sumar kansa tare da fadin morning my son yakatashi lfy , ya dan tabe baki sannan yace nut bad ....
tace ya'akayi ne son me kakeson cine akwai dinshi iri iri akan darning wanda orready zeenat tashirya komai .
turo baki yayi cike shagwaba har zaiyi magana " kome ya tuna sai Kuma ya fasa cewa komai " ummi ta tsurawa fusharshi idanu tace kayi shr ya lumshe idanunsa muje kayi breakfast din ina lura da kai tunda kasoma zancen yarinyar nan bakason zama ma a gidan ballanantana Kaci abinci ahankali ya ware idanunshi akan umminsa sannan yace first lov na koshi fita ma zanyi yanzu ....

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Page 13-14

Bangane fita zakayi ba byn ko breakfast bakayi ba ina fa hankalce dakai fa duk kwanakin nan bakason cin abinci,
ina zaka ma tukun danaji kace fita zakayi naga week end ce yau .ta hade fuska ta mau hade da zuba masa idanunta.
Ya dan yi murmushi gefen baki har dimple dinsa ya lotsa" kyaunsa ya sake bayyana" ya mike daga kan cinyarta ya zauna sosai shima yana kallon yanayin umminsa" yana jin yadda soyayyar Ummi nasa fiyye da komai nasa "yana sonta baya son damuwarta itace duniyarsa sannan itace ke tattare da duk wani farincikinsa tana tsantsar " son shi da nuna masa duk wata kulawar da uwa kadai zata iya yin haka .

Hannuta yakamo duka cikin nasa ganin yadda ta damu muryasa a sanyaye kmr koda yaushe yace am so sorry my first lov muje zanci tayi murmushi tace kai ko hade da dan dungure masa kai "dan bazata iya fushi dashi "shi kadai Allah yabata " batada. Kmr sa duk duniya . Cikin dan daga murya Ummi tayi kiran zeenat .
DEENi ya yamutsa fuskar sannan ya langwabar da kai yace kibarta kawai "first lov .
ki zuba min da kanki nafi son naci dagareki dan ma banson wahalar dake ne ma da sabon girki zaki min yakarasa fadar maganar cike da shagwaba " ummi ta dubesa ta sake yin dariya tace Allah yashirya min kai yace Ameen yana kashe mata idansa .

byn yagama cin abinci duk da bawani abin kirki yaci ba "Amman hakan yatiwa ummi dadi ko bakomai ya dan saki ranshi ba kmr kwanaki ba" wayarsa ce ta sake karade parlour da kara wanda tun soma cin abincinsa yake jin kukanta "Amma ya" share.
ahankali yasa hannu ya dauki wayar yana kallon screen din " sunan FK yagani rubuce yana wayo "tabe baki Yayi kana ya manna wayar da kunnenshi , , FK najin alamun an daga wayar yace Yayi angon zeenat da girma "kujerarka . DEENi yaja tsaki yace ya'akayi ne" sarkin matsala.

bangaren FK kuwa shekewa Yayi da dariya sannan yace ina waje ina jiranka fa dan banson nashigo muyi westing time dan nasan halinka da son jikin tsiya " shima DEENi bay wani damu da shigorwasa ba dan baya son ummi tasan inda zashi ,

'Umminsa yake kallo har sanda yagama" waya sannan yace mata shi zai fita sai ya dawo tayi masa a dawo lfy " mikewa Yayi tsam cikin tafiyarsa ta kaisata ya nufi hanyar kofar fita ya daura hannushi kan handle ummi takira sunansa ya juyo yana dubanta tace kar kade fa yayi murmushi yace love you mum ya murda kofar ya fice .

Tsaye ya iske FK shi kadai jingine da jikin motar DEENI hannuwansa rungumeta da kirjinsa DEENi ya Mika masa suka gaisa sannan suka wuce kai tsaye gidan big dady.

FK na gaba DEENi na biye dashi a baya har suka karasa cikin gidan suka nufin inda suka san zasu tarar da big dady .

zaune suka hango tsohon mai tarin shekaru da dattako,sai dai" ya dan manyanta kadan domin shine "dan" Muhammad bello khaliyal na farko Kuma shi ke yanke hukunci ga duk abinda yataso dangane da komai" na cikin family .
Chapter 9 · 0% Book details