← Book details Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 90

Sashe 3

Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ko lokacin da ummi tadawo tuni murna da farinciki Ganin tilon "dan " nata yamamayeta zuciyarta nan suka zauna a parlour suna hira cikin hirar ne ummi take masa maganar aure in da tace masa yakamata yanemi mata yayi aure kasan shekararka nawa kuwa yanzu ?yayi murmushi ai dole nasan shekaruna ,muke nan kullum cikin rubuta date of birth ,talatin da biyu ne kawai fa ummi Tayi dariya 32 din ne kawai kusan duk sa'annin haihuwar ka duk sunyi aure acikin estate din nan gasu yasir nan ma duk ansa musu rana dan haka kaima ka fidda mata kafin azumi DEENI yazaro idannu yana bin ummi da kallo a shagwabe yace haba first love dan sunan da yake kiranta dashi kennan tun tasowarsa .... ni din guda nawa nake da zakice inyi wani aure yanzu. Dan Allah kiyi hakuri my first lov zuwa wani lokaci ,duk hirar da suke zeenat na zaune tana jinsu haka kawai taji gabanta na faduwa lokacin da taji abinda ummi tace ,Amma jin amsar da yaya DEENI yabata yasa taji wani irin sanyi na ratsa zuciyarta .
kmr ance ya dago idanunsa suka sauka cikin nata harararta yayi yace kallon fa kin wani tsare mutun da idanu, ummi tace uhmm kafa dawo kennan karka takuramin yarinya ,
ya langwabar da kansa yana maida idanunsa kan ummi cikin sanyi murya yace haba first lov baki ga irin kallon da take bin mutune dashi bane, kmr bata san mutun ba , ummi tace kai da wani idanu ka kalleta har kasan tana kallonka. kuma ma ni banga komai ba kai dai ta kurace kawai dakai indai kana gida baka barin yarinya nan ta huta ta sarara , ya dubi ummi ya tabe baki , Sannan yace ke....kawo min coffee ,ta mike taje ta hado coffee din takawo masa gabanta na wani irin faduwa ta durkusa har kasa ta ajiye masa .

Adaidai wannan lokacin ne zeenat ta kammala karatunta na secondary school , ta fito da sakamakon mai kyau domin tasamu almost 7 credit masu kyau .
shi kansa DEENI yaji dadi Sosai sanda ummi ta nuna masa Amman dayake miskili ne, sai cewa yayi Sam shi bai ga wani kokari da Tayi ba tunda bata cinye duka ba .
ummi Tayi murmushin tace kai ne dai bakaga kokarin ta ba. Amman ni nagani km nasan Tayi kokarin Sosai .
Ina laifi duk cikin wayanda suka rubuta jarabawa tare bbu wanda yakaita marks ,.
yace ok inda ta cinye duka ne zan iya cewa Tayi kokarin ai wayanda suke cinye 9 credit ba finta brain sukayi ba.
Ita dai wasa da kallace kallacen banza tasa a gaba.
ummi ta hade fuska tana harararsa yacigaba da zagin zeenat ganin yadda ummi Ta canza fuska ne ,yasa yabar maganar , ummi ta sake duba result din tana shafawa hade da kwallawa zeenat data tashi tun sanda taji DEENi yasoma zaginta kira ,takaraso tazo ta tsaya kusa da ummi DEENi ya dauki wayarsa yana daddannawa ba ko kalli inda take ba ummi ta mika mata slip din tana murmushin tace kinyi kokari sosai , zeenat ta karba ta juya ta bar gurin dan bazata iya zama a duk inda yake ba .
ummi ta dubi DEENI tace yanzu kuma sai aure zanwa zanwa yarinyata .
DEENI ya juyo a sukwane yace wani irin aure kuma first lov da rana tsaka , kudai Bari yarinya tacigaba da karatu kawai" dan yanzu kai yawaye , an daina irin wannan auren, ballanantana mata marasa illimi "ummi ta dubesa da kyau ta numfasa Sannan tace ni tawa iya secondary zan aurar daita dan ma taki sauraran masu sonta . itama shegen iyayi ne daita kuma dai kasan matan wannan family din basa wuce secondary ake musu aure .
kuma kasan baza'a fara karatun jami'a daga kanta ba, uhm nima nafi son na aurar da abita. DEENI ya tabe baki Sannan yace Allah ya kyauta ni ko zanyi aure bazan auren Yar secondary ba wlh sai wacce tagama jami'a mai tarin illimi ,kuma ba auren family zanyi ba dan baya birgeni. yakarasa maganar yana dan murmushi ,ummi tace to Allah yabaka sa'a. amman ni tawa aure zan mata da wuri .
kai kasan halin big dady bazai taba barinka kayi aure a waje ba .
Wlh nasoma a hada aurenka dana su yasir yace uhmmmm su dai yi nasu ni sai nan gaba .

A wata yammacin DEENI zaune akan dadduma awajen shakatawa shi da abokansa wayanda duk kusan , family ne zagaye dashi gefe guda kuma flasks ne cike da ruwan zafi da kananan cups , hira suke sosai atsakaninsu Amman banda DEENI dan gabadaya daukar hirar tasu yake shirme dan duk zance nasu akan maganar aurene wanda shi kuma Sam baya kaunar ji , dan haka ya sharesu yacigaba da lasalasar wayarsa ya yinda ya kai hannunsa daya ya dauki cup din coffee wanda orready fk ya tsiyaya masa ya kai bakinsa yasha hade da rufe rikitattun idanunshi wanda yazame masa jiki fk ya kalli yasir da faysal dake tawowa inda suke, ya kwashe da dariya har suka karaso bai bar musu dariya ba fk yace sannuku da karasowa Mayan angwane kunsha kamshin kunsha kamshin ,faysal yace kai dai anyi dan iskan yaro , kai baka tsaya ruwan ido ba kana biyewa wannan ya nuna DEENI da yatsa fk yayi murmushi yace yayi an gwanen bana wannan karon gabadaya suka dara hannu suka bawa juna suka gaigaisa har DEENI.
yasir ya dube fk yace ai gara muyi aurenmu tunda muna son juna kai ka zauna kar kayi har mahdi ya bayyana ,fk yace A'a nifa bance saboda me zakuyi aurenku ba . Amman gaskiya zaku takura kanku ne kawai yanzu da wani aure wayannan kananan bbys din.
DEENI ya tabe baki Sannan ya dube fk yace shiyasa rawar kan yaran ke kara yawa ba . dukkansu suka sa dariya suna cikin dariyar ne fk har da rike ciki sai gasu zeenat da suka taso daga islamiyya su biyar suka jero kowace sanye da hijab dinta raudat da shemah da samiha da Maryam sai zeenat dake tsakiyar su dukkansu kyawawane .
da hannut fk yake nuna musu inda suke Sannan ya dakata dariyarsa ya kalli inda DEENi ke zaune tamkar bai san abinda ake ciki ba , ko kallon inda suke bai yi ba, yacigaba daddannawa da sarrafa wayarsa .
fk yace kai gaskiya bbys din nan fa su hadu dayawa fa , nima ko zan dan shiga daga ciki ne.
yasir yace dako ka huta , kabar wannan ya nuna DEENi fk ya cigaba A'a ina ai bazan barsa ba tare zamuyi namu auren , ko yakace mutumina kaga Shikenan mun huta da surutu jama'a DEENi ya kallesa a kaikaice yace A'a ku dai da kuka ji zaku iya kuje kuyi Tayi .
Amman ni ya nuna kansa da yatsansa hade da tabe baki, ba yanzu ba" har sanda su zeenat suka zo suka wuce . Suna hirarsu suna dariya Maryam ce ke basu labarin abinda ya faru jiya bbu wanda bai dara ba har ita zeenat din raudat tacewa zeenat ai ke kika daukar masa wlh kuma yarinka yi miki kennan ina ma nice daya gane kuresan suka sake yin dariya .

Tun lokacin daya dawo zance sa da ummi bai wuce DEENI kayi aure fito da mata cikin yan,uwanka kayi aure hirar kennan sai dai idan basu zauna ba .
Chapter 3 · 0% Book details