← Book details Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 90

Sashe 50

Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Byn kmr minti ashirin Zaune Ummi da Zeenat suka taddashi kan kujerar one siter hannushi rike da waya yana daddannawa " a yadda yake operating din phone dinsa zaka dauka kwata kwata baya tattare da wata matsala ne" ballanantana wani abu makamanci damuwa , amman a hakikanin gsky kallo daya zaka yi masa kasan cewa yana tattare da kunci may tarin yawa .

,a fusace Ummi take kallonsa ganin yadda Ya hakince tamkar Bai san da tsatuwar wasu halitu a gurin ba.
,' yayinda gabadaya ranta a dagule yake da abubuwan da ya dinga yiwa inna a gaban dangi .
wanda inda wani ne yasanar daita zai iya yin abinda yayi" zata iya ransuwa da Allah akan sharri aka,a masa ,amman Sai gashi a gabanta komai ya faru.

ahankali DEENI ya dago rikitattun idanushin dasuka gama canza kala tsabar tashin hankali dayake ciki " ya zubawa ummi yana kallonnta ..

Ganin haka tasa , ummi sake hade ranta tamau dan batason yakawo mata rainin wayonsa dayasa ba "sannan ta cigaba dubansa .
,'tare da cewa yayi maka kyau... Deeni, da duk ma abinda kayi min, na gode matuka "tun daga kan dukar min yarinya dakayi tamkar kasamu baiwa tare da hado min ita da takarda saki har kawo abubuwan da suka faru a yau .
Dan wulakanci ma yau kusan tsawon kwanaka uku kennan rabon daka Tako kafafunka cikin gidan nan . tsabar kagama rainani .

shr yayi still yana sauranta ya kasa koda furta mata daidai da kalma daya ce .

, Ummi ta dubi inda Zeenat ke tsaye wace gabadaya atsorace take dangane da yanayin rayuwar data jefa yayan nata ciki .
,ummi tacigaba' ai kinga irin abinda nake gudar miki a cikin aurensa, wahala da zaman kunci tattare da nadama" Amman kike nace akan kinji kin Gani ' bbu wani abunda zai faru Sai alkhari " yanzu wa gari ya waya.
dubi yadda kika koma dan girman Allah tamkar wacce aka hako daga cikin kabari .

Da gani ba say ma an tmby ba nasa zaman hakuri da kunci kikeyi agidansa dan nasan may hali baya canza halinsa .

Deeni dake zaune yayi shr tare da cigaba da duban ummi kawai batare da yace mata komai " dan ma rasa abinda zaice mata yayi km yana son ta fahimce shi tasan duk abinda take tunani akansa ba haka bane amman Sam yakasa magana .
Ummi ta sake juyowa inda Deeni ke zaune suna fuskantar juna dashi .

" Tambayar da zan maka yanzu nake son ka amsa min d eh ko A'a.
daman can ba kai ne da kanka ,ka nemi auren Zeenat din a gurina ba?

.'ahankali Deeni ya dagawa Ummi kansa .alamun shine ya furta Yana son ta aura masa Zeenat din .

Ummi Tacigaba To yanzu dan ta zubar da ciki ne yasa har ka iya mata irin wannan dukan mutuwar ?
Km har da ikirarin zaka kashe min Ita dan baka san ciwonta ba .

Ko kana tunanin idan ka mata illa zan barka ne kaima .

Kai gaka sarkin en zuciya madadin ka kawo maganar gabana nasan yadda zanyi solving din matsalar batare da kowa yasani ba , shine ka tuzartata Tare da zartar da hukunci ta hanyar azabtar min da yarinya tamkar kasamu baiwa.

Sai lokacin deeni yaji wani kuzarin yazo masa Dan haka cikin , tsanyin murya tamkar may shirin zubda kwalla Deeni soma magana " kwarai first lov nayi kuskure guda daya narashin sanar min ki kafin zartar da komai amman na rokike kiyi hakuri.

Amman ta ya zuciyata zatayi sanadiyyar barinta cikin kunci da cuta alhalin nasan amanarta kika damka min acikin tafin hannuna' ya fadi haka tare duban tafin hannun nashi da kwayar idanushi
, indai akwai wanda na cuta to kece da bansanar miki da abinda tamin ba ,kafin na zartar da hukuncina akanta . amman ki gaya min me yakamata nayi byn na kamata dumu dumu da laifin zubar min da ciki har Sau biyu tare da shan maganin hana daukar ciki Sau ba iyaka .

Cikin zafin rai ya Kamo lips dinsa na kasa yasoma cizawa da karfi sakamakon hawayen dayaji yana kokarin son zubo masa.
" wani irin nauyin zuciyarsa tayi "yana ji yadda kirjinsa ke masa zafi da ciwo tamkar an daura masa dutse may shege nauyi a sama kirjinsa , .

, Da kyar yasamu yacigaba da magana. mutane na gudun tsautsayi amman ni na zauna da nawa tsautsayin batare dana sani ba 'bana da miradin danayi gida biyu amman nayi tunani indai tsautsayi ne ya hau kaina "to itama dole tsautsayi ya hau kanta .

,ni muradina gida daya ne kawai nake da bukata amman tunda itama ta cin nawa zuciya gobarar datayi sanadiyyar tarwatsa min zuciyarta tarabani da abinda nafi so a rayuwata ... to tabbas nima say na nemo may kashe min wannan wutar .
ta hanyar musguna mata .

Kada ka taba karya zuciyar mace kada ka taba ruguza iyali domin cika muradinki first lov NASURULDEENI dinki babu abinda bayawa Zeenat na jin dadin rayuwar aure "tare da sanyata cikin farinciki mara misaltuwa.

burina na kyautata mata.
' ta yadda zan samar da murmurshi da farinciki a fuskarta amman firt lov ki duba kiga da irin abinda ta saka min dashi.
gata nan tsaye ki tmbyeta ban kasance may adalci agareta ba A dan ,zaman da mukayi daita .'
ahankali ya mike tsaye hawaye dake makale a idanushi sukayi nasara zubowa batare daya shiryawa hakan ba.

shin na zalinceta ko daidai da rana daya ne.
ki tmbyeta first lov amman duk da haka idan kina ganin banyi daidai ba akan dukan danayi mata to zaki iya rama mata ki hukunta ni ta duk yadda kike so.

kece kikayi sanadiyyar kawo ni duniyar nan...
ko mayar dani lahira kike son yi "ahalin yanzu ba zance miki komai ba.

wlh Deeni dinki bazai taba cewa komai ba. Hawaye yacigaba da bin fuskarta .

km ba,zan miki wata jayayya ba abisa Ga hukunta ni da zakiyi ....

,jikin Ummi yayi maseefar sanyi dangane da jin Dukabinda dan nata ya zaiyana.

,jikinta a sanyaye takaraso kusa da tillon "Dan" nata tana kuka itama tare da dora hannuwanta duka ta riko fuskarsa dashi tana kallonsa.
wani irin matsanancin tausayi tattare da kaunar "Dan' nata ne taji Ya sake nunkuwa acikin zuciyata .
Yayinda kuka mai karfi ya kufce mata" from no where kawai ta rungumeshi ajikinta tana cigaba da kuka shima kukan yake ,yarona kayi hakuri.
" kukan ya isa haka kabar kuka kayiwa umminka uziri bisa Ga zarginta gareka.

amman duk da haka umminka na neman alfarma gareka ,na rokeka Dan Allah kada ka juyawa Zeenat baya ,ita din diyata ce halak malak duk duniya nan batada wata uwar data fini.
, ka cigaba da hakuri daita "inshallahu zata canza ,zata canza ,zan sata ta canza kaji yarona......
" Allah yayi maka albarka yadda kake faranta min ,kaima Ina maka addu'ar Allah yabaka ya'ya wayanda zasu maka fiyye da haka .

Zeenat ,dake tsaye taji hawayen tausayin su gabadata , nabin kuncinta, tasan hakika ta tafka babban kuskure a rayuwarta .
' tare da aikatawa kanta mugunta mafi muni da radadi wanda batasan tsawon lokacin dazata daina jin zafi da ciwon abinda ta aikatawa kanta. Da
wa yan nan bayin Allah ba .

Hakika ummi uwace guda a gurinta har da rabi .
,kodan ummi yaci ace tayi hakuri da juriya tabar cikin jikinta .
,gabadaya tausayinsu ne ya taru ya mamaye mata zuciyarta yayinda hawayen idanunta suka cigaba da zuba shaaaaaaa....................

,kuka ne mai karfi yaci karfinta tasa hannuta duka ta toshe bakinta dashi tare da rugawa da gudu ta haye saman up stairs din ummin tana gunjin kuka .

Kiyi hakuri first love da abinda zance inji cewar Deeni dan girman Allah first love kimin uziri na kara aure domin zama daga ni say Zeenat , zai haifar da mummunar damuwa wanda zaisa mudinga samun matsala daita a yadda nake jin zuciyata.

, uhmmmm Deeni bbu wani matsala ko damuwa daza'a km samu a tsakaninku muddin Ina raye ni kaina zan koma can gidan naku" nacigable da zama tare daku har sai Sanda naga zaman naku ya daidaita.

' maganar kara aure km bazan hannaka ba domin hanaka daidai yake . Dana shiga hakinka tunda kayi Niyya , say day kasani bazan taba barinka ka aure matar da nasan cewa zata fi Zeenat dina da komai ba arayuwa.

, say day idan ka amince zaka aure kasa Zeenat din.
Tukun zan amince da kara aurenka .

Km abisa sharadi duk yayan da matar za'ta haifa maka ,zasu zauna matsayin na Zeenat ne muddin rai matsawar ba nata tasamu ba .

dan haka Sai km tayi kasa kasa da muryata ta yadda bbu mai jinsu tayi masa magana .

Wanda yasa Deeni yin sororo kawai yana duban umminsa tare da nazarin maganarta tsab .
"exactly irin dai abinda abokinsa manir ya fada masa ne .
,say gashi itama umminsa tazo masa da irin maganar wanda shi sam a ranshi yake jin rashin yuwar yin haka .

,'ahankali ya samu guri ya koma ya zauna jagwab.. akan kujera yana may fidda numfashi sama sama.. domin maganar tayi maseefa girgizasa tare da daga masa hankali "har ma tana barazanar tarwatse masa zuciya.
,da kyar yasamu Ya daidaita' numfashinsa ya dawo normal.

,itama Ummi guri tasamu nan kusa dashi ta zauna tare da kamo tafin hannushi cikin nata Tana may nazarin yanayin daya shiga ,ka natsu ka kwantar min da hankalinka Deeni kada kasawa zuciyarka damuwa.
kasani a tashin hankali. wannan bawani abu bane so big kmr yadda ka dauka ,kusan anayin irin hakan Sosai a wannan duniyarta tamu .

Sake , dago rikitattun idanushi yayi yana kallon umminsa dasu take yaji wani ya tsigar masa a kanta kirjinsa ya rike gam Tare jin wani abu ya tsaya nasa a wuya yakasa kwakwarar motse ballanantana yace mata wani abu.

'Ahankali ' ummi ta numfasa sannan tacigaba maganarta irin wannan auren kawai zan iya yarje maka kayi.

,dan bazan taba yarde maka ka auro matar danasan zatafi Zeenat da komai ba, baya Ga kaskantacciya mara galihu ....
Chapter 50 · 0% Book details