← Book details Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 90

Sashe 67

Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ok karuwanci kika zo yimin a gida ko me?
, da sauri laraba tasoma bata hakuri .
dan Allah madam kiyi hakuri wlh bazan sake sanya su ba wannan mistake ne .
,da hannuta mdm Zeenat ta dakarta da ita ya isa bana son jin komai daga yanzu ma na kashe sa irin iriin wayandanan kaya muddin kina son zamanki ya daure dani. sannan ta kallo inda nablah tsaye har lokacin bataje inda ta aiketa ba ,tsawa ta buga mata ke kuma tsayuwar uban me kikewa mutane da bazaki wuce ba kin wani tsareni da shegun idanuki masu kama dana mayu.. bazaki wuce inda na aike ki ba.

Duk da nablah taji maseefar tsoron yadda taga Zeenat Tayi Amman hakan bai sa ta nuna ta fito da tsoronta filli ba a dake sannan km fuskarta a hade ta bar kitchen din hade da tausayawa kai banta.

Domin bata ganin laifi Zeenat sai nata domin ita takawo kanta da kanta cikin wannan maseefa.

Ta Dan tsaya kafin takarasa parlour mai gidan Tasa 'hijab dinta tana goge hawayen daya yasoma bin kuncinta dan iri irin abinda zeenat takeyi musu yana taba mata zuciya sosai .

'cikin sanyin jiki tasoma tafiya har ta iso parlour da mai gidan yake tare da bakinsa da sallamarta tashigo. muryata fal cike da tsoro da fargaba.

kallo daya DEENI yayi mata ya dauke idanunsa sai abokansa guda biyu ne suka amsa mata sallamar.

, ahankali cikin tafiyarta mai daukar hankalin ga duk wanda ya kalleta , ta karaso ciki sosai , ta tsugunna ta ajiye plastic din da cup's .

Banda kallon kasa ido bbu abinda DEENI yake mata ,'ahankali tare da natsuwa ta soma tsiyaya musu coffee .
cikin wata kwasatsiyar murya taji ance ke zaman me kikeyiwa mutane anan .... oya live this place now...

Gabanta ya dukan uku uku ,cikin tsananin tsoro hade da tashin hankali ta Mike tsaye , jikinta ,har rawa rawa yake tasoma kokarin daga kafafunta yayinda idanunta suka ciciko da hawaye tafff, ta bar parlour, daidai bakin kofar main parlour ta kusan ci karo da zeenat da sauri taja da baya ta tsaya, tana mai sa bayan hannuta tana goge hawayen dake bin fuskarta.

Zeenat ta tsaya kawai tana kallonta tare da nazarinta da kyau sannan tace kukan munafurcin uban me kikeyiwa mutane ,kmr ba aikin kudi kikazo yi ba tasoma maseefa tana zaginta .

, duk yadda nablah taso hadiya damuwar dake zuciyarta hakan yakasa samuwa , domin kuwa sabon Hawayen dake makale a idanunta ne suka samu nasarar zubowa .

, uhmmmm daman Sai Dana gaya ummi tabari a sallemiki Dan nasan bazaki iya tabukawa mutane komai Amman tace Sam...

Yanzu kukan iskanci me kikeyiwa mutane nablah ta girgirza kai tare da cewa bbu .

Zeenat ta tasoma kada kai cewa zama ayi komai din sannan ta Miko nablah wani karamin jug mai dauke suga tace ungo Ni ki kaiwa mijinta baiwar banza kawai.

,jikinta a sanyaye km badan ranta yaso ba ta sake koma parlour ...

byn ta fito ne ma abokinsa manir yace DEENI ina kasamo wannan fine bby din mai tsabar kyau gaskiya tamin kyau sosai .....

Take DEENI ya hade rai tamkar Wanda yaji wani mugun abu .. meye matsalarka daita ?

Manir yace yarinyar ce tamun kyau kawai , a fusace deeni yace bakowa bace facce house girl dina.

dayan abokin nasa ne yace gaskiya yarinyar tana da kyau sosai ba karya gashi Tayi maseefar ta haduwa dayawa .
irin wayan nan Ai nashiga mota ne da kewaye kasashen duniya .

A zafafe DEENI yace bafa nason iskanci nan naku idan abinda yakawoku kennan natashi nakama gabana .

Manir yayi dariya tare da cewa kai fa matsalar kennan to laifi ne dan mutun yaga abu ya yaba sai km yazama abin damuwa.
Fahad dake zaune yana nazarin deeni ya amshe da cewa kai meyasa DEENI kike yin irin haka ne ? Kacika daukar komai da zafe.

DEENI ya hassala dan takaici Dan Allah ni kun dameni da zance wata banza yarinyar ni wlh duk na Raina da ajinku wlh .
" da har kuka tsaya karewa wannan banzar yarinyar kallo " fahad yace idan kai makahone baka gani mu wlh muna Gani ,kuma dole mu yaba baiwar da Allah yayi .

, 'Ahankali ya ture document din dake zube gabansa ,Coffeen da nablah tasoma siyaya a cup, din yasa 'hannu ya dauka yasoma kurba ahankali ahankali tare da lumshe ritattun idanunshi .

Manir da fahad suka bishi da wani irin kallo ganin abinda yayi . yayinda manir ya cika da mamakin deeni .

Fahad yace mekake nufi yanzu da haka sai da hadeye wanda ke bakinshi sannan yace ga abinda nake nufi nan kuwa , kowa ya yakama gabansa.

Manir yayi murmushi sannan yace to munji amman zai siyayyamu coffee to , juyar da fuskasa yayi wani gefen sannan yace ai duk kuna da 'hannu ,idan baku tashi Sha ba ,kubarshi .

murmushin fahad ya sake yi yace da alamun rashin mutunci kawai kake son yimana .

DEENI ya daga kafadunsa, duka a alamun I don't care .
nan dai suka mai da abun wasa atsakaninsu suka cigaba dayin abinda ya kawo su byn sungama ne DEENI ya Mike yace yana zuwa .

Zuwa yayi ya canza kayan jikinsa zuwa kanan kaya sai kamshi mat Hamilton 27 yake zubawa part din ummi yashiga yana kiran sunanta .. first lov.. were are you .

jin shiru bata amsa bane yasashi kutsa kansa cikin bedroom dinta kai tsaye batare da yayi tunanin wani abu .

Ita kuwa dake zaune tana jerawa ummi kayanta da mai wakin yakawo dazu a Waldrop ta zabura ta Mike tsaye da sauri, duk ilaihi jikinta bbu inda Bai dauki rawa ba saboda tsabar tsoron muryar data jiyo.

Sosai kamshin turarensa ke kusanto dakin alamun yana gab da shigowa . gashi bbu komai ajikinta daga ita sai daguwar riga mai 'hannu harmless cikin sauri sauri ta soma neman hijab dinta .
data cire amman tarasa inda ta ,ajiye .

har yashigo dakin , cak ta tsaya ta kasa kwakwarar motse ,jin tsayuwarsa jingine da kofa yasa take kirjinta ya buga yayinda zuciyata tashiga ..
aikin da tasaba a duk sanda , ta kasance tare da DEENI.

shima tsaye cak yana Kare mata kallo tsab wanda in ba lura mutun yayi da kyau ba.

,ba za'ice ita yake bi da wannan mayataccen kallo ba .
shida kansa yasan in yace yarinyar batayi ba , tabbas karya yake km son ranshi ya fada .

ahankali yakaraso dakin sosai yana sake kiran sunna ummi . kainta a sunkuye a kasa yayinda zuciyata ke wani irin bugawa da sauri cikin siririyar muryata mai cike da in inna ... tace ta.. tana.. bathroom ...

Bai ma tsaya wani sararonta ba ballanantana ya nuna alamun yaji abinda tace ba , tunda shima yaji alamun haka.
juya kawai yayi yabar dakin cikin takunsa ,na tsanyaye namiji .

Numfashi ta sauke tana may sa dukka 'hannuna ta dafe kirjinta dashi tare da sauke ajiye zuciya.

wayyo Allah wannan mutumin ba dai frigita mutane ba .
numfashi ta dinga fitarwa 'ahankali 'ahankali har ta dawo normal .km Sai a lokacin taga hijab din ta washe a gefen 'tsabar rudewa ce tasa takasa Gani.

fitar shi bai fi da minti uku ba ummi tafito tanawa nablah sannu da aiki sannan tasamu waje ta zauna, tana dan Jan nabla da hira , itama dai ba laifi takan dan saki jikinta ummi dan tafi zeenat sau dubu har aka kira sallah suna tare da ummi dan dakin tadawo yanxun saboda aikin da za'a yi Wanda ya hada har da dakin nablah.

Mikewa tayi nablah Tayi tare cewa ummi Ina son naje nayi sallah .

murmushin ummi Tayi haba nablah yanzu sallah ma sai kin tambaya ,ummi girgiza kawai tare da cewa ,jeki kawai kiyi sallahrki kinji ..

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Page 65

Byn ta idar da sallah magariba,tana zaune akan praymat , tacigaba dayin lazimin daya zame mata jiki .

har sanda taji kiran sallar isha,i daga masallaci dake cikin gidan sannan ta mike ta gabatar da isha'i tayi addu'a sosai .

abinda ke karasa ummi jin kaunar yarinyar nashiga ranta kennan, ita din mai yawan ibada ce ko kadan bata wasa da lokacin sallah.
ahankali nablah ta mike tsaye tana nade praymat . Gaban ya fadi rasssssss sakamakon yiyo sautin muryasa yana yashigowa hade da sallama
yayinda mdm zeenat ke biye dashi tamkar wata bindi.
waje yasamu kusa da umminsa ya zauna yana zuba mata shagwaba tamkar wani karamin yaro .

gabadaya kamshin turarensa yaci koina dakin ummi ta dago idanunta ta kalleshi da kyau tana harararsa wanda kallo daya zakayiwa ummi " ka zagane Hararar tsansar soyayyace irin ta tsakanin uwa da "da" .

Shima kallon umminsa yake yana murmushi tare karyar da kai , ummi ta dubi Zeenat kalli mijinki da kyau sai Naga kmr ya rami yau ko idanuna ne .

Zeenat Tayi murmushi sannan tace bbu wata rama da yayi ,idanunki ne kawai ke ganin hakan.

DEENI ya zabgawa Zeenat harara tare da cewa , rabu daita first love ai bazataga ramar danayi ba , sbd basanin yadda ake kula da miji Tayi ba , amman gabadaya yau a gajiye nike ,ya fadi Haka yaba narke fuska.
abin ma har yaso bawa nablah dariya , Amman ta share kawai saboda ba muhalin yinta bane.

Ummi ta sake duban dan nata da kyau tana murmushin tace kai.. Sam bakasan ka girma ba wlh , kullum shagwaba shagwaba shagwaba tamkar yau aka haifeka ,bazama ka dan rage, ka barwa ya'yanka ba .
Chapter 67 · 0% Book details