← Book details Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 90

Sashe 59

Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nablah kina ganin masu kudin nan iyayi ne dasu gashi mafi yawancinsu "basuson shishigi dayawan kallo.
ki zauna lfy da duk mutane gidan, kitsaya a matsayin ki ,abinda ya kai ki shi zakiyi dan Allah nablah karkisa naji kunya a in da zan kai ki kinji Yar kanwata ...

' Ahankali nablah ta dawo daga tunanin data tafi na wucin gadi tare da dago shanyayun idanunta tana sake kallon matar data shigo saboda jin sautin muryarta mai cike da tsabar iyaye wanda dagani har da iskanci aciki .

Ummi kina ganin yarinyar nan kuwa zata iya aikin gidan nan ? Sai naga kmr tayi karama
Amman dai ...sai km tayi shr ta Mike tsaye tare da cewa .
ummi zo muyi wata magana dake.

Ba musu ummi tabi bayanta byn sunshiga wani daki dake cikin dakunan dake kasa ne , Zeenat ta sauke ajiyar zuciya sannan tace
,
,Gsky ummi ni fa kwata kwata yarinyar nan banji ta kwanta min a rai ba haka km tunda ake kawo masu aiki gidan nan, ban taba jin yarinyar da naji tsanarta farar daya a zuciyarta ba kmr ta ,Dan haka ummi kibari suyi tafiyarsu kawai .

Ni asona ma , da abar laraba , kawai ta isa ba sai an karo wata ba ,tunda tana yin komai yadda yakamata.

,ummi ta girgiza kai byn tagama jin Zeenat din tsaf..,ni km kinga Ina ganin yarinyar naji ta kwanta min wlh.
kema kiyi kokarin ta miki tamkar yadda naji araina kinji diyata , ba'a saurin tsanar mutun , km ,da alamun akwai natsuwa a tattare da yarinyar .
Zeenat tayi shr tare da kwabe baki kawai takasa sake furta komai ,.
Har Suka dawo parlour.

tasan tunda yarinyar tayiwa ummi magana takare .

ummi ta zauna tare da sake duban inda nablah da Aunty Salmah ke zaune , sai data numfasa sannan tasoma magana kmr haka gsky yarinyar tayi sai dai Kuma ajira zuwan may gidan muji me zai ce akanta , idan Tayi masa zakiji ni a waya ,idan km akasin haka ya faru ,Shima zakiji .
, nablah ta runtse idanunta kirjinta ya shiga bugawa jin sai wani yaganta sannan za,a dauketa aiki .
bayan duk wannan kallon kurulla da'aka tasa gaba da shi .
,nan gaba km sai an sake kawo mata sabon rainin hankali .
na hada da Kato ya ganita.
, tsuke dan karamin bakinta tayi tana mai jan tsaki acikin xuciyarta .

Aunty Salmah tace bbu komai hjy duk yadda kika yi daidai ne 'ahankali ummi ta sauke ajiyer zuciya .. tare da saki murmushi jin dadi.
, Sannan tace baku ci komai ba.
aunty Salmah tayi murmushi itama sannan tasa hannu ta dauki malt ta bude Tasha kadan ta,ajiye amman ita nablah kasha komai tayi Dan bataji zata iya sakawa cikinta komai ba balle ruwa gabadaya hankalinta a tashe yake da jin furucin ummi na karshe .

sake fuskantar Aunty Salmah da kyau ummi tayi , akwai check up da',ake wa sabbin ma,aikatamu saboda sanin ingancin lafiyar su ,so itama za'a mata da fatan hakan bazai zama da wata damuwa ba.

" Aunty salma tace wannan ba wata matsala bace Dan na yarda da sis na ,💯Kuma ina da tabbacin komai normal zaku gani inshallahu ...km duk aikin dakike so zata miki Dan gwanace gurin iya aiki bbu aikin da zai gagareta ummi tayi murmushi tare da cewa Nagode sosai sannan ta kalli nablah dake zaune a gefe shr sai faman wasa take da yatsun hannuta.

kina jin abinda yaayarki tace ?
,nablah ta dagawa ummi kai alamun taji ,ummi tace A'a nifa bana son kyaliyya ki bude baki kmr yadda na miki ,sannan ta dubi aunty Salmah ko bata magana ne naga tunda kuka zo batace komai ba?.

Aunty tayi murmushi ,Tana yi .
,kiyi magana mana kinjin mutane , tare da cewa Killa har da rashin sabon,dabatayi daku bane .
amman tana da saurin sabo da mutane da son yara .
Ummi tace mayye sunanta ,aunty tace nablah ..sai da ummi ta sake maimaita sunan a kasan ranta wanda hatta zeenat dake zaune sai da ta dan juyo ta sake kallon inda nablah ke zaune a rakube ,ummi tacigaba nablah barkanki da zuwa gidana ... gidan dana, amana ne a hannuki zaki zauna tare damu na tsawon shekara biyar kmr yadda auntyki tasanar min a waya ,wai kince inkin zo bazaki koma ba sai kinyi wayannan shekaru dai kin dinga zuwa dubasu time to time to Dan Allah ki natsu duk abinda ban baki ba karkisa hannu ki dauka in km kina bukatar wani abu kisanar dani ko wannan ummi ta nuna mata Zeenat da yatsanta, zata baki matsawar baifi karfinta ba yanzu dai za,a kaiki ki huta kafin zuwa gobe zata Nuna miki aikin dazaki dinga yiwa diyata km matar dana wacce kike Gani zaune a gabanki ,kin iya abinci ? Da kyar nablah ta iya bude baki cike da sanyin jiki tace eh...

Itama aunty Salmah takara da cewa ta iya Sosai amman bansani ba ko ta iya irin na yan gayu ba .
ummi ta sake yin murmushi kawai to shikennan badamuwa koda bata iya ba.
da zarar tayiwa mai gidan za'a dinga koya mata har ta iya .abinda yasa kika ji Ina cewa haka mai gidan ne akwai shi da kyamkyami shiyasa .

Aunty Salmah tace bbu komai ai hakan yana da kyau , ummi tacigaba gidan nan sama da kasa ne aikin share share da girki sai abinda baza a rasa ba .

aunty Salmah tace abu na karshe da zance kafin na wuce Bai wuce kuyi hakuri da nablah domin yarinyace karama da bata wuce shabakwai ba koda zatayi ba daidai ba a tsawata mata dan bata taba yin aiki ba wannan shine karo na farko duk da nasan bata da rawar kai ummi tayi shr Tana sauraron aunty Salmah tare da addu'ar Allah Yasa oga DEENI yayi maraba da wannan matashiyar yarinya .
dan ita kanta yarinya ta kwanta mata fiyye da tunanin mai karatu uwa uba natsuwa da take Gani a tattare da ita .

Aunty Salmah ta juyo tana kallon nablah kin san ban kawo ki aikin nan ba sai da amincewarki dan haka na rokeki kiyi musu duk yadda suke so kinji takarasa fadar haka tana mai kamo hannun nablah cikin nata tamkar zata zubda hawaye ,sai duk jikin nablah ya sake yin sanyi, idanunta suka ciciko da Hawaye data dade tana boyesu take ta mayar dasu dan batason aunty,ta tagane yanayin datake ciki dan tabbas aunty Salmah naganin hawayenta sai tayi kuka itama .dan tasan ko a yanzu da take magana ma dauriya ce kawai da karfin hali irin nata.

Aunty Salmah ta kalli ummi tana mai cigaba da yi mata bayanin ,ta zabi yin aikin nan ne sbd tana son cigaba da karatunta, dan tun 2016 tayi weac yayinda tayi jamb dinta a ,2017 . ummi ta katseta ta hanyar tmbyeta kanwarki ce jini ?
Aunty ta bata amsa da uwarmu daya ubanmu daya itace autarmu a mata ummi tace Ga kama nan kam.
sai dai tafiki kyau sosai aunty tayi murmushi sannan tace saka makamakon abubuwa da suka mana yawa ne yasa ta gwammaci tazo tayi aiki dan wata uku kennan dayin walimarta, Shima da kyar da bugabuga Allah Ya rufa asiri muka biya mata kudin . shiyasa data takawo wannan tunanin muka amince.
in bancin haka baza mu taba amince ba sbd zuciyarmu ce nablah gabadaya ilahirin Yan gidan mu muna mugun son nablah koda zamu taho har kuka mahaifiyarmu tayi.
haka ma yan gidan mu kaf. ummi ta jinjina kai yayinda zuciyarta Ta motsa da tausayinsu .

Ummi tace karki damu Salmah da ai na kowa sannan ta sake duban inda nablah ke rakube tamkar tana gaban sukarta yayinda Zeenat ke zaune haushi tamkar ta hadiye zuciya haka dinga ji .

Ummi tace wani school kike son zuwa aunt Salmah tayi saurin cewa BUK dan tasan halin nablah da sanyi tsiya .

ummi ta sake tmby wani course Shima aunty ce tabada amsa da accounting take son yi sai dai rashin mathematics yasa nace ta canza ....

Ummi takira sunan Salmah .... ki barta ta amsa min da kanta man ai ita tafi sanin abinda yakamata daita.

Sannan ,ummi ta tattara hankalinta kacukan akan nablah tare da zuba mata idanunta dan haka kawai taji yarinyar tayi mugun shiga ranta .
uhm nablah me kike son karanta a BUK nan dai tayiwa ummi bayanin kmr yadda aunty,ta tace dan bazata so ta fadi wani abu.
da daban wanda zai yi disgrace din auntyta. ummi ta numfasa ,tace sai maganar salary nawa za'a biyata Aunty tace mudai bamu san kan yadda abun yake ba ,Ku kukasan yadda kuke biya masu aiki tana gama fadar haka taja bakinta tayi shr.

ummi tace eh to kmr dai shafa data wuce muna bata dubu talatin a wata .
Amman ita wannan bazan iya cewa Ga iya abinda za'a bata ba sai mai gidan ya dawo tukun Dan ,ba mamaki idan Tayi ,zai iya bata fiyye da hakan .Sai km Yadda bada kudin zai kasance za'a barsu ne anan ko km za'a rinka bata a hannuta sbd koda zata bukaci wanni abu.
,dan kudin masu aikin gidannan a gurina suke km duk lokacin suka bukaci yin wani abu dashi nakan basu abunsu .

Aunty Salmah tayi saurin cewa A'a account dina za'a dinga turowa ummi ta sake cewa A'a Salmah kibarta ta fadi yadda take so ayi sbd hakinta ne aunty Salmah taja bakinta tayi shr .

ummi ta juyo suna fuskartan juna da nablah tace ya nablah me kika ce ,a turawa Salmah ne ko zaki bude account naki ?

Nablah ta girgiza kai a tura a account din auntyna kawai , dukkansu dariya sukayi har aunty amman Banda Zeenat Sai ma tsaki data ja tana cika tana batsewa.

Ummi tace gsky kun birgeni dagani akwai fahimtar juna a family dinku .
, shikennan kituromin account number dinki ,yanzu dai kinga wata yayi rabi Dan haka duk abinda mai gidan yabada zaki gani ta account .
Sannan tace Zeenat taje takawowa aunty Salmah kudin mota .
Chapter 59 · 0% Book details