← Book details Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 90

Sashe 49

Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inna tacigaba ko baka maidaita jikata ba zata samu wanda yafi kyau da kudi da komai "amman wlh tunda kagama moremata jiki Sai ka maidaita gidanka.
ban da ma kaddarar aure mai jikata zatayi da kai tsami gaye da kai da tsayi awa bishiya .

abin dariya abin takaici a wulakanci deeni ya dinga kallon inna Yana jin wani irin zafi a kirjinsa tamkar zuciyarsa zata buga.

a zafafe Yace to baza'a maidaita ba say kiyi duk abinda zakiyi.

,ni kake cewa bazaka maidaita ba , zubairu kana jinshi ko to wlh bada ni kake ba da wannan ta zaune kake tashiga nuna Ummi da hannu ,mara kunya yaro kawai may dan karan taurin kai awa na mutane farko .

Deeni ya bude baki big dady ya katse shi ta hanyar buga masa tsawa.
" mahaifiyar tamu kake kokarin yin sa,insa daita ,kar ka sake na sake jin bakin ka kaji dai nagaya maka .

Dan Allah inna kiyi hakuri Ya isa haka "

Inna tace bai isa ba zubairu , nace bai isa ba kai ya kalli tsabar idanunka ya gayamaka haka ko yagawa uwarsa haka ,say ni daya raina ko dan haka ko yamayar daita ko km wlh koto ce zata rabamu dashi tare da fashewa da wani mugun kuka ,wlh Allah yaisa tsakaninmu dakai deeni bamu taba yafe maka ba .fk yatashi ya mike dan takaici inna ya bar parlour,n .

Da kyar big Dady yasamu ya rarrashi inna . ranshi a bace Yace yanzu yanzu ka maida matarka inji cewar big dady .

deeni Yayi shr Yana kallonsa Yana huci .
inna tace bakaji magana ake maka ba" kinbabbe kawai Sai faman huci kake kmr ,zaka hadiye mutane.
" deeni ya tsareta da rikitattun idanushin kawai zafi zuciyarsa da kirjinsa suke masa .haushi da takaicin inna suka taru suka mamaye masa zuciya.

inna tace daina kallona da wayan nan mugayen idanun naka masu kama dana mage , munafiki kawai.

Zeenat ce Sai Sai ta koma gidanka ko kaki ko kaso uhmmmm.
zeenat dai kanta na kasa Sai risgar kuka take tana addu'ar aranta kar Allah Yasa deeni Yace ya maidata.
duk da tsananin son da take masa bazata iya juri zama dashi ba cikin wannan situation din ba.
yayinda hawaye ke cigaba da bin kuncinta .

Wai wasa ake dakai ne ka tsai da mutane kana bata mana lokacin kowaye sa,anka anan inji wani kanin mahaifin deeni.
shi kuwa big dady tunda yayi maganar karshe bai sake cewa komai ba Sai idanu daya zuwaba deeni Yana kallonsa ko kifta ido baiyi .

'Ahankali deeni yake kallon duk ilahirin wayan dake zaune a parlour kaf dinsu iyayensa ne idan aka dauke fk wanda shima sako yashigo kawowa ya iske ana maganar ,'ahankali yacigaba da kallonsu idanunshi suka fada cikin na umminsa wacce gabadaya tazamo kalar tausayi, wasu abubuwa yake hangowa daga cikin idannun umminsa masu kama da rarrashi da ban hakuri .wanda suke nine a bukace take da son ya aikata abinda akace masa Yayi.

,ahakali ya mai da idanunshi kasa tare da sauke ajiyar zuciya. muryasa can kasa kasa Yace na ...mai daita...

Inna taja tsaki tare da Mikewa tsaye munafiki kawai ' daman can kana sonta iskanci ne kawai irin na mai shayi ya tsaida uwarsa ya tsai fatan shayi , tsami gaye kawai ..
Deeni ya dago rikitattun idanushin suka hada ido da Ummi tayi masa gargadi da idanunta alamun kar ya sake Yace Komai

Bye bye bye until after sallah missing u guys

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

*Assalamu alaikum warahmatul Allah inawa dinbin masoya wannan littafin barka da sallah da fatan kunyi sallah lfy Allah ya karbi Ibadunmu da mukayu cikin Ramadan Allah Yasa muna cikin bayin da Allah ya, enta daga wuta zuwa jannatul firdaus Ameen ,kmr yadda nace zan cigaba da type din wannan labarin nawa byn sallah, to a yau ne alkawari Allah yacika Allah ya nuna mana lokaci ,hakika may hankali da tunani ne kadai zai Gane yadda duniya ke gudu, Allah Yasa mudace yabamu ikon cikawa da kyau da imani ,km Allah yabamu ikon aikata ayyukan alkhari*

Page 54

'Ahankali Deeni ya dauke rikitattun idanushin daga cikin idanun umminsa ya maidasu kan inna dake tsaye tana fama , babatu da sambatu iri iri 'km duk cikin taron mutane dake zaune a parlour bbu wanda yayi yunkurin dakatar daita daga maganganu da take .

zuciyar Deeni cinkushe da haushi hade da takaicin inna" bakinciki ganinta ke sake nunkuwa a kasan ransa yayinda yashiga da zuciyarsa wani irin zafi da suya zuciyarsa ke yi.
" so yake ya murje idanunshi Tare da cire kunyar jamar dake zaune a gurin, sannan ya zage kunjinsa ya zabga mata rashin mutunci fiyye da irin wanda ta iya .
,amman Ina...tuni idanun umminsa dake yawo a kansa" yasa ya kasa aiwatar da komai sakamakon gargadin dinsa datake ta hanyar kwayar idanunta .

dan haka daya rasa yadda zaiyi ya fanshe tarin wulakancin inna gareshi,sai kawai ya shiga aikawa inna da wani irin mugun Kallo may hade da harara .

Wanda yasa ,ita kanta inna dake tsaye har lokacin sake jin haushin DEENI da takaicin irin kallon kaskancin da wulakancin dayake aiko mata dashi .

"Km hakan yayi sanadiyyar kara hassalata , dan haka a tsawace Tace ni daina kallona ,ka wani tsareni da wa'yan nan mugayen idanun naka masu kama dana mage , kana aikomin da kallon wulakancin to bada ni kake da wannan uwartaka ta zaune kake... ehee.. takarasa fadar haka tana may jan mugun tsaki a fili tare da soma kokari kamo hannun Zeenat .

Ke tashi mu tafi , can sashina ko kya samu ki maida jikinki ki murmure daga wannan bakar ramar da kikayi " inna tasoma kokarin mikar daita Zeenat tsaye .
Yayinda Zeenat din km taki mikewa Sai ma sake cure jikinta da tayi gurin guda alamun babu inda zata .

,au bazaki mike mu tafi can gurina ba ,kinfi son ki zauna inda za'a dinga miki izaya da tsotse miki jinin jiki.
Dan zama da wannan mugun azalumin kadai ya,isa yasa jinin jikinki ya kafe batare kowa yasani ba "ni tashi mutafi .

,juyin duniya nan inna tayi da Zeenat kan ta tashi su tafi can part dinta " amman kememe Zeenat taki tashi .
ganin haka yasa inna sake tunzura, ta cigaba da tsayuwarta tare da surfa masu maseefa iri iri km har lokacin bbu wanda yaiya cewa komai

big dady ne "ya dan dago idanushi yana duban sashin da inna ke tsaye Tana surfa maseefa ,ya xuba mata kawai domin shi kansa big Dady rasa me zai cewa inna yayi...

' kusan minti goma ya dauka Yana kallonta batare da yayi yunkurin dakatar daita ko ce mata wani abu ba ' kafin daga baya ' ya gyara zamansa Tare da numfasawa. cikin tsantsar ladabi da laushin murya yasoma magana, Dan Allah inna kiyi hakuri ki tafiyarki abinki "tunda yarinyar nan Ta nuna bazata biki ba.

, Say da inna ta tabe bakinta tukun sannan tace "yo Ai ka kace min nayi tafiyata man " tunda fadeela da danta sunfini daraja da kima a idanunku" duk irin wulakanta min jika da wannan banza yaron nata yayi baku Gani ba Sai na laifin zakugani .

,big dady sam Bai damu ko jin mamakin abinda inna tace ba, dan yasan kadan daga cikin aikinta. domin zata iya fadar fiyye da abinda yafi haka ma.

Dan haka big Dady Bai damu da abinda tace ba ya kara kwantar da murya cike da girmamawa ya sake cewa , Dan girma Allah inna kiyi hakuri kiyi tafiyarki tare da yiwa yaran nan fatar alkhari a rayuwar aurensu tunda komai yazo da sauki saki daya ne yayi mata . Km ya maidaita .
Duk ma da abinda Deeni yayi mata Ai bai laifi bane tunda ita tajawa kanta .

,inna ta katse big Dady Ta hanyar daga masa hannuta,dakata... ya isa haka karka cika min kunne" naji zan tafi amman wlh wlh kaji na rantse ,to kagayawa wannan gantalallan "dan 'naka yakiyaye ni" kar ya km yin gigin kai hannushi da sunan sake taba min lafiyar jikata.

Domin ita ba jakar gidan ubansa bace .
Big Dady yace shikennan kiyi hakuri ki yi tafiyarki zan gaya masa .

Inna Tace da dai yafi dan wlh idan ya km yunkurin kai hannushi jikinta ba yarda zanyi ba .

, da kyar da Allah da rarrashi, big Dady da sauran mutane dake zaune a parlour aka samu inna ta fice daga parlour tana zage zage.

'ahankali big Dady Ya sake numfasawa tare da duban inda Deeni ke zaune ya hade fuska tamkar hadari suna fuskartar juna ,tsawon lokaci big Dady ya dauka Yana dubansa ,kafin daga baya yayi masa fada sosai akan irin hukuncin daya dauka akan Zeenat din sannan daga karshe ya bige dayi masu nasiha mai shiga jiki shi da Zeenat ,akan su taru su zauna lfy.

Yace deeni Kayi hakuri akan laifin da Zeenat ta aikata a gareka, hakika munsa bata kyauta ba amman ka dauka daman can haka Allah ya rubuto cikin data zubar maka ba masu rayuwa bane a doron kasa.

Dan haka kayi hakuri ku zauna lfy hakan kadai shine muradinmu da km kwanciyar hankalinmu dana umminku gabadayan .

Sauran en'uwa ma kowa ya tofa albarka bakinsa sannan
,Jiki a sanyaye Deeni yace yaji tare da yin musu godeya , duk da ran nan nashi , in yayi dubu to a jagule yake .
da kyar ya samu ya kokarta ya mike tsaye dan kokarin barin parlour har yakai daidai bakin kofar fita .

" cak yaja ya tsaya jikinsa har wani shake yayi sakamakon jin sautin muryar umminsa mafi soyuwa a zuciyarsa .
' ,kaje gida kajirani gani nan zuwa yanzu, abubuwa dayawa suka zo masa tare da tsaya masa a rai .
jin yadda ummi tayi maganar kadai yaisa yasan yadda ranta yayi kololuwar bace ..
dan gane da abubuwan dake faruwa a atsakaninsa da Zeenat kasa cewa komai yayi sai , kansa kawai daya iya daga mata alamun yaji 'sannan Yakarasa barin parlour .
Chapter 49 · 0% Book details