← Book details Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 90

Sashe 20

Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da misalin karfe takwas na dare fk ya km samu shemah da zance shi fa ba zai iya wani hakura daita ba kawai tayi hakuri ta amincewa da bukatar domin shi yana matukar son ta km aurenta yake son yi ,tace dan Allah yaya kayi hakuri wlh da bbu wanda nake so ne ,zan iya soka dan kaima baka rasa komai da zankika ba , kadai yi hakuri kawai .
al'amarin dayayi matukar dagawa fk hankali kennan ,yayi shr kawai yana kallon yanayinta tare da nazarin kalamanta masu kokarin tarwatsa masa zuciyar rasa yadda zanyi daita yayi can dabara tazo masa,ya tsareta da idanunshi Yace ke banso iskanci da rainin hankali fa ni zaki cewa kina da wanda zaki kike so byn Banga uban da kike saurara ba ,lafazinsa yayi mugun bata mata rai dan haka a ranta abace tace to dole ne Sai na aurenka kaje Kanemi wata mana ko ana soyayya dole ? ta juya a fusace zata bar guri ,ya fizgota hannuta , gabadayanta ta fado jikinsa , idanun ta zaro a tsorace, ,take taji wani irin faduwar gaba , .
Hannuwansa dukka yasa rungumeta tsam ajikinsa yana sauke ajiyar zuciya daidai kunneta ya kai bakinsa Yace maimaita abinda kikace Ina jinki cikin tsiwa tace wannan wani irin iskanci dazaka wani rungume mutun ? Ok nine ma nake miki iskanci ?
Uhmmmm fa shemah karkibari muyi haka dake zaki amince ta girma da arziki ne ko km na jawo soyayyata ta karfin tsiya ,.batare da na wahalar da kaina ba muryarta na rawa tace anki a amince da soyayyarka .
ko ana so dole ne ?
, dan Allah ni kasake ni ,ya zuba mata manyan idanunshi kawai ,yasoma yawo da hannushi a jikinta gabadaya jikinta ya dauki kirma abinda bai taba faruwa daita ba kennan tunda take arayuwar ta ,wai namiji ya rabi jikinta har takaita ga runguma ,dan takaici ma batasan sanda , kwalla ta cicciko a idanunta ba , hawaye yaga yana silalowa daga idanunta ahankali ya sauke ajiyar zuciya, ya dan sausauta rungumar da yayi mata yasa yatsansa ya dangwalo hawayen dake bin fuskarta yana kallo Yace duk wannan kukan akan nace Ina sonki ne kike zubda hawayen ki?
,tayi shr taki cewa komai dan haushi ji tayi kmr ta daura hannuta akanta ta kurma ihu , ahankali ya sake maida ita jikinsa ya rungumeta yana shinshina wuyanta daidai nan Sai ga big dady dake dawo daga masallaci , a tsorace yake binsu da kallo cike da mamaki da alajabi abinda yagani , meke shirin faruwa km yau acikin zuri'arsu ,fk yacigaba manneta da jikinsa yana rarrashi ta amincewa aurensa , dagowar nan da zai lyi karaf idanunsa suka sauka kan big dady dake tsaye duk da duhu ne hakan bai hana gareshi ba gabansa yaji yayi muguwar faduwa jikinsa ya dauki kirma duk da ya tsorata Amman yaji dadi Ganin da big dady yayi musu ,yasan hakan zai sa a aura masa shemah batare da bata lokaci ba tsabar frigice yasa yakasa rabata da jikinsa gabadaya jikinsu rawa yake shemah da batasan wainar da'ake tuyawa ba sake lafewa tayi ajikinsa saboda irin rungumar dayayi mata ba wacce zata iya kwacewa bace har big dady ya wuce su a gurin shemah batasa big dady yagansu , ahankali fk yasoma rabata da jikinsa har zuwa yanzu hawaye bai daina bin fuskarta ba hannuta yakamo yasoma tafiya ita kum tana biye dashi bbu wanda ya iya cewa dan'uwansa komai har yakawo part dinsu yaja ya tsaya ahankali Yace shemah kiyi hakuri dan Allah kibar kuka ba nufi na kuraki ba Ina matukar kaunarki bansan lokacin dana fara sonki ba Amman zan baki lokacin kiyi tunani akai ,zan dawo zuwa jibi yana gama fadar haka ya juya da kyar yake iya daga kafafunsa tsabar frigice da nauyin da suka masa zuciyarsa tamkar zata buga , dan fargaba haduwarsu da big dady shi yasan ba makuwa tunda har big dady yagansu aure kmr anyi an gama Amman kunya fa ,har ya iso part dinsu wanda kusan nan samari suke zaune wayanda basuyi aure ,

Itama tana shiga dakisu ta wuce kai tsaye tana kuka , mamanta dake zaune a parlour tace ke lafiyarki Amman ko juyo batayi ba fadawa tayi kan gado tana risgar kuka to meye yaya faruk yake nufi daya sonta alhalin ita DEENi take mutuwar so ..... Dan haka bata taba aurensa ba ,tunawa datayi ba'a musu auren dole a family dinsu sai sun amince da juna yasa taji hankalinta ya kwanta Amman gabadaya jikinta yayi bala'in sanyi haka ta wuni a daki batare data sake fita ko parlour ba ,fk bai dawo ba kmr yadda Yace mata kusan sati tsakani shiyasa tayi tunanin ko yayi wa kansa fada ne ya hakura daita dan haka ta sake abinta kwasam Sai gashi a wani daren lahadi byn tagaishi a dage ,yayi murmushi yace yazo ne akan maganar su ,a fusace tace wata magana kennan i tough mun gama da wannan zance tunda nace ban sonka , Yace haka kika ce ,tace eh ko dole soyyaya dakai ,Yace uhmm Amman dolenki ki aureni ya wuce batare da damuwa ,

DEENi yasamu yaya mahamud yayi masa bayanin shi kuma ya samu big dady da zance tsohon yaji dadi Sosai jin sun hada kansu yace Shikenan bbu damu zai tuntubi yarinyan tukun asan abinyi .

Nan dai aka saka ranar aure tare da yanka sadaki yaya mahamud ne yayi komai ko sisin Kobo bata fita daga aljihun ogo deeni ba ko mahaifin zeenat yayi murna sosai da jin DEENi ne zai aure diyarsa

Anyaka sadaki da dukiyar aure naira duba dari biyar wanda duk a aljihun yaya ma

💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Page 23-24

Ni dan girman Allah kabarni na wuce tun kafin laifina ya Karu.

,Murmushi karfin hali kawai yayi ,tare da nuna mata hanya da hannushi alamun ta wuce din.

, kasa tafiya tayi " sakamakon idanushi da taji yana mata yawo a gangar ajikinta . Gabadaya taji tamkar ya daureta ne .
takasa kwakwaran motsi" jikinta yayi bala'in yin sanyi.
,taji ina ma zuciyarta na da yanci da bata kamu da soyayyayar deeni ba.

Da bbu shakka zata iya hakura da kamil tunda shima yana da nashi kyawun daidai gwargwado .

Yayi shr kawai yana kallonta" kaunarta ce ke tasomasa tare da nukurkusan zuciyarsa.
,ya dinga jin tamkar ya halaka kanshi lokacin daya tsinci idanun deeni akan su.
ya dinga kallonta "yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa " da gske dai yana shirin yarasata kennan ,rashima na har abada.
km ta haramta ta zama matarsa wani irin zugi zuciyarsa keyi ahankali
Yakira sunanta..Zeenat kina son deeni sosai ko ? Cikin sanyi
ta dago kanunun idanunta ta kalleshi dasu "sannan tace , wannan wace irin tmby ce ? Yace amsa kawai nake bukata ,tace to bana son shi shikennan.
Karkimin karya mana Kina son shi kalli...kalli yadda yanayinki ya canza jikinki har rawa yake saboda kin ganshi .
ya tabbata kennan baki sona ,rainamin hankali kawai kika dinyi .

A fusace Zeenat tace Nifa karka zageni da laifi da bansan na aikata ba. mgnr ina sonshi ko bana sonshi ma duk bata taso ba .

kai kanka kasan bantaba amsa maka da Ina sonka ba.
ballanantana kace yaudararka nayi ka dai yi hakuri Allah ya hada kowa da rabonsa , yace ok yanzun duk tarin son da na miki yazama tarihi kennan ?
Ta zuba mishi ido kawai dan tasan duk abinda zata gaya masa ahalin yanzu ba fahinmta zai yi ba shiyasa tayi shr taki cewa komai
Ahankali Ya girgiza kanshi kawai batare da sake cewa mata komai ba ya juya yasoma tafiya.

, Tayi jim jikinta ya mata tsanyi ,bata ji dadin yadda taga reaction dinsa ba .
tasan kwata kwata bata kyautawa masa ba. Amman ba yadda taiya da zuciyarta " DEENi shine muradin ranta .
raba zuciyarta dashi tamkar barazana ce ga rayuwarta.
Duk da taji ba dadi ba hakan bai sa taji tausayinsa yashigeta har taji zata iya hakura da auren DEENi . Dan haka ko ajikinta ta wuce.

Jikinta a sanyaye yashigo part dinsu hankalinta a tashe
Tana shiga daki Ta daure fuskarta "ganin ya shigo dan a zatonta yana shigowa zai zabgamata mari.
sanye yake da t shirt din su na sojoji da wando.

Tana jinshi yacewa Ummi shi ya wuce sai da safe "Ummi tace can zaka kwana ne yau ?
yace eh "akwai abinda zai maidani tace to Allah ya tsare min kai ya km bada sa'a ,ka yawaita addu'a dan Allah yace Ina yi sai dai zan kara kulawa .
ya sake wuce zeenat zaune ko kallon inda take baiyi ba .

bayansa tabi da kallo tana jin wata irin masefaffiyar kaunarsa nabin jininta, hade da ratsa kowani part na jikinta.
, aranta tace attajirina kennan ,miskilili zaki maza .
nan ya fita yabarta da dadeden kamshinsa tare da fargaba.
sai dai, da ganin yanayinsa yana cikin tsananin fushi .

da misalin karfe tara dare tana kwance akan gado" juyi kawai take, yayinda zuciyarta ke nazari akan irin kallon da yaya deeni yayi mata, dazu sakamakon ganin da yayi mata tare da kamil .

ta ji tamkar takirashi tabashi hakuri amman tsananin tsoransa ya hanata aikata hakan , zuciyarta ce ta bata shawara kan tura masa text ba sai takirashi ba .
dan haka ahankali ta mirgina ta janyo wayar Ummi dake kan bedside .
ta soma rubuta masa text da niyar turawa masa " sai km taji zuciyata na gargadinta akan kar ta sake ta tura masa text din . Tayi tana tunanin ,ta tura ne ko ta share
Tayi haka ya yafi sau goma kafin daga karshe tayi jahadi ta tura masa .

Yaya dan Allah kayi hakuri idan na bata maka rai dazu wlh bazan sake ba ... daga zeenat
Chapter 20 · 0% Book details