← Book details Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 90

Sashe 56

Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Page 58

Rungume take a faffadan kirjinsa har lokacin " yayinda hawayen tausayin kanta ke cigaba da bin kuncinta" danasani tattare da nadamar abinda ta aikatawa kanta a can baya ne ke damun zuciya .
'hakika rayuwa bata da tabbas gashi komai yana neman tsaya mata " zuciyarta kemata wani irin zafi yau tazo mata tazo mata abu mafi muni ,kishiya ...fa.
yau ita zeenat da kanta ake kokarin son sanya mijin yi karo mata kishiya... Kishirya.. ta sake maimaita hakan akasan ranta abinda tafi mugun tsana a rayuwarta kennan ,wai aba kishiya ..

kirjinta ke mata radadi da nauyi tamkar an dora mata dutse ita kadai tasan yadda take jin zuciyarta da gangar jikinta... wani irin maseefaffen kishin mijinta ne ke sake tasomata fiyye da yadda take ji a da.
tsanar sauran matan dake duniya zaune bbu aure ne ya dirar mata lokacin.

Kukanta yasoma damun tunani ,kasancewarsa mutun marason damuwa da yawan hayaniya. hakan yasa yasoma sausauta rungumar da yayi mata daga qarshe ya ma rabata da sansar jikinshi gabadaya.

, Tare da zuba mata rikitattun idanushi kawai Dan shi sam kwata kwata bai iya wani abu wai rarrashi ba . ballanantana har ya tsaya wani bata lokacinsa gurin rarrashinta .

,a dake taji sautin muryasa ',malama kiyiwa mutane shr duk kinbi kin cika min kunne da wannan bazan kukan naki mara ma'ana ..

ko uban wani ne ya aikeki wulakanta cikin da Allah yabaki tun farko .

Wlh idan kikasa damuwarki tashafi lafiyar mahaifiyata akan maganar kishiya ..nan zan baki mamaki ..
kishiya ...bama daya zanyi ba har biyu idan nagama sai nayi .
"inyaso ki mutu sai ki kashe kanki kmr yadda kika ce ,sha sha kawai ya fadi hakan yana may da jan mugun tsaki... mtssss .

take jikinta ya dauki rawa kirrrrrrma jin maganar bama kishiya daya ba har idan yaso zaiyi ..
"ai ...batasan sanda ta zube kasa ba.
Tana kuka Tana girgiza masa kai dan gabadaya kasa magana tayi sai jujjuya kai kawai take tana zubda kwalla.

Wata uwar ,harara ya watsa mata hade da binta da wani irin bazan kallo wanda yasan hantar cikinta kadawa wayyo hrt karka min haka dan girman Allah karka min kishi....sai km Tayi shr Tana cigaba da kuka.... bakinsa Ya tabi tare da cewa meyya haka oya Mike .. Mike ni kibar min dakin kinsa fa ni bana son damuwa .

Yana gama fadar haka ya haura saman gadonsa ya dau towel daman km abinda ya fito dauka kennan .

bathroom ya sake koma ya sakarwa kansa ruwa tare da dauro alwala sannan ya fito kugunsa daure da towel .

mamaki ganinta yayi har lokacin bata bar dakin ba Tana nan durkushe tamkar yadda yabarta ,ganin yanayinsa da km yadda yake kallonta da rikitattun idanushi masu matukar birkita mata kwalkwaluwa ,da hana zuciyarta sukuni .
yasa ta mike tsaye da sauri jiki har rawa rawa yake tsabar tashin hankali ,a sukwane ta tabar masa dakinsa Dan tasan halinsa maseefar sa, bakaramin aikinsa bane ya shuka mata rashin mutunci idan ma taci sa'a Bai hada mata da mugun duka ba tunda daman ya mata gargadi kar sake ganinta bedroom ba .

Fitarta daga dakin yayi daidai da sauke naunauyen ajiyar zuciyar da yayi..
, yayinda wani gefe na zucitarsa na Dan tausayawa mata game da halin rayuwar data jefe kanta ciki.

hakika shi yasan tana wahalar da zuciyarta ne kawai akan batun kishiya .
Dan kishiya ba fashi sai ta zauna daita.

'ahankali ya sake sauke wani naunauyen ajiyar zuciya tare laso lip's dinshi na kasa ...
" cikin sauri ya shiga shirya kansa cikin wasu hadaddun kananan kaya masu matukar kyau da daukar hankali shirt ce ashi colour mai gajeren hannu sanye a jikinsa sai wando blue jeans wanda suka yi matukar karbar surar jikinsa.
' koda yake shi din may matukar kyau ne km kowani irin kaya ya sanyawa jikinsa sai sun amshi karbi shi.
, cikin sanyin nan nasa da takunsa na kasaita yakarasa gaban mirrow ya dauki turarensa mai matukar kamshi ya feshe ilahirin jikinsa dashi.
' sannan ya gabatar da sallah byn ya idar sallah ne ya sauko parlour kasa cike da isa .

Anan ya iske ,Ummi tare da zeenat zaune sunyi jugun jugun abin duniya ya damesu.

Ummi ta rafka uban tagumi tana tunani duk da yasan zance dai bazai wuce akan maganar aunty shi bane .

Yana tsaye yana kallonsu yaga zeenat ta kwanta akan cinyar ummi tana kuka ' tana goge Hawayen idanunta da bayan hannuta kukan ya isa haka mamana kada wani ciwon yakamaki fa.. . Ummi bazan iya zama da kishiya ba wlh taba kirjina kiji ta fadi haka tare da janyo hannun Ummi zuwa saman kirjinata .

Kallo daya yayi musu tare da dauke idanunshi daga kansu..
ya tabe baki kai tsaye dinning area ya nufa yaci abincinsa hankali kwance . Sannan yacigaba da zamansa yaciro wayarsa yana operating ..
Km duk yana jin abinda zeenat kecewa da yadda Ummi ke rarrashinta da kwantar mata da hankali akan bbu wata kishiya da za'a yo mata ita kadai ce bbu kari ...
, Jin haka Yasa Daga can inda yake zaune yayi gyaran murya.
,Ummi ce ta juyo 'ahankali Tana dubansa ,yatsansa daya ,ya karkada mata alamun a,a harara Ummi ta sakar masa yayinda shi km ya girgiza mata kai kawai yana tabe baki.

Ahankali Ya Mike tsaye ya dawo kusa da Ummi Ya zauna fuskarsa a hade yace ke.....yi excuse dinmu please zata Mike kennan ummin ta maidaita Dan me zaka korar min yarinya tana cikin halin damuwa ?
idan har baka shirya yin magana dani bane tana nan kana iya barin maganar har zuwa wani lokaci dan bbu inda zata ke koma kiyi kwanciyar kinji..
,koma kuwa tayi kwanciyarta kmr yadda Ummi tace amman har lokacin Hawaye bai daina bin kuncinta ba .

Kafadarsa ya sake dagawa alamun bai damu ba da abinda Ummi tace ba ..
Wayarsa ce ta dauki kara sauti mai dadi Mikewa tsaye tare da pic din call din ya manna a kunnenshi tana tafiya .

Hello ..Yaya ganin nan zuwa yanzu sannan yakashe wayar yabar musu gidan gabadaya .

Yana fita Ummi ta dauki wayarta takira hajiya turai bagun farko hjy turai ta dauki wayar da sallamarta " bbu abinda Ummi tasoma tmbyrta sai an km samu kuwa ?

Ummi tayi hakan ne Dan kada zeenat din tadago wani abu dangane da shirinta.

bangaren hjy turai kuwa cewa Tayi eh ansamu amman sai dai guda daya ce km Tanada dan shekara ,Ummi tace kmr shekara nawa gareta ?

eh zata kai kmr 23 haka inji cewar hjy turai ok ki kawota naganta hjy turai tace sai dai kibari zuwa gobe idan Allah Ya kai mu ' latifa zata zo gurina idan zata wuce gida zan bari takaraso miki da yarinya ,Ummi tace ok shikennan sai sun zo din takashe wayarta tare yiwa hjy turai godiya .

Washegari da misalin karfe hudu daidai latifa takawowa Ummi shafa. kallo daya Ummi tayiwa yarinyar taji kwata kwata bata kwanta mata arai ba a ranta tace itama kennan Ina Ga oga DEENI.
tasan ma bazai wank mu,ammultu da yarinyar ba , girgiza kai kawai Tayi byn tasa an kawowa latifa abin motsa baki .

,'ahankali Ummi ta Mike tsaye ta nufi wani kofa tayi warning din glass tare da cewa latifa ta biyo bayanta , latifa ta Mike 'ahankali tabi bayan Ummi .

Wani madaidaici parlour Ummi takai latifa byn sun zauna ne Ummi tace Kira sunan lafita ta amsa kina jina latifa ..yarinyar nan bata min ba km nasan tunda bata min ba da wuya tawa mai gidan Shima kinsa shi da kyankyami tsiya .

dan haka asamo wata kota gurinki ne amman dai zan bar Ita wannan din kafin asamu wata ,dan aikin gida sbd aikin nayiwa laraba yawa ,latifa tace ok babu damuwa ,daman kuwa akwai wata yarinya dake neman aikin gida irin wannan amman kibari zan miki kokari inshallahu .
Ummi tace shikennan latifa Nagode sosai suka yiwa juna sallama sannan latifa ta wuce .

Byn fitar DEENI daga gida kai tsaye gidan yayansa mahamud dake cikin estate din yayi .

zaune suke shida da Yaya Muhamud din babban parlour baki na gidansa .
Shr yabiya baya kafin Yaya Muhamud ya numfasa tukun yasoma magana kmr haka DEENI abinda yasa nace kazo nan ina nemanka ,akwai magana may mahimmanci da nake son muyi akan company,s dinmu.
,kaga dai yanayin danake ciki halin yanzu nima girma ne yake zuwa min yayinda abubuwa ke sake min yawa ni kadai raina nake kokari akan lamuran company,s dinmu na cikin gida da sauran kasashen duniya shine naga yakamata ace kaima , ka'ajiye wannan aikin naka kazo mutaru mu kula da komai Tare.

,kasan mutane wasu basu da amana , amman yaka Gani akan lamarin .. DEENI yayi shr kawai yana sauraransa har yakai karshen zance ,sannan ya dan yi murmushi karfin hali har dimple dinsa ya lotsa ,rasa mezai cewa yayansa yayi dan haka yace shikennan Yaya zan duba nagani idan hakan zai yiwu dan gsky Ina matukar son aikina km banason abinda zai rabani dashi .

,DEENI..yaya Muhamud ya sake kiran sunanshi DEENI ya dago da idanushin yana dubansa dasu , wannan aikin naka yana mahimmanci a rayuwa Shima km talafawa company,s dinmu haka ,amman abinda nake so dakai kaduba din kmr yadda kace ,nan suka bar zance suka shiga hirar duniya har DEENI yake sanar masa da abinda mama ta abuja, tayiwa Ummi akan zeenat , Shima Yaya Muhamud din baiji dadin abinda Tayi ba .

Bayan wata biyu

Al'amarin duniya fa yasoma damun Zeenat tayi mugun tada hankali kan maganar aunty,n su Ita DEENI gabadaya afrigice take da komai , kawai burinta ahalin yanzu bai wuce kawai ta ganta dauke da ciki ba .

amman kwata kwata hakan yaki samuwa gareta ga lokacin na tafiya , gabadaya hankalinta a tashe yake matuka.
Chapter 56 · 0% Book details