← Book details Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 90

Sashe 60

Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zeenat ta Mike a yangance ta nufi dakinta na kasa bata dade ba ta sake fitowa ta mikawa Aunty Salmah kudi masu yawa takarba tare dayin godiya sannan ummi ta danna intercom minti kadan Sai Ga laraba ummi tace laraba Ga sis nan kinsamu koma nace "ya" laraba tashiga bude hakora tana dariya ki dauki jakar kayanta ki kai opposite to ur room laraba ta duka tare da dauka jakar kayan nablah tayi gaba tana murmushi samun abokiyar hira Dan tunda shafa ta wuce take cike da kewa .

Aunty Salmah ta Mike tsaye to ni nablah zanwuce itama nabla Mikewa tsaye tayi domin son yiwa auntyta rakiya.

ummi tacewa Salmah baki bani account din ba har gashi zaki wuce aunty Salmah tace zan turo miki ta waya sannan km zan bawa mahaifiyarmu number ki sbd koda tana son magana da nablah.

ummi tace bbu komai Sai kinjimu sukai yi sallama suka fito tare da nablah hannunsu cikin juna .

Sun Dan yi nisa da gidan kadan suka tsaya aunty Salmah ta dube nablah da kyau tace yana Ga duk kinyi wani iri,kodai kin fasa yin aiki ne muwuce Dan nima Ina jin wani iri ajikina barinki dazanyi ?
, estate shr haka kmr makarbarta , maganar aunty Salmah ce tasa nablah sakin murmushi tare da cewa kai aunty , aunty Salmah takatseta da bawani kai aunty , idan kinji da matsi da takura ,waya kawai zakiyi min kice aunty kizo nabla ta sake sakin murmushi Wanda ya bayyana wushiryarta me matukar kara mata tsantsar kyau.
cikin siririyar muryata me dadin sauraro tace kina zuwa ki dauke ni peeeeeee mu wuce abunmu ko auntyna.... suka saki dariya a tare sannan suka cigaba da takawa 'ahankali har suka karaso bakin get din estate din .
ita km aunty Salmah tashiga office din da suka shiga dazu sanda zasu shigo, ta sake sa hannu da lokacin data fita ,duk nablah na tsaye tana kallosun tare da dagawa auntyta hannu har ta fice daga estate din sannan ta juyo jikinta a mace 'ahankali tasa bayan hannuta ta goge Hawayen daya zubo daga idanunta.

Da misalin karfe tara na dare tana zaune a dakin da aka mata sauki byn ta idar da sallah isha'i ta cire hijab dinta ta nike tare da shirin ajiye akan jakar kayanta kennan taji ana nouking kofar dakin 'ahankali ta mike taje ta bude kofar badan tayi wa kofar key ba .
laraba tagani tsaye tana mata murmushi tare da cewa kizo inji hjy dayake ita da haka take kiran ummi.
nablah tace to ta juya koma cikin dakin ta dauko hijab dinta ta zira har kasa ta biyo bayan laraba 'ahankali take daga kafafunta cike da sanyi jiki da natsuwa har suka iso wani parlour.

,kallo daya nablah tayi gurin tagane bawanda aka saukesu ciki bane dazu abinda yasa tayi saurin gane hakan kujerun wancan parlour da wannan ba iri daya bane , sannan komai na wannan parlour daban yake hatta pantting laraba ta Dan duka tace hjy gata nan ummi batace komai ba Sai ma daga mata hannu datayi alamun ta wuce .

Ummi ce zaune da Zeenat suna facinga din juna hira suke suna kallon Ball hankalinsu kwance , nablah ta gaishe su da hannu ummi ta amsa mata tare da nuna mata gurin zama .
amman ita Zeenat ko kallon inda nablah take batayi ba sai ma sake maida hankalinta datayi Ga TV .
Nablah bata zauna kan kujera ba kmr yadda ummi tayi mata nuni waje tasamu kasa nesa kadan dasu ta tattare hijab dinta ta zauna shr kusan minti goma bbu Wanda ya sake cewa komai acikinsu daga ummi har Zeenat Sai karar TV da AC dake aiki....

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Page 60

'Ahankali ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta wanda kusan rashin abinyi ne kesata yin haka.

,haske taga ya garwaye parlour gabadaya 'koina ya dauki haske tamkar rana ce ba dare ba.
wani irin kamshi ne mai azababen dadi yake kusantota ,har inda take zaune ,yayinda mamallakin turaren ke tukarowa parlour zuwa indasuke haka shima kamshin ke kai kawo acikin hancin nablah .
har zuwa sanda mamallakin kamshin ya karasa yashigowa, gabadaya parlour ya canza wani irin cent na daban", take gabanta yashiga dukan uku uku gashi tana san dagowa ta kalli kowaye mamallakin wannan azababen kamshi Amman takasa dago idanunta,dan ko kwakkwaran motse kasawa tayi ballanantana tasan kowaye mamallakin wannan turaren mace ko namiji ne sakamakon kanta dake Duke akasa har lokacin.
Ta kafe teas din parlour da ido ".

Ta kasan idanunta ta hango wando jeans. wanda hakan ya tabbatar mata da mammallakin kamshi turaren nan namiji ne .
"duk da bataga komai nashi , baya ga Zara zaran yatsun kafafuwansa da kowani ke kwance da gargasan gashi.
'ahankali yake takowa zuwa inda ummi take zaune .

Muryar ummi taji tana cewa ka fito son ?
tun da zu muke Jira ... matarka tace wanka kake yi ,'ahankali ya juyo ga mahaifiyarsa yana kallonta sannan yadanyi murmushi gefen baki .
hannunsa yasa ya dauki remut ya canza channel zuwa ta kallon Ball sannan ya Mike kwance kan three site hade da cewa gani first lov anything for you my beautiful mum...
Ummi ta saki murmushi sakamakon jin dadi abinda yace sannan tace kai ko Allah ya shirya min kai ...tare da kai hannuta kai kan tilon dan nata ta shafa tautausar sumar kansa tana jin wani irin sanyi a ranta .

Muryata A dake takira sunansa ' deeni.....
Ya dago rikitattun idanushi yana kallon ummi batare da yace komai ba ...
"maganar mai aiki da mukayi dakai za'a kawo ,to orready ma she's here.. ta iso sauran muji meyye ra:ayinka nidai na amince daita hundred percent ..

kasa kasa yayi da muryasa wanda daman can haka yanayin maganarsa take ..
Kuma yadda yayi magana ummi ce kawai zata iya jin meyace ..

tana ina .......?

abinda kunne nablah ya ji kennan.
gata can ummi ta fada tare da nuna inda nablah take zaune ...

'ahankali ya juyo tare da kallon inda ummi tayi mishi nuni da hannuta. idanunshi ya runtse gam sannan cikin sanyayyayiyar muryasa mai kashi jikin duk wanda tsautsayi yasa ya fada kunne shi " yace first lov... kice ta Mike naganta ..

tsoro da fargaba tare da frigice ne suka taru suka kaiwa zuciyar nablah farmaki" tashi daya taji jikinta yakama rawa gabanta yashiga faduwa da sauri, tasoma tunanin abinda ya kawota wannan gida mai cike da abun tsoro da abubuwan ban mamaki ...

sai kawai ta tsinci kanta da ambato sunnan Allah a kasan ranta da karanto duk addu'ar datazo bakinta Dan rage jin tsoro " take taji wata natsuwa tazota mata aboye ta dinga sauke ajiyar zuciya .

'Ahankali ummi takira sunata nablah Mike tsaye man ya ganki , batare da wata gardama ba,ko bata lokaci ta Mike tsaye kmr yadda ummi tace .Amman still jikinta Bai bar kirma ba haka ma hannuwata suna sarkafe da juna tana cigaba da wasa dasu " yayinda ta cikin hijab dinta kuwa uhmmmm tashin hankali kennan 'dan kuwa jikinta sharkaf yake da gumi tsabar frigici datake ciki ,duk da tsanyi AC dake aiki a parlour hakan bai hana gumi tsassafowa ilahirin jikinta ba .

idanunshi da Suke a runtse ya kafeta dasu yana kallonta ,jin shr,n da yayi yawa ne yasa nablah dago fararen idanunta dan satar kallon mutumin dataji an Kira da suna DEENI . take zuciyoyinsu suka buga a lokaci daya .......

Yayinda jikin nablah ya dauki kirma... zuciyarta ta sake amsawa daf..daf..daf.. 'da sauri tayi kasa da idanunta ahankali ta furta wayyo Allah na.. a kasan ranta.. mutun ko aljani nake Gani yau .

, tsabar kyauwu halitta da Allah yayi masa .tunda take a rayuwarta bata taba ganin mai tsananin kyau halitta da kwar jinin irin mutumin da take gabansa tsaye a halin yanzu haka ba .

kusan tsawon minti 5 ya dauka yana kallonta batare daya bude Idanunshi ba" sannan 'ahankali ya dauke idanunsa daga gareta yakoma ya kwanta sosai acikin kujerar dayake "ummi tace ya'akayi ne DEENI naji kayi shr... ....

Tayi.....
.
abinda kawai nablah ta iya ji kennan daga bakinsa , Dan gabadaya ma jitayi kunneta ya daina jin magana tsabar tsoro da rikici hakan km sai lokacin hankalinta ya dawo gangar jikinta daga mummunar damuwar data tsinci kai ciki ...
Amman fa duk da Haka a tsorace take da mutumin dake kwance a gabanta .

,ummi kuwa ta furta kalmar alhamdulilllahi yafi Sau dari kafin daga baya ta kalli nablah a tsanake sannan tace jeki nabla ma hadu gobe kinji ..

,muryarta nablah a sarke tace to ... sai da safenku sannan ta juya cikin tsanyi jiki ahankali take tafiya yayinda itama ummi ta juyo tana sake bin bayan nablah din da kallo har tabar parlour zuciyarta na karanto mata abubuwa dayawa game da yarinyar ga wani irin tausayin yarinyar daya mamaye zuciya ...

Bangaren deeni kuwa gabadaya ji yayi tamkar am masa wanka ne da ruwan sanyi , jikinsa ya mutu murus tamkar mara lfy haka ya dinga ji ajikinsa tun sanda yabi hannu ummi da ido .

kwarai yaso ya bude idanunshi yakarewa yanayinta kallo Amman sam yakasa aitawatar da hakan , sai ma tsintar kansa da yayi da mummunar faduwar gaba a lokacin da yake kallonta .
, wanda har yanzu dayake kwance a wajen bai daina jin yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri ba ..

'ahankali yasake runtse idanunshi gam ko zai daina jin abinda yake ji ajikinsa ,amman kwata kwata sabanin haka Ya dinga ji .
Sai ma zuciyarsa da tacigaba da harbawa da sauri da sauri .

abinda bai taba ji atare dashi ba kennan tun iya tsawon rayuwarsa wai faduwar gaba akan mace ....
Macce ma , mai matsayin mai aiki ...

ahankali ya furta sunan da yaji umminsa takira yarinyar dashi nab....lah... Yadda ba mai jinsa ....

muryar matarsa yaji tana cewa ummi ai wannan yarinyar bakaramin daga tuta tayi ba , tunda har my hrt yace tayi.
Chapter 60 · 0% Book details