← Book details Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 90

Sashe 32

Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ita dai zeenat tsit tayi da bakin ganin yadda ya dau zafi , kyacci yayi tare da jan tsaki sannan Yasa kai ya fice abinsa .

Hirar yaushe gamo ta barke tsakaninsu.
,Ummi ta dubi zeenat me zaki ci a dafa miki ta dan langwabar da kanta tana tunanin abinda zatace Amin soyayyiyar doya ,Ummi ta sake kallonta da kyau dan sanin data mata bata cin doya ,shr kawai tayi ta nufi kitchen .

Har dare suna tare dasu shemah sunki tafiya .
,to oga da kanta ce yau tazo gida, dan zeenat ce lidarsau gabadaya komai za'a yi sai tabada Command sannan za'a yi .
" dan haka gabadayasu suka taro anan part din Ummi suna ta hira har sanda Ummi tagama soya doyar tace Maryam tazo ta daukar musu.
tare suka ci suka sha ,sai zeena bata wani ci may yawa ba .
say faman murna take ganinta cikin yan'uwanta .

ta gefe daya km ga Ummi murna tamkar ta kasheta dan dadi .
,har mantawa tayi da wani deeni ,dama wayarta gabadaya.
, deeni yayita kiranta a waya yaji shr taba dauka ba.
,har say data kaishi ga kiran Ummi ta miko mata wayar .
ta karba tare da bmyr Ummi da hannuta waye ,mijinki abinda Ummi ta fada kennan.

Ai da sauri Ta manne wayar a kunneta tare da sallama ,ko amsa sallamar bai yi ba .

Yana jin muryarta yace ke.... dan iskan Ina kika shiga kika bar wayarki ,tun daxo Ina faman kira?
,mikewa tayi tsam tayi ciki dakin Ummi tare da marairaice murya wayyo dan Allah Yaya kayi hakuri wlh abinci nake ci .
km wayar tana cikin hand bag dina.
Cin abinci ne har tsawon awa hudu ?
Kifa kiyaye zeenat .
naga kmr kanki na rawa rawa fa.

Say hakuri take faman bashi ,shi km yana sake botsarewa ,ki cigaba zan gyara miki ,zama ne bar ganin kina kusa da Ummi ,km kishirya ganin nan zuwa ,mu wuce ,gida .

Batasan sanda ta sakar masa kuka ba.
tana sake bashi hakuri ok kuka ma zaki yi wa mutane tsabar kin raina min hankali ko .

, , ita dai batace masa komai ba say ma hakuri data tacigaba bashi .
, dan Allah Yaya kar kamin haka kabarni zuwa byn suna na koma .
,gobe ne sunan fa.
,anki abar ki' idan ma kika sa wasa ,sunan ma ba zakizo ba gabadaya naga abinda zai faru.

,kawai ya kashe wayarsa batare da tsaya jin abinda zatace ba .

Sosai take kuka har takaraso ta mikawa Ummi wayar duk da ta dan goge hawayen fuskarta hakan bai hana Ummi ganewa ba .
,ta tambayeta tace bbu komai ,haka dai zakice bbu komai kiyi ta zama da abu acikin har yazo yamiki illa.

,ta zauna tare dayin shr sure Maryam ma sudan ga sauyi a tare daita Amman bbu wanda ya damu da tmbyrta ,suka cigaba da hirar su sama sama .

Shr kawai tayi zaune a gurin yayinda ta dinga jin wani abu nataso mata a kahon zuciya, tasa hannu ta dafe kirjinta tare da runtse idanunta gam cigaba abin yayi da taso mata .
gabadaya cikinta ya aushine ,bakinta yacika da miya ,wani irin amai taji yana taso mata ,da gudu tayi bathroom din dake manne a main parlour .
Ako ta dinga Kwara amai ba kaukautawa tare da rike cikinta .
Aman ta dinga kwarawa tamkar zata amayo da kayan cikinta . gabadayansu suka gigice sukayo kanta sunata mata sannu.
Maryam ce tayi dakin Ummi dan ta sanar mata.
Wani yunkurin amai ta sake yi ,dai dai lokacin da deeni ya sawo kanshi cikin gidan
,da sauri ya karasa shigowa duk da bai san takamaiman wakeyin amain ba.
,suna ganinsa suka dare gabadaya ,ga mamakinsa zeenat ya hangota durkushe Sai amai take Kwara gabadaya ta galaibaita jikinta yayi week ,atare suka yo kanta shi da Ummi kusan ma yariga Ummi karasowa bakin kofar bayin yana kallonta har lokacin amai take
say dai ga , dukkanin ,alamun bbu wani wadataccen abinci acikinta .

Ahankali ya durkusa a gabanta ya dafa kafadarta yana mata sannu.
,zaman dirshan tayi a bakin kofar tana mayar da numfashi .
Ta fashe da kuka da ,tare da jingina jikin bangon .ruwa ya dibo ya wanke mata bakinta da fuskarta .

ganin haka yasa Ummi juyawa takoma dakinta tare yin addu'ar Allah ya inganta musu , daman ita tun wancen zuwan nata datayi gidan nasu ,take ma zeenat din kallon may ciki.

Zeenat duk tarasa inda zatasa kanta taji dadi.
km har lokacin su samiha na sunki tafiya , ahankali deeni ya juyo inda suke tsaye cirko cirko suna kallon shi da zeenat din .
,muryarsa zafafe Yace tsayuwar uban me kukewa mutane ,yan iskan banza kawai yarinya tana mai anrasa wanda zai taimaka mata ,duk kunzo kun rufeta kuna kokarin kasheta.
,Ai tunin suka gigice suka soma tattara inasu Ina su ,subar gidan .
Yaja tsaki ya km maida kansa kan matarsa .

Juye juye kaiwa take tana kuka tare da kiran sunan Ummi .
ya fizgota tare da daka mata tsawa kina hauka ne ?

ko kallonsa batayi batayi ahankali tasoma rarrafawa tafito daga bathroom din ta zauna kan kujera ta jingina kanta tacigaba da kuka tana mayar da numfashi.

ya Mike ya dawo kusa daita yana kallonta yasa hannushi zai dafata ta Mike da sauri Ta km shige bathroom ta durkusa tashiga kwara wani amai ,jikinta har wani rawa yake.
lokaci daya jikinta ya dauki zafi ya riketa yana mata sannu ta langwabe masa tasoma kokarin mikewa ya rikota.
Yace Ina zaki? gurin Ummi zani .
,say km ta fada kansa wayyo kwanciya zanyi na gaji yaya ..
Ya dagota ya wanke mata baki da jikinta ,ya dauke cak yayi dakin Ummi ,daita.

Ummi ,ta dinga jero mata sannu .....
, mikowa Ummi hannuta take alamun tazo gareta.

,Ummi takarasa ta zauna kusa daita ta kamo hannuta cikin nata.
,sannu zeenat .ya jiki
Ahankali zeenat ta lumshe idanunta ,cikin sanyi murya yadda deeni bazai ji abinda zata fadawa ummin ba.

Tace ,ummin dan Allah karki bari Yaya deeni ya tafi dani gida ,take gaban Ummi yashiga dukan uku uku.
,itama ummi cikin muryata kasa kasa tace wani abun yake miki agidan ta girgiza kai.
wlh baya min komai sbd sunan shemah ne.
,say lokacin gaban Ummi yabar faduwa dayake .
tace shikennan ta Mike tabar dakin ,shi km deeni ya dawo inda Ummi ta tashi.
,daukarta yayi ya zaunar daita akan cinyarsa ,ya hada fuskarshi da tata waje daya ido cikin ido suke kallon juna , zeenat ....yakira sunan da wata irin murya ta wacce tayi nasarar kashe mata jiki ,ta amsa da Na'...am ....my hrt.

sunan data kirashi dashi yayi mishi dadi Sosai har yasa shi yi murmushi wanda har dimple dinsa ya lotsa .
Idanunsa ya zuba mata yana sake kallon kwayar idanunta .
Yace Me kika sanarwa first lov wanda ni kika kasa sanar min after ol ma
meke damunki kika dinga kwara irin wannan amai ?
Ta girgiza masa kai kawai alamun bbu komai .
Yace yanzu yakike jin jikin naki.
da kyar ta iya bude bakinta tace daidai nake jina.
say abunda ba'a rasa ba .
,yace kinci abinci ma kuwa?
,tayi murmushin karfin hali ,tareda cewa naci doya dazu itace ma ta dinga tasomin .
Amman Tunda na amayar daita naji ,daidai.

, Yace ok ki shirya mu wuce gidanmu ko ..
ba mutsu tace masa to tasoma kokarin mikewa yace bi ahankali fa .

Tsab ta shirya abunta kmr bbu abinda ta shuka .
, parlour'n kasa , Suka tadda Ummi a zaune tana kallon labarai a CNN.
'ahankali Ummi ta dago tana kallonsu ,Ina zuwa haka km .
,sukayi suru suru dukkansu suna duban Ummi dake zaune.
say ma deeni ne yayi karfin hali cewa gida zamu .
gidan lfy zaku byn kana kallon yarinta badata da lfy shine ,zaka wani ce gida.

Ba gida ba tukun runbu zaku dan Allah ni kyalle min yarinta takara samun natsuwa .
,Yaya da naci haka idan zaka iya kadawo jibi ka tafi daita.
DEENI yaji tamkar kasa ta tsage yashige cikin Dan tsabar kunya da takaici abinda Ummi tamasa ,.

Take 'ya Gane setup , ne kawai aka masa dan kar zeenat din tabishi .
dan haka ya dinga kallon zeenat din tare da hararar ta .

Da sauri tace Allah Yaya ni bbu ruwa acikin ,mu wuce kawai abunmu .
da hannushi ya katseta ,karki dama kiyi zamanki kawai basai kin bini ba ya juya.
,tabi bayansa da hanzari zata bishi.
Ummi takira sunnanta ke zeenat dawo nan ahankali tasoma girgizawa Ummi kai tamkar wata kadangaruwa.

Wai ,bada ke nake ba inji cewar Ummi ,jikinta a sabule ta dawo kusa da Ummi .
ta zauna ,duk jikinta yayi mata sanyi .
Ummi tace kima saki jikinki ki manta dashi ,ki daina wani dar dar .

,ke wai har yanzu baki bar jin tsoransa ? Zeenat Ta zubawa Ummi ido kawai tana kallonta ,Ummi tace kin tsareni da idanu .
, zeenat tace Ai kece Ummi da wani abu.
Aa ba haka yakama kiyi masa ba.
.ni dana so ki lallabaminshi ya Amince da kanshi Shi kika tunzarashi .
Ummi ta saki baki Aa ba tunzarashi nayi ba kashe shi nayi .

,wawiya kawai kicigaba da jin tsoronsa say ya kwashe miki hanjin ciki tare da manna miki hauka .

Dan haka Zeenat din tayi shr ,dan gsky bataji dadin abinda tayi masa ba .

ahankali ummi ta dinga janta da hira har dai zeenat din ta saki jikinta sosai suka shiga hirarsu .
Har shadayan dare , zeenat tasoma gyangyadi Ummi tace suje su kwanta .

Kwance take akan gadon Ummi .hankalinta kwance take sharar bacci ba matsi ba takurar oga deeni ,yau daya taji salama , har taso ta makara tashin asuba sai da Ummi tayi da gaske tukun ta mkie .

Washegari ranar suna yaro yaci sunan mahaifin deeni ,wato aliyu .
Chapter 32 · 0% Book details