← Book details Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 90

Sashe 23

Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zeenat .....ummi takira sunanta a frigice ta juyo tana kallon ummi ,ci abinci abinda ummi ta iya cewa kennan .
DEENi dake zaune haushi kmr ya kashe shi tsaki ya dan ja ,ummi ta juyo bangaren sa Tace lfy kai km ?
Fuskarsa a dakune Yace babu , Sai da taga Ummi ta sake dubeta sannan tasoma cin abincin , shima bawani sosai .

Byn sati biyu

Shirye shiryen bikinsu zeenat aka soma sosai ba kama hannu yaro.

,anshirya komai na al'adar hausa kmr sabbabin dinkuna da gyaran jiki komai km tare akeyi musu ita da shemah km iri daya.
musamman ummi ta dauko kwararriyar mai gyaran jikin daga india domin ta gyara mata tilor diyarta da kyau.
duk wani gata da uwa zata yiwa diyarta "ummi tayiwa zeenat shi .
shima mahaifin zeenat din yayi iya bakin kokarin Sosai .

a nyi kamu amare idan aka feshe su da turare masu dadin kamshi na mutune India wanda duk wacce ummi ta dauko ta gyara zeenat din ce tazo dashi.
Anyi musu murzar lalle da kitso .
amman ansha fama da zeenat gurinyin kitso dan cewa tayi ita sam na attachment ,zatayi .
sai da ummi ta bude mata wuta sosai tare da cewa ,zata sanarwa DEENi tukun ta natsu .

Sau ran kwana biyu daurin aure mutane India suka iso , kusan mutum ashirin maza da mata sosai aka shiga hidimar da ,baki.ummi taji dadi Sosai dan kusan duk shakikanta ne suka zo wanda km shine zuwansu na farko Nigeria idan .

,gabadaya gidan nasu cike yake da baki dan haka ba kasafai zeenat din take zama a part dinsu ba ,tana can gidansu shemah .

Zeenat Tace dan Maryam muje kirani part dinmu ina son naga ummi yau duk banganta ba .
, Maryam Tace gaskiya na gaji da yawa wlh kije kawai . zeenat ta ja saki Tace dan Allah muje kiraki ni yanzu zamudawo.
shemah dake kwance ta mike zaune tace muje na rakaki kinsa halin Maryam da maseefar son jikin tsiya.
, Mikewa sukayi har sun fito sai ga Maryam Tace wlh baza kubarni ni kadai ba , zeenat tace ke km kika sani " idan zaki muje .
Tare , suka nufo part dinsu zeenat.
tafe suke suna hira irin tasu ta amare daga nisa zeenat ta hango motar DEENI parke a kofar part dinsu "daga gefe .
" can baya km motar fk ce sai wata motar daban wanda batasan ko ta waye ba .

Jingine yake jikin motar shi yana amsa waya sanye cikin English wear's black jeans da rigar ashi colour "mai gajeren hannu wanda ta fidda ainihin kyaunsa da gargasan gashin jikinsa dake kwance kan Gabar hannushi .
idanunta fes akanshi tana binshi da wani irin kallo saboda yadda taga yakara yi mata kyau. fuskasa har wani shekin annuri take fitarwa kmr ance ya dago idanunshi suka hada idanu.
da sauri ta dauke idanunta wani abu ta dinga ji yana tsirga mata ajikita. sai taga ya fita daban cikinsu fk duk da bawani kallonsa tayi sosai ba .
ta sake dago idanunta da niyar sata kallonsa suka sake hada ido harara ya sakar mata , kallo daya ya sake yi mata ya kau da fuskarsa gefe yacigaba da wayarsa a kallo dayan da Yayi mata yane yadda jikinta ya tsanyi .

kai tsaye zeenat taja hannun Maryam wacce tafi kusa daita ta juya da sauri ta karya cona itama shemah ganin haka yasa tabiyo bayansu da sauri tana jin fk na kiranta . shemah Tace yazaki biyo damu tana km.
zeenat Tace bbu komai mu bi nan di yafi sauki .

ta bayan part dinmsu suka shiga , da ummi tasoma cin karo ta rungume tana sakin ajiyar ,ummi tace meyye haka ?muryata kmr mai shirin yin kuka take Haba ummi yau fa duk banganki ba ,baki ga har wata rama nayi ba " tayi murmushi tace lallai kam kin rame dan ga natsuwa nan suna bikin dariya mutane dake tare da ummi suka shiga yi .
Ummi tayi gaba zeenat nabiye daita tana zuba mata shagwaba.
shape shape tayi abinda zatayi suka bar gidan .

Ranar daurin auren da safe ta nufo gidansu dan dauka kayanta dazata saka .
wanda ta manta bata hadu dashi ba cikin kaya .
,tafe take tana sauri . yayinda su ya faruk da abonkan DEENi ke tsaye duk cikin shirinsu na zuwa daurin aure .
amman banda DEENi wanda dagani shi suke Jira .
Wani irin kunya ce taji takamata dan haka ta dan janyo gefen mayafinta ta rufe fuskarta ,tana jin yaya faruk nacewa amaryamu ki bude idanunta kada ki fadi mana .
amman ina ko waiwayo batayi ba tacigaba da tafiyarta ta kofar baya tabi yauma.
tashigo dogon parlour'nsu ta baya kennan tasoma jiyo kamshin turarensa kafin tayi kokarin bude fuskarta taji sunyi karo da mutun .
da sauri takarasa bude fuskarta "yaya DEENi ne wanda zai fito har wayar dake hannushi ta fadi .
,gabanta ne yayi wani irin faduwa dan har wani juya juya ta dinga ji da sauri ta tsugunna dan miko masa shima ya tsugunna da zai dauka a tare hannunsu yakai kan wayar ,wani irin shock ne yajata " wanda baita kadai ba har shi DEENi yaji abinda taji.

Wani iri shima yaji ajikinsa tamkar an jona masa lantarkin .
. Shine yasoma kokarin janye hannushi daga kan nata ,ahankali ta Miko masa wayar batare da ta mike ba hade da cewa kayi hakuri dan Allah .

komai Bai iya cewa ba baya ga amsar wayar da Yayi ya barta nan tsugunne.

Bayansa tabi da kallo yayi matukar yi mata kyau har batasan yadda zata misalta ba sanye yake cikin shadda fara kal sai kamshin yake zubawa .
gabadaya kamshin turarensa ya gyaraye dogon parlour'n .
Ahankali zuciyarta tasoma bugawa tamkar zata basa kirjinta ..
girgiza kai kawai tayi dan batasan wani irin aure take shirin yi ba haka ta juya cikin sanyi jiki tabar gurin tana shiga ciki.m mutane akama kiranta da amarya amarya kinsha kamshi ita dai bata iya cewa komai ba dan gabadaya jikinta a sanyaye yake .

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Page 27-28

Part din cike yake da abonkan arzikin da en'uwa ,Ummi
Jikinta a sanyaye ta dinga ratsa mutane dake ,zaune a parlour ' har ta iso dakin ummi , da idanun take bin en dakin da kallo .
kozata ga ummi ganin bata alamunta bane , yasa tmbye matar uncle din Inda ummi take.
tace yanzu tashiga bathroom .
Ahankali ta fidda numfashi tare sauke ajiyar zuciya .
cikin haka ummi ta fito tana ganin zeenat din.
ta bata fuskarta "ta zauna tana dubanta"

gefen ummi zeenat tasamu ta zauna fuskarta dauke da murmushi wanda da Gani na karfin hali ne .

Cikin kasa da murya ummi tace yana ganki haka ina kayanki ?

Cikin sanyi jiki zeenat tace shi nazo dauka .

,ummi tace ke dai kin cika shiririta wlh "
komai baza kiyi shi cikin sauri da kazar kazar ba kin dinga jan jiki kennan ,kmr wata mage .

Alhalin kin san halin wanda zaki aura " dan oya oya ne .

jin haka yasa jikin zeenat din sake yin sanye, tare jin wata irin faduwar gaba " zuciyar ta dinga dokawa da sauri tamkar baso kirjinta.
ahankali tasa hannuta ta kamo na ummi
cikin nata jikinta har rawa yake hade da rage murya tamkar mai shirin zubda kwalla tace dan Allah ummi kiyi hakuri kinji karkiyi fushi dani ,zan canza inshallahu Amman " kimin addu'a .
wlh tun sanda aka samo shirin bikin nan nake jin faduwar gaba wanda narasa dalili .
ummi ta tayi shr tare da zuba mata idanu kawai tana kallonta .
tausayinta ne ya sake kamata , ,duk sai taga takara ramewa ba kmr kwanaki ba hakan yasa taji ba dadi aranta.
, ahankali ummi ta mike tare da riko hannuta tayi cikin , bedroom daita. En dakin suka bisu da kallon sha'awa duk da basu ji maganarsu ba Amman sun birgesu .

,Har suka shigo bedroom din Ummi na rike da hannuta Ta zauna daita tana rarrashita kan ta kwantar da hankalinta fargaban aurene kawai ke sata jin faduwar gaba Amman bbu abinda zai faru inshallahu "
Ummi da kanta ta shirya diyatata cikin wata arniyarta geziner ligth blue sai daukar ido take da kamshi tare da fesheta da turaruka kala kala masu sanyi kamshin take zeenat ta fito amarya sak .tayi kyau sosai
Ummi ,ta dauki waya tayi mata hotuna sannan takira Maryam tace tazo ta tafi daita din .

Kwanciyar tayi flat a kan gadon su shemah tana kallo da sauraran duk abinda ke faruwa .
a cikin dakin dake cike da en mata da kawaye

abinka ga mai yawan kawaye " da mutane kala daban daban " yasa dayawa wayan dake cikin dakin kawayen zeenat din ne .
gyara kwanciyarta tayi idanunta na kallon celling dakin hannuwanta duk rungume da kirjinta yayainda zuciyarta ke cigaba tsalle tamkar zata fasa kirjinta ta fito waje.

ahankali ta runtse idanunta sanyi taji yana ratsa koina a jikinta duk da tarin fargaban dake tattare daita hakan bai hanata jin jikinta yayi mata nauyi ba .
Tana ji ajikinta burinta da dokin son auren DEENi .
duk babu shi ahalin yanzu sakamakon fargaba da tsoron kasancewa tare dashi a muhalli daya .
Ta dauki lokacin mai tsawo kwance yayinda ta dinga jin wani iri ajikinta .
Bugun zuciyata na sake karuwa.
ta dinga kokarin ganinta ta cire damuwar dake damunta wanda a zahirance ita ta daurawa kanta .
har yanzu da take kwance jikinta a sanyaye yake takasa tabuka komai.
idanunta ta runtse tana cigaba da sauraron hirar dasuke sama sama .

10:30

Karfe goma da rabi daidai na ranar lahadi Allah ya cika alkawarinsa domin dimbin, jama'a sun shaida daurin auren NASURULDEENI ALIYU BELLO da MUZEENAT HABIB BELLO" daurin auren daya tara manya attajirai da kusoshin gwanati hade da maikata
bakaramin farinciki family din muhd bello suka yi ba ganin sun kara karfafa zumunci a atsakaninsu, .
dan haka farincikisu ya sake karuwa takoina ka juya , family din murna ne cunkushe a fuskokinsu
Chapter 23 · 0% Book details