← Book details Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 90

Sashe 12

Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zeenat data zuba tagumi ,Da hannu biyu tabi bayansa da kallo har yabar gurin idanunta na kansa , itama ummi data dauke idanunta daga kan DEENI "zuru tayi tana kallon Zeenat din , tana girgiza kanta .
waskewa zeenat tayi hade da sakarwa ummi murmushin dole ummi tayi mata dakuwa da hannu .

Byn DEENi ya gama amsa wayar oganshi ne yana zaune cikin mota wayar fk yashigo " yasa hannu ya dauki wayar ya duba ganin fk ne yasa ya maida wayar ,mazauninta .
Yakirasa yafi sau gomasha daya Amman yaki pic sai a karo na shabiyu ne ya danna wani abu "sai ga muryar fk radau yakarade koina a motar , hello.... hello DEENi kana jina ....
Yayi shr yaki yin magana,sai ma cigaba da yayi " da direving dinshi .
fk yace haba DEENi ya kana jin zaka min shr. "duk fa" maganar bata kai haka.
afusace DEENi ya katse shi yace maganar tafi haka har ta zarce haka a waje na.
km wlh wlh karka kuskura, ka tako inda nake da sunan kasan ni ai bansa cewar da kungurumin ,dan iska nake zaune ba.
fk yayi murmushi yace Allah dai ya huci zuciyarka ,dan shi.
bai fiyye fushi ba" kwata kwata ma bayason duk wani abinda zai kawo masa tashin hankali .
dan haka yayi tabawa DEENi hakuri hade da bashi baki .
DEENi yaja numfashi ya sauke ajiyar zuciya . hakan yasa fk ya gane cewar ya sauko kennan fk yace to yanzu yazamuyi da maganar da big dady yace.
DEENi ya tabe baki yace ya dai zakayi dan ni tuni na hakura da wannan yarinyar , karma ka km yimin wannan bazar zance.
daidai da yakaraso wajen aiki ,ya katse wayar fk batare daya tsaya ji mai fk din zai km ce masa ba .

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Page 17-18

Wata daya kennan fk yaji "shiru DEENi bai km yimasa zance maganarsa da Zeenat ba musamman" yazo gurinsa dan zance daman Kuma sun dade basu ga juna ba" sai dai sukan yi waya lokaci zuwa , lokaci dama ya kirashi a waya cewa yana nan zuwa .

Byn sun gaisa fk yace friend har yanzu ban sake jin batunka da yarinyar nan ba .
deeni ya gyara zama ,hade da yaja tsaki sannan ya lumshe idanunsa dan takaici da Haushi maganar .
ya zubawa fk ido yana kallonsa kawai domin rasa me zaice masa Yayi ,tsawon lokacin suna zaune a haka sannan fk yace friend hakuri zakayi dan Allah ba wai Ina son dawo maka da hannun agogo baya bane .

Amman idan maganar danayi akan Zeenat ya bata maka rai, kayi hakuri.

ahankali deeni ya furzar da iska mai dumi ya miko hannushi ya dafa gwiwar fk , Friend ban tasamun abinda ya bani matsala kmr maganar yarinyar nan" abin haushi duk lokacin da nayi kudirin hakura daita sai nakasa .

Kullum addu'a ta Allah yaye min ita daga raina Amman abin ya faskara ko son yarinyar ne yakamani "oho " fk yayi murmushi yace lallai sonta kakeyi Allah yasa itama ta soka haka .

DEENi ya gintse fuska yace Ina ruwana daita first lov ce kawai damuwata ,data amince da yanzu an wuce gurin Amman tsohuwar nan sai cewa take zan cuci Yar mutane ita bazata bani Yarinyar karama ba inzo Ina bata wahala fk yace sanin halin ka tayi dan kai din bana wasa bane kana raina yarinyar ne dayawa shiyasa ummi batason aura maka ita wani lokacin sai inga kmr da gaskiya ummi DEENI yayi masa wani kallo dan ni bason iskanci idan abinda yakawo kennan kana iya tafiya .

Fk yace zanje in sameta da kaina kar damu .
deeni yace dama kabar ta kawai dan ko kaje ba amincewa zatayi ba.
nasan halin first lov , da zata yarda da tunin ta amince .
na dai fada mata cewar ni na hakura dayin auren gabadaya" inda tagaji da zamana haka tasan abinyi .

Fk yayi ta dariya tare da xolayar DEENI" friend ka dai shiga da yawa da ka'ajiye duk wani girman kai ,ka dinga kiran yarinyar kana janta ajiki ,idan ummi taga haka zatafi yarda da gaske kakeyi "Amman kai kullum fuskarka a hade kmr hadari .

DEENi ya tabe baki, kasan Allah bazan taba iya kiran ko wace irin yarinyar bace, da sunnan zance koba Zeenat ba. kai ma abinda kariga kasani ne "bansa ta Ina zan soma ba ,nifa bana kawo Zeenat a raina ,in dai first lov ta yarda " to tayi hakuri ta aureni kawai dan ni banda wani lokacin ya mace . dan ma taji dadi ta samu miji irina ,yakarasa fadar maganar yana jan tsaki fk yayi dariya yace friend banda yabon kai fa , DEENI ya dan yi murmushi gefen baki har dimple dinsa ya lotsa kai ma kasan gaskiya fada ne dai kawai bazakayi cikin "nida ita wazai taimaka wani ?

Bbu abinda zata nuna min " fari ne kawaiya ceceta " wanda kai kasan ko man bleaching takara bazata taba kamo nawa ba "fk yace ai shiyasa ka daurawa kanka girman kai al'amarin mata" km duk da kafita kyau ita zuciyarka ta zaba ,ta zama abokiyar rayuwarka " zanyi maka iya bakin kokarina ,.

DEENi yabishi da kallo yace sannan ya maida bayansa ya jingina da kujera , dama kabar, damun kanka akan zance yarinyar nan , wai dole ne sai na aureta ,fk yace tunda nace zanyi kabarni mana ,na gwada sa'a ta ko ummi zata yarda . DEENi ya daga kafadarsa alamun shi yasani ,sannan yace tunda ka nace kaje din Amman idan labarin ba may dadi bane ,karka zomin dashi ba ,.

Kmr yadda fk yayi alkawari haka ce takasance yasamu ummi da zance byn sun gaisa ne yace daman akan zance deeni ne da Zeenat" ummi najin haka ta canza fuska " har tasa karfin gwiwar da fk yazo dashi " yayi kasa.

Ahankali yacigaba" dan girman Allah ummi kiyi hakuri ki amince da auren nan "saboda dukkansu naki ne a ganina wannan abin farin ciki ne .
Ummi ta sake tamke fuskarta Sosai tace faruk Ina matukar ganin kimarka da mutuncinka zai fi kyau kabar zance nan" bana jin cewar zan iya amincewa .
fk yayi shr yana tunanin yadda zai bullo mata can dabara tazo masa yace to Shikenan Amman naso ki Amince domin deeni yana cikin wani hali nason yarinyar nan. daidai lokacin da Zeenat ta dawo daga gidansu Maryam tanac kokarin shigowa parlour ummi .
,karaf zance ya fada cikin kunneta cak taja ta tsaya jikinta ya dauki kirma .
Fk yace ummi kin san halinshi baya daga cikin mutane masu magana biyu ,ya min ransuwa ba zai tabayin aure ba ,in ba Zeenat ba ,km duk duniya ita ya Gani yake so.

zamanshi haka nasan yana damunki ummi tace in duk duniya Zeenat yagani yake so ita Zeenat din ya sameta yaji ko tana son shi ? Ko haka kawai dan shi yana sonta" zan dauke diyata ta nabashi batare da ya nemi amincewarta ba.

Nifa bazanyiwa diyata auren dole ba dan kawai Ina son na faranta masa rai ba .

Daga inda Zeenat ke tsaye tana jin komai" take jikinta ya dauki yacigaba wara har wani zazzabi zazzabi taji yana neman rufeta , kafafunta suka Gaza daukarta sakamakon kirmar da suke , nan ta sulale kasa tana jin yadda gabanta yashiga faduwa da sauri da sauri , tarasa dalilin ummin nakin aurenta da yaya DEENi .
alhalin tasan yana sonta har haka .
,to hakan na nufin ummi tafison yaya yaje waje ya aure wata , sabanin ita kennan .
kawai batayi aune ba taji saukar hawaye nabin kuncinta .
Da sauri tasa Hannuta ta dangwalo hawayen dake bin fuskarta, tana kallo ta girgiza kai kawai tana jin tamkar an diga mata dalma ne zuciya ,.
Ta runtse idanunta ahankali muryarta cike da rauni tace meyasa ...
Meyasa ummi kike son ki ruguzamin rayuwa please ummi ki amince na auri yaya DEENi , Ina sonshi har bansan iya kar kaunarsa a zuciyata ba " bazan iya rayuwa in bashi ba

Fk ya fahimci abinda ummi take nufi shiyasa yace ma DEENi ya dinga kiran yarinyar suna hira. ko km yajata ajikinsa . Ta hakan ne komai zai zo da sauki , fuskasa dauke da murmushi yace ummi idan dan wannan ne ,karki damu , duk wannan me sauki ne zamu tuntubi yarinyar muji , idan bata amince ba Shikenan .

Ummi tace da dai yafiye muku" ba ku tsaya girman kai ba, fk ya sake yin dariya yana girgiza kai yayi mata godiya ya mike .

Jin da Zeenat tayi fk yayiwa ummi sallama ne yasa tayi hanzari mikewa da sauri tashige bathroom din parlour din dake manne da falon nan ta fashe da wani irin kuka ita kam zuwa yanzu tafara jin haushin ummu .

Fk na fita yakira deeni bugu biyu ya dauki wayar , fk yace friend kafara da bani goron albishir ,cikin yanayi na ko in kula deeni yace kada kace min first lov ta saurareka ?

Fk yace ta saurareni km inshallahu zamuyi nasara da alamun ummi ta amince ,.
duk yayi masa bayanin yadda suka yi da ummi ,
yakarasa zance da ummu ta nuna tanason asamu yarinyar a nemi amincewarta .....
DEENi yayi shr sannan yace to ai wannan shine mai wahalar dan bazan taba iyawa ba , fk yace wai kai tsorota kake jine ko yaya ?
,ai take deeni ya hassala a fusace ya aiko masa da wata irin uwar ashariya " wanda yasa fk yayi sauri cire wayar daga kunnenshi ,ya dan duba sai daya tabbatar daya yana kan layi. sannan ya mayar yacigaba magana" haba friend meyasa kake saurin daukar zafi akan abinda bai yakawo ba .

bance dole sai kasameta da kankaba ,ni dakaina zanyi komai.
sai Kuma ya sausauta yana jan numfashi yace ai kai ne da wani zancen baza.
naji tsorota akan me ,raini ne kawai banaso , yanzun dai kai kaje kasameta kuyi magana da in ni nakirata bafa ra'ayinta zanjira ba. umarni kawai zan bata fk yace Shikenan sai na nemeka .
Chapter 12 · 0% Book details