← Book details Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 90

Sashe 73

Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hakan da yayi ne Yasa taji tausayinsa aranta yana sonta baya son ganinta 'cikin fushi da rashin hankali Dan haka ummi tace to Shikenan naji Allah Ya sake Kare min kai .
Take , yaji hankalinsa ya kwanta yayinda jijiyoyin jikinsa da suka tsaya cak suka daina aiki na w wuncin gafi suka cigaba aiki tare da sauke ajiyar zuciya.
Sannan ya numfasa tare da juyowa yasa hannu ya dauki cup coffee ya soma kurba Ahankali ahankali .
muryar ummi yaji yanzu km sai maganar auren ko Dan gaskiya yarinyar 'tana abubuwa masu mahimmanci dazai sa a hada zuri'a daita .

A frigice DEENI yazaro idannu waje coffee daya kurba bai san lokacin daya hadiye da karfi ba.
" ai ko ya sarke shi take yafara Tari kmr ransa zai fita ummi sai faman sannu take jero masa da kyar aka samu tarin ya tsaya ya dago rikitattun idanunshi da suka gama canza kala ya saukesu bisa fuskar umminsa .

yanzu ummi bazata rabashi da zance auren yarinyar nan ba ya fadi haka a kasan ransa yayi shr can kuma yafara magana ahankali yace ummi duk wayannan ababen da kika lisafa akan yarinyar nan nifa ba ko daya da yayi min bawai na kushe zabinki bane " Amman zan aureta da zumar samun ya'ya daga gareta.
Dan a halin yanzu gara na zauna da zeenat kadai na karasa rayuwata daita , yakarasa fadar kmr zai yi kuka .

ummi ta gyra zamanta ta riko hannushi tana sauke numfashi ka amince aje ga iyayenta kennan ?
muryasa a sukwane yace uhm Na amince zan aureta Amman ba Sai kinje da kanki nemar min AUREN SIRRI ba... da kaina zandangana Ga iyayenta tunda oready kina da address din gidansu .

Yacigaba a gsky first love zan dai aureta yarinyar ne kawai badan Ina so ba Sai Dan farincikinki .
km taza zauna matsayin matata sannan ta haifa miki yaran da kike kwadayi samu daga gareta batare da ita kanta tasan da zaman nine mijinta ba Dan sanin nine mijinta zai sa naji some how..'yana gama furta haka yayi Mike yayi waje ranshi a bace zuciyarsa tamkar zata tarwatse tsabar takaici ,ummi tabi bayansa da kallo sarai taji yace a karshe sai dai bata fuskanci inda maganarsa ta dosa ba ta numfasa abinda yake nufi shiyasani damuwarta daya ce ya amince mata da auren yarinyar tunda ya amince ,mgn takare .

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

*Assalamu alaikum warahmatul Allah Ina wa duk masoya wannan labari Na auren sirri fatan alkhari .yayinda duk wani korafe korafenku yake isowa gareni kai tsaye batare da bata lokaci ba say day yana da kyau mu kula mu gane wani abu shi manufar rubuta labari karan kanshi ba wai dan nishatarwa bane da biyyyewa son ranmu . Muna yi ne dan fadakarwa da wa,azantarwa Ga al,ummu ta hanyar da mutun zai samu damar ya gyara kuskurensa .da km Wanda yake da akidar aikata mummunar aiki nasan dawaya masu kawo korafinsu masoya bagudo ne, domin kuwa kaunace Silar damuwarku har takai ga korafinku ya iso har inda nake .bazan iya misalta muku tarin kaunata gareku ba. amman ina son Kusan wani abu kuna 'cikin zuciyar bagudo . Bagudo ni'feyi ju km inshallahu Muna taren tare har abada*🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻

Page 69

Kai tsaye dakinsa ya nufa ya fada kan royal bed dinshi ya kwanta flat yana fidda numfashi ahankali. yayinda , kyawawan idanunshi suka gama rikidewa tamkar garwashi tsabar tashin hankali dayake ciki.
why ...why ummi why did you want's to do this to me?
,meyasa zakiyi min Haka ummi ?
Meyasa kike kokarin son cusawa zuciyarta abinda bata so ?

,bana son yarinyar nan , Bana kaunar ganinta asalima Na tsani kusancina daita domin hakan na jifani 'cikin tsananin tunani da rasa natsuwata.
" bazan iya bijere miki ba ummi ,to meyasa kike so ki tursasani yin AUREN SIRRI da kaskantacciya macce?

tsawon lokaci ya dauka yana kwance idanunshi na kallon celing dakin gabadaya tunaninsa a halin yanzu ya ta,allaka ne akan abinda ummi take son ya aikata .
,yana son umminsa bayason abinda zai disashe farincikinta ballanantana har yakai shi Ga bijirewa
umarnita.bacin ran umminsa ,babban tashin hankalisa ne,a gareshi bancin haka da Babu abinda zai kaishi auran wannan yarinyar may idanuwa tamkar Na mage .
" mtssss yaja tsaki a ranshi Dan duk wannan zance dayake yi yana yinsa ne a zuci .

ahankali ya runtse rikitattun idanunshi banda yana jin bacci Sai Dan yana bukatar maido da natsuwatsa dake kokarin barin gangar jikinsa .

Bangaren nablah kuwa gabadaya duk wata surar dake jikinta ta sauya , ta murje ta sake yin kyau daita Sai dai walwalarta da kuzarinta sunka ragu.
sakamakon matsi da takurar da Zeenat din ke yawan yi mata, Wanda ita kanta tarasa dalilin hakan .
km kwata kwata bata dauki takurar da Zeenat din kemata amatsayin wani aibu ba .

Baya ga tunaninta Haka wasu daga 'cikin masu arziki da manyan masu hannu da shuni sukeyiwa marasa shi km marasa galihu irinta .

Duk da yawan takurar da Zeenat din ke mata hakan bai hanata samun farinciki da walwala daga gurinsu laraba da safeena ba . Dan haka ta tattara Zeenat takurarta ta watsar a gefe tacigaba da abinda yakawota iyakarta daita aiki Wanda tasan dolenta ne Tayi shi Dan abinda tazo yi kennan .

Ranar Saturday ' nablah na zaune ita da safeena a main parlour din gidan sanye take 'cikin doguwar rigar material may ratsin pink and popul yayinda jikinta ke rufe da dan karamin hijab kmr koda yaushe.

babu kwaliyar komai a fuskarta kasancewarta ba ma,aboyaciyar son kwalliya bace da kalekalen zamani, sai Dan Whit lip's din data shafawa lebenta.

,rashin kwalliyarta bai hana ainihin sihirtaccen kyawunta fitowa ba.haka ma kayataccen fatar jikinta choculate colour ta kwance luf. luf..koda take sanye 'cikin ' hijab kyawunta bai boyuwa ba..
Sai dai fuskarta Tayi fayau ..wanda ya nuna alamun rama atattare daita km hakan ya sake fidda asalin siffar halittata kyawun jikinta .

Yayinda kallo daya zakayi mata kaji farar daya tashiga ranka Wanda dama tun asali Haka yanayinta yake 'tana da saurin shiga rai duk Wanda ya daura idanushi kanta , da wuya kangata kaji bata tashiga ranka ba .

bbu kowa a gidan daga ita Sai safeena shiyasa ma ta samu dama ta dan sake ta zauna a parlour Dan bata manta gargadin da matar gidan Tayi mata ba .

Ahankali suke hirarsu 'cikin harshen turanci ita da safeena 'gefe daya km hankalinsu nakan TV .

Salamarsa ce da wani wanda batasan ko waye ba ,ta doki dodon kunneta Wanda hakan yayi daidai da faduwar da gaban yayi , Wanda km tarasa dalili .
dan Kusan duk sanda zata gansa ko jiyo sautin muryarsa Sai ,gabanta yayi mummunar faduwa.

Ahankali Ya karasa shigowa parlour gabadaya fk Na biye dashi a baya .
har zata dago idanunta da niyar kallon inda suke tafasa.
ta maida Hankalinta sosai kan TV dake aiki a parlour tare da amsa sallama aciki batare da ta dubeshi ba Shima Dan sanin mahimmancin sallamar datayi ne Yasa ta amsawa.
" Dan Tasha alwashin bazata km gaida shi ba tunda baya amsa gaisuwa.

Fk yakarasa shigowa parlour Sosai,ahankali idanunsa suka , sauka akan nablah dake zaune Kusan minti biyu ya dauka tsaye yana kallon bakuwar fuskar daya gani agidan ,yaso kwarai ya dauke kansa daga dubanta Amman ya kasa yin hakan.
,a zuciyarsa yake tasbihi Ga ubangijin halitai Dan rabon shi daganin kamilalliyar macce mai tarin kyau da kwarjini irinta ya Dade ,kai shi bai ma taba ganin ba .

Gabanta ya tsananta bugawa da sauri yayinda a 'cikin jikinta ta dinga jin ana kallonta km still har lokacin taki ta yarda ta juyo bayanta Dan tasan deeni ne tsaye .
Sai dake dubanta Wanda bata sanshi ba km tayin hakan ne sbd gujewa kanta wulakanci daga gareshi .

haka kawai taji ta takura a gurin takasa sakewa shanyayun idanunta dake kan TV ta lumshe gabadaya hankalinta baya gangar jikinta ta matsu su bar gurin ko tasamu natsuwar zuciyarta.
, Amman hakan ya gagara samuwa Sai gani tayi ma sun samu gurin sun zauna kujerar dake facing dinta suna cigaba da hirarsu.

safeena ta gaishesu suka amsa a tare amman ita nablah takasa bude bakinta ta gaidasu Sai ma mikewa datayi tsaye 'tana gyara hijab din jikinta Tayi hanyar step .

fk yabi bayanta da wani irin kallo .yana tunanin ko wacece ita a kasan ranshi.shima oga deeni tun shigowarsa zuciyarsa ke kanta Amman ganin yadda Tayi musu banza tamkar bata gansu ba.
, yasa zuciyarsa ta sosu kwarai ranshi ya dinga baci , ballanantana da yaga fk din yayi mata kuriiiii da idanu yana kare mata kallon, hakan ya sake hassala zuciyarsa ,haushinta tare da takaicinta suka taru suka mamaye ruhinsa.

'Tana shiga dakinta ta kwanta ruf da ciki 'akan gado tana sauke ajiyar zuciya wayyo.. wayyo.. Allahna wannan wacce irin maseefa ce take shirin ruguzamin rayuwa ?
meke shirin faruwa dani?

hakika wani mummunar abu Na kusanto rayuwata da Al,amurana gabadaya.
,domin yawan faduwar gabar da nakeyi ta yiwa a tun sanda nazo gidan nan wanda narasa dalilin jin hakan .
Ahankali ta dinga maganar zuci da kanta batare tasani ba .

Ahankali taji an bude kofar dakin safeena ce tashigo ahankali 'tana kiran sunanta .

Ya km Muna zaune Muna hirarmu zaki gudo daki ,kibarnk Ni kardai ?

kefa Naga alamun zaman kadaici baya damunki fa Sai ma Naga kmr baki jin dadi ..

nablah Tayi murmushi yaqe may tattare da takaici kana tace wlh bbu komai safeena km bbu abinda ke damuna , kawai dai Ina son Na dan kwanta na huta ne sbd Ina dan jin bacci ,kafin Aunty Zeenat ta dawo .

Ke dai ki fadi gsky ba wannan ne dalilin dayasa kika dawo daki ba . safeena ta fadi hakan 'tana kokarin zama gefen nablah , nifa Sai Naga kmr shigowar bros ne Yasa duk kika rikece kika kasa zama .

Nablah dake kwance taji gabanta ya sake faduwa jin abinda safeena tace dan Haka a sukwane ta Mike zaune 'tana bin safeena da wani kallon mamaki .
Muryarta a sanyaye tace ko daya ba abinda kike tunani bane ,kawai day Ina bukatar natsuwa ne.
Chapter 73 · 0% Book details