← Book details Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 90

Sashe 65

Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nablah tayi saurin girgiza kanta tare da cewa dan Allah aunty kiyi hakuri wlh na dauka ko mungama aikin ne.

Zeenat , ta sake watsamata wata uwar hararar hade da kallon banza.. wanda hakan ya suka sake frigita zuciyar nabla dake tsaye Amman ta dake batare da tabari Zeenat din ta gane yanayin data ciki ba .

Mtsssssss Zeenat taja tsaki tare da cewa dan Allah malam ni fito ki kije ki karasawa mutane aiki sannan km ki daura min abinci ,Yar isakar baiwa... nablah tayi shr tare da dago shanyayun idanunta tana kallon Zeenat dasu ,yayinda take jin zuciyarta tamkar zata kama da wuta tsabar takaicin sunan da Zeenat din kirata dashi .

Zeenat tace
Kin wani tsareni da idanunwa narai narai kina kallona ko baza kiyi bane ?
a tsanake batare da wata alamun tsoro ko fargaba ba nablah tace zanyi ..
Ok minti biyu kacal nabaki "naganki a kitchen "idan kika kuskura kika bata min lokaci zakiga yadda zan ci ubanki a gidan nan " tana gama fadar haka
ta juya fuuuuuu tasoma tafiya tana kunfar baki.

"Nablah tayi zuru kawai tare da bin bayan Zeenat da wani irin kallon mamaki da alajabi abinda tayi mata.

dan ko kusa batayi tsammani zata fuskanci irin wannan babbar wulakancin ba mai cike da al,mara .

Yau itace aka aiki tajawo aka zagin mahaifinta..abanza uban ta fa aka zaga ,ta furta akan akasan ranta, wato silar ainkinta ne jawo a dinga wulakanta mata uba Haka km ma har da kiranta da sunan baiwa...baiwa fa takirani dashi ta sake maimaita sunan a filli gabadaya abin yazo mata wani iri km abazata" tamkar ba gaske ba.
Anya kuwa rayuwar zata yuwu a Haka tun ba,aje koina ba an fara da zagar mata mahaifnta.
" Anya kuwa zan iya daukar wannan kalar kaskancin da iskanci kuwa ,abinda ta tmbyi kanta da kanta Keenan?

,'ahankali ta furzar da iska ta bakinta tana furta wlh da sake Dan zan iya daukar komai na kunci rayuwa Amman Banda zagar min iyaye .

,

, Mtssss taja tsaki itama tana harara kofar da Zeenat tabi .cikin sanyi jiki ta nufi kitchen .

Ko minti biyu batayi da daura ruwan abincin dare ba Zeenat takaraso ta tsaya a bakin kitchen din tana kiran.. ke....ke.. nablah dake tsaye tana jin Tayi banza daita duk da tasan daita take sannan km taki juyowa ...
Sai ma cigaba da aikinta Tayi.

Sai da Zeenat ta sake maimaita kiranta sannan nablah da ke ..Kusan Sau uku sannan nablah ta juyo a danketa tana kallon cikin idanunta Zeenat .

Zeenat tace ,Yar iska yarinya kawai kina jin mutane suna kiranki Amman dan dakikanci irin naki kika yi shr..ko

nablah ta hadiye bacin ran dataji yana taso mata tun daga tsintsiyar kafafunta ,sannan tace kiyi hakuri basan dani kike ba" sbd ita kalmar ke.. din da kika ce bata daga cikinta sunan nablah....

. eyyyye Zeenat ta fadi Haka tare da ta ware ido tana kallon nablah da mamaki ni zaki kawa rainin hankali , nablah tace kiyi hakuri aunty barainin sense bane a zafafe Zeenat tace yi min shr stupid girl kawai ni zaki kalla kicewa ba sunanki ke ba.... Dan bakida mutunci , to kisani ni daga yau da sunan ke ... zan dinga kiraki ,Dan Allah idan nakiraki dan ubanki karki amsa kiga yadda zanyi dake a cikin gidan nan .. .

nablah ta datse lip's din bakinta na kasa da karfi gaske jin zafin abinda Zeenat tace mata , kusan minti biyu tsakani nablah ta sake duban inda Zeenat ke tsaye har lokaci gabadaya gabobin jikinta sun sage muryarta cike da rauni km Haka kawai ta tsinci kanta da cewa kiyi hakuri aunty .da hannu Zeenat ta katseta .. yimin shr Dan Allah dan bana son sake jin ko muryarki ne .. km ki sauke pot dinan ki daura min indomi yanzu yanzu taja tsaki tare barin kitchen din.

cike da mamaki yarinyar Zeenat takarasa ta zauna ranta a abace wahake take fidda numfashi dan kwata kwata bata taba jin tsanar mai aikinta irin yadda take jin haushin nablah .

Gashin yarinyar kmr bata da wani alamun tsoro atare atare daita .

Cikin mintinan da basu wuce biyar ba ta sauke indomi ta yuye a plate sannan ta sake maida pot din abinci dare kan gas .

zaune ta sameta ta hankice a parlour sai faman cika take tana batsewa tare da hura hanci 'tana kada kafa daya ..

ahankali nablah ta ajiye mata plate din indomi agabanta akan center table tare da kwalbar vitermilk kana ta juya ,tabar parlour .
,banda tunanin da mamaki Zeenat bbu abinda nablah keyi .

ko meyasa ita takasance irin haka ba kmr ummi ba ,mai matsananin son mutane da kyautata musu" km tana lura da irin yadda ummi din ke matukar bawa duk wasu mutane dake shigowa cikin gidan, kulawa ta musamman " sabanin ita wannan bazanr matar mai kama da mutane China .

, 'Ahankali nablah tacigaba da aikinta na zagin Zeenat din aranta sai data gyara koina tsab .

sannan taje tambaye Zeenat din ko akwai wani sauran aikin da zatayi Dan gujewa cin mutuncinta .

,a yatsine Zeenat din ta dago fuskarta tamkar hadari sannan tayi mata nuni da hannuta alamun zata iya wucewa kawai .

jikinta a mace tabar gurin , da kyar ta dinga daga kafafuwanta tsabar gajiya datayi , yayinda idanunta suka ciciko da Hawayen batayi kokarin hana hawayen idanunta zubowa ba,sbd tashin hankali take ciki da wutar dake ruruwa a zuciyarta tana tafe tana kukan zuci yayinda hawayen idanunta ke sake cigaba da bin fuskarta...

ahankali ta hau step daidai conar da zata kaita dakinta.
anan suka kusan cin karo da deeni da ba dan Allah yakiyaye da sai daita tajita a faffadan kirjinsa . sakamakon hannunta duka biyu datasa tana goge Hawayen idanunta ..

daddaden kamshin turarensa ne ya doki hancinta a frigice tayi sauri janye jikina..
Ta makale jikin bango batare da tasan Tayi hakan ba , jikinta ya dauki rawa kirrrrrrma hawaye km sharrrrrrr suna sake bin fuskarta ido cikin ido suke kallon juna ,itace ta soma janye idanunta ta ta runtse gam tana jinra kawai taji saukar mari ..
, tsayawa yayi cak Shima yana karemata kallo up and down .

A tsorace tasa tafin hannunta duka ta rufe fuskarta dashi.. kijinta na sake daukar kirrrrrrma .

'Ahankali ya ja wani irin mugun tsaki mtsssssss wanda hakan ya sake jefe zuciyar nabla shiga cikin rudani .

, yana tsananin jin haushi yadda yarinyar ke behaviors kmr wata dakiykiya ..
harara ya zabga mata kana ya sake jan tsaki sannan ya yasoma taka step . tana jin takunsa har sai da yakurewa step din Sosai sannan ta bude idanunta da sauri ta fada dakinta tare dannawa kofar key ..

.ta fada kan gado takarasa fashewa da wani sabon kuka.... Mai cin rai blaming kanta kawai take ta yadda tayi sanadin jefa kanta cikin meyakawoni matsala.
, meyakawoni cikin wannan gidan ?

meyasa na kawo kaina cikin halaka irin haka ?
anya kuwa nayiwa kaina adalci Dana zabarwa kaina irin wannan rayuwar ,mai cike da kaskancin da wahala ..
Anya kuwa zan iya cigaba da yin wannan aikin kuwa ? Haka ta dinga jerowa kanta tambayar iri iri batare da tasan abinda yakamata Tayi ba ..
yanzu irin rayuwar da zanyi kennan?
..Ta sake jeho kanta tmby.
agigice tatashi zaune ta jingina bayanta da jikin gadon dakin tare da zubawa celling dakin Ido tana tunanin abinda yakamata tayi "shr yabiyo baya na wani dan lokaci .

tuno auntynta datayi ne yasa tayi saurin sauke ajiyar zuciya, Dan tasan ita kadai ce zata iya fidda ita a wannan halin wulakancin datake ciki , batare wata matsala ba. ai aikin bai zama dole ba , da sauri ta hau goge Hawayen fuskarta tace zan kwantar da hankalina na zuwa wani lokaci "kafin nasamu yin waya da auntyna . ahankali ta Mike tashiga bayi ta dauro alwala sallar magrib koda ta idar ma bata tashi ba sai datayi isha'i a gurin .
, bata bi takan komai ba dan ko abinci bataji zata iya zuwa ta sakawa cikinta ba .
ballallantana ta hadu da hawan jini ,da ciwon ulcer wato deeni da Zeenat .

,Ta kwanta anan ta dunkule jikinta cikin hijab tare da lumshe idanunta kawai" duk da ba wani bacci takeji ba, ahankali tarinka jin yadda zuciyata tasoma beating dip....dip.... kafin daga baya tashigayi da sauri da sauri sakamakon tunowa da Mr horo datayi ...
"Tarasa dalilin dayasa duk sanda tayi arba dashi ko ta tuno shi take shiga cikin tashin hankali, ba.
, addu'a tasoma aciki. zuciyarta ya Allah...ya Allah kamin tsari dashi da duk wani wani shirin dake tattare dashi . Allah idan zama acikin gidan nan alkhari ne a rayuwarta Allah kasamun natsuwa da hakuri zama da matar gidan .
,idan km bbu alkhari Allah ka fidda cikin kowace irin maseefa cikin sauki . haka tayi tayi yan addu'oita , har taji zuciyarta ta dan samu natsuwa daga tashin hankali data shiga na wuncin gadi ,daga karshe bacci mai nauyi yayi gabadaita.

Acan kasa kuwa DEENI ne kwance akan thrre sites hannunsa rike da remut yayinda zeenat ke zaune a gefenshi suna hira ,rashin ganin nablah yasa duk ummi ta damu har . takai ga tambayar zeenat ita , ummi tace ni kuwa ina yarinyar nablah take ne har yanzu banga saukowarta ba ko lafiya?deeni dake zaune yaji gabansa ya fadi zuciyarsa tashiga harbawa .

" zeenat ta Dan yatsina fuska kana tace wa ummi . ai tun dazu kafin ki dawo ta sauko taci abincinta ta koma dakinta dayake fita ummi tayi ,yau . Ummi ok na jita shr ne .sannan tacigaba yabon nablah yarinya mai hankali wlh .
Zeenat taji magannun ummi na neman saka mata ciwon kai ,ta barta da karyar data ,sharara mata ta ba gaira ba dalili .
Chapter 65 · 0% Book details