← Book details Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 90

Sashe 57

Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

haka ma ta bangaren Ummi itama hankalinta a tashe yake da yadda take ganin yanayin diyar tata.
,shi kuwa gogan sam bbu ruwanshi da wani tashin hankali da suke cikin .
' hakar gabansa kawai yake domin komai yana tafiyar masa yadda yake so daga office har gida .

Sakamakon damuwar da zeenat tasawa ranta ne har hakan yajawo ta Dan rame kadan kallo daya mutun zai mata yagane tana cikin tension .
" Ko school ma sai da wata friend dinta may suna halima ta gane Tana cikin damuwa dan haka tmbyeta ,zeenat bata wani boye mata komai dangane da halin datake ciki ba .

,nan fa halima tace Ina ai baki Ga ta zama ba zeenat kishiya fa ....Ai ni ko sunanta ban kaunar ji ballanantana tashigo min gida gaskiya kitashi tsaye tun wuri , zeenat marairaice murya hali bansa yadda zanyi ba ,bansan koina ba , hospital kawai nasa km muje ,hali tace ok kada ki damu akwai wani mutun danasan yana bada maganin haihuwa ,kibari zan rakaki gurinsa amman a sango ota dake hanyar abe okuta yake ,idai zaki zan rakaki ,zeenat najin haka ta kamo hannunwan halima duka cikin hannuta Tana murna dan Allah hali kitaima min koma Ina ne zani indai zan samu cikin haihuwa nidai banason mijina yayi min kishiya dan bana kaunar zama daita a rayuwata ta duniya km nasan rashin haihuwar nan zai iya bawata shigo min gida .
gara mutuwata danaga zuwan wannan rana.
,hali tace haba kada ki damu zan taimakamiki ai murigada mun zama daya .
Nan fa suka bar zance da zumar gobe zasu tafi songo ota .😭😭😭

Washegari kuwa da wuri zeenat tashirya har Ummi tacewa yana Ga yau kinashiri cikin sauri haka.
Murmushi Tayi kawai Tayi wlh , Ummi lecture gareni da wuri shiyasa kika ganni haka.
Ummi tace ok , koke fa haka nake son ganinki cikin walwala da kazarkazar tattare kwanciyar hankali .
,banason ganinki cikin damuwa zeenat ta sake yin murmushi tare da cewa Ummi sai ta dawo Ummi tayi mata addu'a .

Haka suka je gurin may bada maganin Ita da hali batare da sanin kowa ba .
Bawani abu mutumin yabata ba, baya Ga garin magani baki yace ta da lemun tsami ta dinga da sha da zarar sun gama sex da mijinta har sai maganin yakare har yana sake tabbatar mata maganin bazai kai Ga karewa ba zata samu ciki . Uhmmmm

da murnarta dawo gida km Tayi kmr yadda mutumin yace Tayi.
,tare da zaman jira tsammani , har zuwa lokacin zuwan period dinta, bata Ga jini ba , .

Tacigaba da shan magani ,murna kuwa kmr ta Yaya ,dan duka tunanin ciki gareta amman byn kmr sati daya da shanye maganin sai Ga jini ..
ranar kuwa data Ga jinin zaman dirshan Tayi a bayi "tare da daura hannuta duka bisa kai ta saka kuka a gurin .

,wunin ranar bbu inda taje ko parlour kasa bata keko ba , , Ummi zaune ita da DEENI wanda Bai dade da dawo ba zaune yake kusa da ummi suna hira ,ganin shr shr bata zeenat ba yasata zuwa dakinta , da fari ta dauka ko bacci take ,ganinta kwance tana sheshekar kuka ne yasa gaban Ummi faduwa da sauri takaraso inda take kwance Tana kiran sunanta ke zeenat.. lfy ki kuwa ,kukan me kike haka ?

Aiko zeenat naganin Ummi ta sake rushewa da wani sabon kuka km tashiga gayawa Ummi abinda ya faru amman sai dai ta boye bata gayawa Ummi zance zuwa gurin amso magani ba .

Allah sarki Ummi baiwar Allah haka ta dinga rararshinta Tana kuka itama. jin shr yayi yawa ne yasa DEENI biyo bayan Ummi yaga ko lfy aiko yaga abin mamaki dan zaune ya tadda ummi yayinda zeenat din ke rungume ajikinta suna aikin kuka tamkar wayan,da akayiwa mutuwa mai zafi.
Yana ganin haka yasan iskancin zeenat din ne ya motsa ,dan haka bai wani damu ba ko tada hankalinsa.
" dan yasan zance gizo baya wuce na koki ,sai ma tsawar daya dakawa zeenat din ..Tare da nunata da yatsansa daya ke....... banson wulakancin da rainin hankali fa yazaki zo ki tasa min uwa gaba da kuka?
Ke...duk matsalar ki sai sanya mutane ciki.

" kinsa Allah idan baki daidaita kanki da kyau ba zan iya ra.....
Ummi ta katseshi ta hanyar taga masa hannu ,ya isa haka bana son jin komai .
km ni ai baita ce tasani kuka ba, Tayi missing din kwanakin period dinta ne so shine da shirmenta ta dauka ko ciki ne da Ita ,sai km Ga period din Ta yazo .
" kasanta da shririta shine ta zauna Tana kuka ,ni km tausayi tabani ,Ummi na kaiwa karshen maganarta , DEENI ya watsawa zeenat din harara ,yanzu ne kika damu da haihuwa ko da kika ji zance abinda kika fi tsana a rayuwarki ?
Kinsa Allah zeenat ki fita daga idona kada ki kashe min uwa da matsalarki .
,kikasa wasa ma wlh me gabadaya zanyi in yaso ki mutu gabadaya na huta da matsalarki , km bbu abinda zai faru Dan duniyata zan cigaba da ci hankali kwance byn baki raye .
kinga karshen kishi kennan.... zeenat najin haka ta fashe da wanj sabon kukan Ummi kina jinsa ko .....so yake na mutu yakara aure sbd ya daina sona ...sai km Hawaye sharrrrrr .

Dakuwa Ummi Tayi masa da hannuta ungo nan DEENI wani irin rashin imani ne haka ,kake nuna mata , rashin son nata har yakai ka dinga yi mata fatar mutuwa km a gabana DEENI... ko kunya idanuna bakaji ba .
To inshallahu ta Allah bataka ba km bbu wata mutuwa a fuskar diyata km haihuwa zatayi shi da yarda Allah .

Zeenat fa tashiga neman haihuwa zanga zabga tamkar zatayi hauka duk inda taji ana bada maganin haihuwa sai karfa taje ba .

har gurin wata sabuwar malama datazo Lagos wacce ake Kira da malama shema,u taje neman magani haihuwa.

wanda mutune sukayi ittifaki akanta muguwar Yar damfara ce daga Yola take ,da farko Kano ta fara zuwa tana Dan farar mutane mlm aminu Ibrahim daurawa ya fatattakota ,shine tayo garin Lagos . Nan ma dai zeenat taje bbu wata nasara data samu sai kudinta data kashe .

Cikin haka maganar da mama ta abuja Tayi akan kara auren DEENI taje Ga kunne big Dady , musamman yasa tazo daga abuja km ya nuna mata sam Bai ji dadin abinda Tayi ba.

,inda ma shi DEENI din ne da kansa yaso kara aure wannan dadan bbu may hanashi amman tace lallai sai ya kara aure akan wata lalura ta matasa ko wani dalili na dabam , hakan baiyi ba dan haka bayason a km tadda zance .

Wannan batu da big Dady yayi da km daurin gidin Ummi da take dashi yasa hankalin zeenat din kwanciya .

Cikin dan kankani lokacin ta maida kibarta Tayi fes daita ta dawo da gayunta kmr da.

A cikin wannan lokacin ne latifa takira Ummi tasanar daita cewa an samu mai aiki karama Yar shekara gamo shabakwai ... yanzu haka jakar kayanta a gidanta ya kwana Amma ita bazata samu damar zuwa ba ,sai dai zata turo mata da number yayar yarinyar takira ta ,tabata address din estate din murna fall cike da zuciyar ummi tace badamuwa turo min yanzu yanzu ,kinji diyarta....ummi na sauke wayar sako yashigo tana dubawa taga suna kmr salmah Tare da number .

Uhmmmm muje zuwa
Fans 😃😃😃😃😃😃😃

*Please kuyi hakuri da rashin jina two days uzurirrika gareni ,da suka Sha kaina amman karka danu zuwa anjima nasamu time zan suburbudo muku one page more kusha sha'aninku, dashi lov you ol gyus*😍😍😍😍😍

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Page 59

Al'amarin gidan kuwa gabadaya ya sake canzawa tun daga kan mutane dake rayuwa a cikin gidan har zuwa Ga gidan karan kansa .
Dan gabadaya DEENI ya gyara kowa Ina a gidan inda ya sake fadada girman dakunan dake kasa tare da kawatasu da ado .
Wanda ,a halin yanzu yakoma amfani da dakin sama da kasa .kallo daya zakawa gidan ya birgeka km kasan ya fita daban da sauran gidanjen dake cikin estate din.

Ummi bata Kira number Salmah ba sai byn data sallami shafa da kwana biyu sannan takirata

Ranar da shafa ta tarkata tabar gidan ranar itama Zeenat tashi da zumar dawowa dakinta na kasa wanda DEENI ya cire mata ,dan haka bata tsaya wani bata lokaci ba tasa laraba tayi mata komai ,tare da abubuwan ta masu mahimmanci sai abinda baza'a rasa ba tabari a dakin sama .itama takoma amfani da daki biyu a cikin gidan.

Matashiyar budurwa ce Tare da yayarta tsaye abakin titi .
suna jiran mota ' sun dauki sama da rabin awa tsaye a haka suna jiran abin hawa amman kowace mota tazo wucewa" cike take tap da mutane .
,sakamakon cunkoson ababen hawa da aka tashi dashi a garin Lagos.

, aunty me zai hana muhau machine ne , kinsa fa inda zamu da Nisa sosai .
, saboda ke da zaki dawo .
Dan naga yanayin garin yau sai a slow inji cewar nablah.....

, aunty Salmah ta dan juyo ta kalli gefen inda sisinta ke tsaye tare da cewa 'shikenan nablah muhau machine din kawai Dan nima bana son dadewa .

gaba kadan suka karasa wajen yan machina,
malam dan Allah lawansi bustop zaka kai mu, inji cewar aunty Salmah.
mai okada ya gyara tsayuwar machine dinsa ta yadda za su samu damar hawa ..

Kin hawa aunty salma tayi sai ma tmbyr mai okada take da nawa zamu bayar tukun.

, Atakaice dai muna kai mutun daya a naira dari mutun biyu dari da hamsi aunty Salma tace Shikenan ke nablah fara hawa.
" dayake kaidar Aunty salmah kennan.
muddin da kanneta zata hau machine bata yarda tafara zama a farko, sai dai tace su hau gaba ita km ta zauna a baya.

'Ahankali Suka dane machine"
dai dai bakin filling station din dake lawansi, suka sauka aunty Salmah ta bude jakarta tabawa Dan okada kudinsa .

tafiya suka soma yi zuwa inda zasu shiga motar da zata kai su surelere .
Chapter 57 · 0% Book details