← Book details Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 90

Sashe 11

Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kar kice min duk akan son DEENI kike neman yin fada da er'uwarki . Saboda Allah Ke ko kunya abinda kika aikata baki ji ba .
" zeenat tayi shr takasa cewa komai dan ita kadai tasan yadda take jin zuciyarta, .
Ummi tace meyasa zeenat , meyasa bakya jin maganata ne ,irin abinda zaki min kennan ko wannan shine kalar tarbiyar dana baki uhmm ?
kina ganin haka kawai zanki amincewa da auranki da DEENI " kiyi tunanin mana .
koda yake baki san ciwon kanki ba shiyasa.
' ballanantana" kisan gata neke miki .

mutumin da bai san da zamanki ba, bai damu dake ba" ko kallon arziki baki isheshi ba" shine zaki zauna kina westing din hawayenki akansa takarasa fadar maganar tana takaicin zeenat,.
" Ummi ta sake maida dubanta sosai gareta tana mamakin yadda zeenat din ta canza cikin lokacin kadan . Alhalin ita duk iya lokacin ta dauka tare da yarinyar bata taba ganin irin haka atattare daita ba
cikin kuka zeenat tace ummi kinki amincewa da aurenmu yaya DEENi .
ai gashi nan ai ...... sai km tayi shr" dan jin kunyar abinda take kokarin son fadi "dan haka tacigaba da sheshekar kukanta,.

" Ummi tace uhm Ina jinki kikarasa mana , tace wlh wlh idan kika kuskura" kika bari yasan kina wannan" haukar akansa " kin shiga uku da wulakanciinsa " .

zeenat ta zube nan kasa tana kuka hade da kamo kafafun Ummi .
tace dan Allah Ummi ki Amince da maganar yaya kinji "wlh ni Ina sonshi a haka " kiyi mana addu'a kawai" bbu abinda zai faru inshallahu .
Ummi ta sake zuba mata idanun tana kallon sarautar Allah, da rashin kunya irin ta Zeenat , su fa daman yayan zamanin nan ba wata kunyace ta ishe su ba .

,ummi tace" da bai ce yana sonki ba fa ?
Ta jeho mata tmyr " data girgiza zuciyar Zeenat " din" tayi kasa da kanta tana zubda kwalla ita fa ganinta bbu abinda tayi .
a ranta ko cewa tayi ai shima yana sona tunda ya iya furtawa .

Ummi ta sake kiran sunanta tace zeenat idan bakiji kunyata" ta matsayina ta mahaifiyarki ba " ,
Ai kya ji kunyata ta ummin DEENI .
amman tunda kin nacewa auren DEENi km kinji" kin Gani to wlh duk abinda kika Gani Shikenan , .
da ma sharadi kozan amince da auranki dashi .
Banda zuwa kawo kara kum duk abinda yabiyo baya babu ruwana ciki sai dai ki haye abinki tunda shi kika zaba .
da sauri zeenat tace to....ummin indai kin amince bbu ma abinda zai faru sai alkhari .
Wani irin kallo Ummi tabita dashi wanda da Gani kasan na tausayi ne.
Dan yanzu ta daina mamakin duk abinda zatayi .
da murna ta tashi ta koma bedroom tayi kwanciyarta tana jin dadi Ummi ta amince da aurenta da yaya DEENi . idanunta ta lumshe" tana jin Yadda soyayyar DEENi ke sake huda zuciyarta .

Yinin ranar da murna zeenat tayi shi cike da tsantsar farinciki ga tarin tunanin DEENi dake sake mamaye kowane part na jikinta yau tazo mata da abubuwa masu yawa bacin rai da farinciki .
duk abinda takeyi Ummi na hankalce daita . kallonta kawai take tana binta da idanu .

Washegari zeenat" ta zaci ummi zata sanarwa yaya DEENi cewa ta amince" sai kurum taji ummi ta share da zance gabadaya , koda dai da wuri yake fita ,.

wasa wasa ummin ta share da maganar kwata kwata garakar gabanta kawai take , .
tana jin lokacin da dama idan yaya DEENi ya dauko mata maganar zata katse shi tace kar ya dameta ya rabu daita .

sai dai abun yana damun zeenat matuka yadda kullum yaya DEENi ke sake daure mata fuska da wulakanci iri iri. Amman takan masa uziri ganinta killa sai lokacin da ummi ta amince masa ' sannan zai daina nuna ko in kula dayake ,mata.

shi kansa yaya DEENi baisan cewar zeenat din tasan da zance ba. kullum dai ya shigo wajen ummi sai yayi mata nacin ,shifa yana nan yana Jirata.
ita km tace kar ya dameta bayace yafi son Yar jami'a ba .
"to yaje ya nema Amman ita sam bazata bashi diyarta ba , .

yana fita zeenat ta matso sosai kusa da ummi tace ummi dan Allah bakince ,kin hakura ki amince tunda na yarda ba .

sai ummi ta dube tana watsa mata harara tace sakariya bazan kawai".
kalli fa ko kallo arziki baki isheshi ba .Amman duk kinbi jin tsamgwami kanki .dan fitina tsiya da jaraba , .
ni duk abinda nake Ina yi ne "dan Kare matuncinki , ba dan Ina kin aurenki da DEENi bane .

tunda yashiga dakinsa bai sake fitowa ba" sai dai yatashi" yayi sallah kawai yakoma gado .
yasawa ranshi, cewa ya hakura daita kwata kwata dan baiga dalilin da zai sa shi ya dinga batawa kansa lokaci ba .

Kwance yake akan makeken royal bed dinshi ya rufe kanshi cikin alky blanket mai matukar taushi ,.
bacci yake Sosai hankalinsa kwance ya rufe koina na jikinsa banda fuskarsa saboda yanayin unguwar su mai dauke da sanyin ni'ima ,.

ahankali ta bude Kofar dakin" kwance ta ganshi, yana sharar baccinsa ,sai yanzu hankalinta ya kwanta gangar jikinta yasamu natsuwa , kusan kwana biyu kennnn rabon data sashi a idanunta,.

ahankali take daga kafafunta har ta isa inda yake,. kwance
idanunta ta zuba masa" tana kare ma kwakkywan fuskasa kallo yadda tayi kyau tana fidda annuri na musamman .
Ahankali ta lumshe idanunta " tana jin wani irin tsanyi nabi jijiyoyon jikinta.
Ahankali ta bude idannuta suka sake sauka akan beautiful face dinshi ,.
fuskarsa ta kurawa ido har wani kyalli kyallin kyauwu take fitarwa , cikin rawar hannu takai hannuta gefen fuskasa ta dan tashafo . wani irin taushi taji wanda ya sake dulmiyar daita a duniyar kaunarsa .
Take taji koina na jikinta ya mutu sai wani yammmmuu take ji.
ita kanta tarasa dalilin dayasa take jin haka ajikinta .
ganin bacci yake sosai yasa ta juya ahankali tabar dakin cike da shaukin soyayyar DEENi dama Ummi ce "tace ta dubashi dan har lokacin fitarsa aiki na neman wuce .

Koda ta sanar da Ummi cewar bacci yake har yanzu, yasa ummi ta nufi dakin" dakanta kusa dashi taje" kai DEENI sai data kira sunanshi" kusan sau biyu" sannan ya dan bude gengerous eyes dinshi ya kalleta dashi "tace lafiyarka da har yanzu dabaka tashi ba , .
tacikin blanket din ya dan yi Mika hade da salati sannna ya dan gyara kwanciyarsa yace lfy first lov ,natashi har nayi sallah " to bazaka aiki bane yace zani.

Ummi tace Ina jiranka idan kagama.
ya amsa mata da kai kawai .
a hankali ya zame jikinsa daga cikin blanket din , daga sai dan gareni wando Mika ya sake yi yasa hannunsa ya gyara jijiyarsa dake mike .
Sannan ya shiga bathroom,.
duk da yamakara hakan bai sashin yin sauri ba, wanda normally haka yake da sanyi jiki .
wanka yayi, ya fito. ya shirya cikin kakinsa da suka dace da surar jikinsa, har ya murda handle din kofar "dazata Kai shi parlour ya tuna Yayi mantuwar wasu files a dakin baccins" dan haka yakoma ciki daukowa .

Tsaye take a bakin kofar dakinsa tafi kusan minti biyar a wajen tana saka dawarwara yadda zata sake shiga Bedroom din sa.
ummi ce tasake aikota .
Ta dubashi dan taji shr har yanzu .
tana son tayi nocking Amman tsoro da fargabane suka hanata .
daidai wannan lokacin DEENI ke shirin fitowa daga part dinsa . ta daura hannuta kan handle din kofar.
ai agigice cikin matsanancin tsoro tasaki wani irin kara da tasa DEENI , tushe kunnuwanshi " da duka hannushi "ai batasan sanda ta fada saman fadaden kirjinsa ba .
hade da runtse idanunta gam dan tsabar jin tsoro , batasa abinda zai mata ba Jira kawai take taji saukar mari dan gabadaya tagama frigicewa.
Amman abin mamaki sai taji sabanin haka.s shiyasa tasaki jiki ta sake narkewa a fadadden kirjinsa tana shakar dadeden kamshin turarenn jikinsa mai birkita mata tunani "a duk sanda ta Shaka .

wani irin ya dinga ji ajikinsa, yrrrrrrrrrrrrr.... yrrrrrrrrrrrrr abinda bai taba faruwa dashi ba kennan" jikinsa ya hadu da wata macce" shi tunda yake ma ko hannun macce bai ta ba rikewa ba ballanantana yakai ga hada jiki .
Ya dinga jin wani irin wani irin a gangar ajikinsa.
gabadaya tsigar jikinsa suka mike tsaye , yaji da zai iya " rungume zai yi kawai zaiyi .
ko zai ragewa zuciyarsa radadi da ciwon dayake ji.
Amman Ina... Sam bazai taba iya aikata hakan ba .
ganin yadda tayi lamo ajikinsa ne yasa, cikin takaici ya bambareta daga kirjinsa cikin tsanyi jiki,
tsayuwa ce ta gareta , zuciyarta ke neman tarwatse tsabar tsoro da rikincin data tsinci kanta ciki.
,ko ta kanta bai bi ba ya tsuke fuska yana kallonta ,itama idannuta ta zuba masa ko kiftawa batayi.
ga wani irin tsoransa dake lugudar zuciyarta.

ahankali muryasa a sanyaye yace malama ki daina min "irin wannan kallon na munafurci .
in ba haka na kwakule idanun rashin kunya tsaki yaja hade da bin gefenta yazagayeta ya wuce kai tsaye part din umminsa yashiga" sai dai bai ganta ba,.
dan haka ya wuce main parlour 'dan yasan tunda bata dakinta, tana can .

zaune yasameta tana yin breakfast fuskarsa a dan sake yakarasa har kusa daita ya zauna yace gud morning my first lov, ta dubeshi fuskarta dauke da murmushi tace morning dear ,kata tashi lfy girarsa ya dage mata.

cikin tsnayin jiki zeenat takaraso wajen, kallo daya DEENi Yayi mata yasa ta canza hanya batare da ta sake kallonsa , kan wasu kujeru dake ajiye a gefe ummi tabishi da kallo batare da tace masa komai ba " da kanta tayi savice , din shi ,shi km sai wani zuba mata shawaba yake , .
coffee kawai ya iya yasha, ya mike tsaye cikin hanzari sakamakon wayarsa data dauki kara yana dubawa yaga ogansa ne daga wajen aiki .
dan haka yayiwa umminsa sallama da hannushi ya fice wayar manne da kunnenshi .
Chapter 11 · 0% Book details