← Book details Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 90

Sashe 58

Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna tafi suna hirarsu abin sha'awa har suka isa wajen shiga motar Masha.

, daidai Bakin get din da zai kai ka ilori Street suka sauka , tafiya kadan sukayi suka isa inda zasu .

aunty Salma tasa hannu ta tura get din gidan wanda koda yaushe haka yake a bude, .

Da sallamarsu suka karasa bakin net din latifa . Aunty Salmah na kwalara mata Kira latifa latifa.. Amman shiru ba amsa yayinda kofar ma take a kulle .
Tsayuwar Minti goma sukayi kafin daga baya suka jiyo sautin muryar latifa .
ku biyo ta nan kofar kitchen,an kulle nan ne sbd yara .
" zagayawa sukayi ta kofar kitchen suka shiga.

Latifa naganin su tasaki murmushi ,kai kai gsky dai Salmah kunyi latti wlh kin kuwa san nisan unguwar da zaku kuwa ?

aunty Salma tayi dariya wlh kinsa halin mutumin naki hukuma ne sai da rarrashi .
duk shi ya bata mana lokaci , gashi Bai fita da wuri ba.

, to shikenan sai kuxo Ku tafi tun rana batayi ba . "ai ma hajiyar takirani tun sassafe tamin kwantance yadda zamuje can din " da ,na so mu wuce ta mushi ne saboda akwai mota mai zuwa can direct sai dai kinsa jakar nablah na nan shiyasa dole sai munbiyo tanan din .

Latifa tace ok ina zuwa ku shiga daga ciki bari na amso sako dana aika .

dan Allah kiyi sauri ba sai munshiga ba .

ina jakar take saboda kar lokaci ya wuce ?latifa ta kwallawa mai aikinta kira... ke uzaima ...
"uzaima ta amsa tare da karasowa ,Gani aunty jeki dauko jakar nablah a karkashin step yanzu .

Sannan taje tasamu yaron mijinta da ta aika tun dazu ATM tace ibrahim ya'akayi ne ,ya tura hannu ciki aljihun wandonsa ya ciro kudi masu yawa ya mikawa latifa Tare da ATM a saman kudin tace yauwa na gode.

har ya juya ta kiransa ya dawo , akwai wa'yanda nike son ka dan kai mun su inda zasu samu motar zuwa obalende .
, yace to badamuwa ,ta koma ciki inda ta tarar har an dauko jakar nablah ,latifa taciro dubu biyar ta mikawa Aunty salmah gashi kikara kuyi kudin mota dashi ,saboda yanayin hanya .

aunty Salma ta amsa tayi godiya, hade da yi mata sallama .
bakomai sai kin dawo mayi waya duk abinda ake ciki Kya sanar min ni dai addu'ata Allah Yasa tayi musu ..

Kai tsaye inda zusu samu motar da zata kai su obalende ya, ajiye su .

, Suna tsaye cikin mota BRT dayake standing suka samu , Aunty salmah tace nablah ajiye jakar kayanki ki zauna akai .
Sannan kiciromin wayata a jaka ki duba dealing zakiga wata number MTN karshenta 12 kikiramin ,ki mikomin.

,haka kuwa nablah tayi tare da Mikowa Aunty salmah wayar .

ta manna wayar a kunneta tare dayin sallama. hello hjy gamu cikin motar obalende daga nan wace motar zamu shiga" daga can bangare ummi kuwa cewa tayi yauwa inkunzo ku hau motar mai zuwa aja sai ku sauka (a jakonde first get).
ai kinsa lekki ko?

" aunty Salmah tace A,a bansan side din ba , ina dai jin sunan waje.

Ok .. inda kun sauka a first get din kiyi flashing dina.
Aunty salam ta, ajiye wayar..

Bayan kmr awa daya da rabi sai gasu jakonde first get...

Kiran ummi suka sake yi kmr yadda tace .
ok kuyi crossing main road ta hannuku na daman zakuga sambord an rubuta lekki road hanyar zaku biyo layi na uku .
daga hannun hagunku in kun kai kikirani

,nan dai suka sakeyin tafiya minti goma suka sake kiranta byn ta dauka ne tace kuna kan layin ne?
Aunty salmah tace Eh to zakuga cona ta hannun hagunku zakuga wani babban church ,dan suna tafiya ne suna waya da ummi tana basu direction .

Aunty tace ga church din nan ma mungani to ku tsaya a wajen zaki ga get opposite din shi .aunty Salmah tayi saurin cewa shine.

PLASNUW ROWS FAMILY ESTATE ?

Ummi tace yauwa shine kin iya rubuto?
Sai da Aunty salam tayi murmushi sannan tace ba laifi .
ok bani minti biyu na kira securities din get din.
" za su tambayi sunanki aunty salam tace to ....

Nablah ta zubawa hadadden get din gidan idanunta kawai wanda basan yadda zata iya kwatanta girman sa ba ballanantana tsawonsa .

sai dai zata iya kiran get din da JAMA GET ..wato na gidan bursunan dake garin Lagos KIRIKIRI .

daya daga cikin securities din get din ne ya dan leko ganinsu tsaye ne yasa shi cewa madam can i help you?
who are you, looking 4 duk a tare ya jehowa auty Salmah tamyr dayake itace kusa dashi.
,
the person we are lokin 4 said we should Wait 4 her "inji cewar aunty Salmah mutumin yace or rigth sannan yakoma mazauninsa "

can ya sake lekowa yace are you salmah ?
"auty Salmah ta daga masa kai .
'yace ok you can come in.
tare da bude musu Dan karamin get suka shiga ya nuna masu ,wani gurin yace inter and rigth ur ful name down
,Can u write ya sake tmbyr Aunty Salmah.
tace Eh.
byn sunyi komai har da sign sannan ya sake bude wata kofar yayi gaba yace su biyo shi a baya.

daidai wani katanfarin gida mai dauke da tampal ,wanda duk gidanje wajen kusan haka gininsu yake iri daya Kuma sun kai guda hamsi a jere , banda new buildings da ake sakeyi km kowanne gida da number a jiki,..
no 20 ya nuna musu da yatsansa yace this is the place sannan ya juya.

Ahankali suka isa ga kofar daya nuna batare da bata lokaci ba sukayi nouking, wata mata ce da bata wuce ki mananin shekaru ashirin da takwas zuwa talatin ba tazo ta bude musu kofa hade da yi musu sannu da zuwa.

wani hadaddin falo may maseefar kyau ya kawatu da kayan kwalliya wanda yasha kyau ya gaji da kayan more rayuwar duniya .
, sukashiga hade da yin sallama , ga wani kamshi na musamman dake tashi ta koina a parlour, wani irin sanyi ne ke ratsa musu tsantsar jiki .
take duk wani zafi rana da gajiyar hanyar da suka debo suka nemata suka rasa ...

wata dattijuwar mace ce zaune bisa kujera dake zagaye da parlour ,hannunta rike da waya, duk da ba wai saninta nablah tayi ba Amman take jikinta yabata da ita suka dinga commincating a waya da auntyta .

kallo daya nablah da ummi sukayiwa juna" take gabansu yashiga faduwa a tare zuciyoyinsu ya amsa dummmmmm na minti biya kafin daga baya ya dawo daidai.
,wani bakon al,amari ne , yashige su a tare wanda dukkansu basu san dalilin jin hakan ba. a wannan kallo da nablah tayiwa ummi ne, tagane yadda take jin dadin duniya .
Ga km tsabar jin dadi da hutu na musamman da ya bayyana a jikinta .

Gaban nablah yacigaba da faduwa yayinda Koina na jikinta ya dauki kirma .... musamman zuciyarta da taji tana dokawa da sauri.

Da fara,ar ummi ta tare su ,tana musu , sannu da zuwa tare da nuna musu wajen zama da hannuta zama sukayi suna gaida ummi .

sannuku.. kunsha rana Amman Kuma kunyi sauri wlh ai nayi mamakin da kika ce kuna first get.

aunty salam tayi murmushi sannan tace nima wlh haka nagani .
,yayinda ita km nablah ke zaune abunta Tana raba idanuwa tare da karewa koina na parlour da kallo .

Ajiyar zuciya kawai Ta dinga saki 'ahankali 'ahankali domin , irin gidanje datake gani a TV ne wai yau take zaune acikinsa, km har zata zauna a cikinsa ta cigaba da rayuwata zuwa na wani dan lokaci , .

'Ahankali ta maida shanyayun idanunta inda ummi ke zaune tana sake dubanta da kyau , girgiza kanta kawai Tayi tare da yin zance zuci, cikin haka ta tsinci kanta da yi musu addu'ar hakika wasu sun zo duniya a sa'a, Allah yasa lahirar su tayi kyau 'ahankali ta maida kanta kasa ta sunkuyar tana wasa da Zara zaran yatsun hannuta masu matukar kyawun gaske.

Suna nan zaune a gurin aka shigo musu da abin sha ,ruwa ne may tsanyi da malt sai kayan fruit wanda suka dauki tsanyi suma.

, km duk nablah Tana ganin hakan ne a zahiri aka ajiye agaban su, hjy ta gyara zamanta tare da kiran sunan aunty Salmah .... salmah ko?
Aunty ta dagawa ummi kai kawai .
, wannan ita yarinyar kennan?
murya auty salmah ne ya daki kunne nablah .
eh itace hjy .

'Ahankali ummi ta saki ajiyar zuciya sannan ta dauki wayarta dake gefen kujera takira zeenat .

minti kadan byn kiran wayar da ummi tayi, nablah taga wata kyakkyawan mata ta fito daga wani bedroom wanda da alamun muhalinta kennan itama kana ganinta kasan naira tasamu gidin zama ajikinta tafiya take tamkar bazatayi ba, sai rangwada take tana zuba kamshi jikinta sanye da Riga da sike na a tamfar super exclusive kayan sun zauna ajikinta das.
,Takaraso . ta zauna kusa da ummi batare da tace komai ba ,yayinda fuskarta take a daure bbu wani annuri tana kallon nablah dake zaune a gefen aunty Salmah taji wani abu ya dungule mata a kirji, gabanta yashiga faduwa 'ahankali ta dauke idanunta daga kan nablah ,tana sake jin faduwar gaba.

'Ahankali ummi ta numfasa sannan ta cewa Aunty Salmah kice yarinyar ta Mike tsaye mana .
" tun kafin aunty Salmah ta bawa nablah umarni ,ta Mike tsaye cikin sanyi jiki wanda kusan yanayina kennan akoda yaushe.
Amman wannan karan yafi na kowani lokaci Dan gabadaya ilahirin jikina ya sake yin sanyi
,daganin irin kallon da zeenat ke mata .
dan haka gaban nablah yacigaba dukan uku uku kallon tsaf ummi tayi mata sannan ta lumshe idanunta .
ita kuwa nablah tunda tayiwa ummi da Zeenat kallo daya ta dauke idanunta daga garesu bata sake kallon Ida suke ba , domin hakan yana cikin nasihar da auntyta tayi mata kafin su fito daga gida .
Chapter 58 · 0% Book details