← Book details Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 90

Sashe 7

Auren Sirri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Byn kwanaki , DEENi yakasa hakuri da maganar zeenat din kmr yadda yaso shima ta share da zance kawai ya manta dasu "
Amman yakasa, ya samu ummi da kansa a wata safiya dayazo gaisheta byn yayi shirinsa na zuwa aiki cikin kakinsa dake kara masa kyau tamkar dan shi kadai akayi" sai kamshin yake zubawa ta koina "gashin kan nan nasa kwance luf luf luf dasu , duk da bacika yawa sukayi ba ,saboda yanayin aiki "Amman dayake Allah yayi mishi suma takoina ajikinsa ko yayi askin ma baya wani dadewa" gashin zai sake fitowa" sosai yayi kyau matuka ,ita kanta ummi satar kallonsa take har ya tagota ya sakar mata murmushi tace son kayi kyau sosai fa, uniform din nan nakara maka kyau ,ya dage mata girarsa daya yace Allah first lov yace ai daman can nj may kyau ne sannan duk maccen datayi dacen samuna , ta gama samun duniyarta sai dai ta nemi lahirarta kawai " ummi tayi dariya sosai ya kamo hannun umminsa cikin nasa muryasa a shagwabe hade da dan karyar da wuyansa, yace first lov da kanki ma kin yaba dani "tace uhmm yabon gwani yazama dole "yace to meyasa bazaki bani auren zeenat ba ?
Ta lissafomasa dalilinta kmr yadda ta sanarwa Muhammad ta Kuma sake jaddada masa yaje gaba ya nemi mata Amman banda diyarta ranshi ya baci Amman ya share take Yar fara'a dake fuskarsa ta dauke " sai dai bai nuna ba , cikin sanyi murya yace to Shikenan ummi na hakura" Amman bazan taba zuwa koina neman aure ba" saboda banida nagartar daza'a soni Kuma bani aure" ummi tace ba fa haka nake nufi ba yace haka ne mana first lov" ina da munanan halayen da ban cancanci abani mata aure ba. ummi tayi murmushi tace nifa bance haka ba yace haba first lov kince mana gashin nan kema da kanki kin hanani taki Yar , to waye zai amince yabani yana kaiwa nan ya cire hannun umminsa cikin nasa ya mike cikin sanyi jiki tamkar bai damu ba ,.
gabadaya jikin ummi yayi tsanyi ita bawai auren ne bata so ba halinsa take gudu ta yaya zata yarda ta aura masa marainiyar Allah yazo yana cutar mata da yarinya .

Abin mamaki duk a tunanin DEENi na bazai shiga damuwa ba akan kin amincewar ummi ,
sai gashi dumu dumu cikin tashin hankali kullun sai yayiwa umminsa naci da magiya akan tabashi auren zeenat ,ita kuwa ummi duk lokacin dataga ya dauko mata zance sai share hade da bata fuska .

Please kumin uziri , may be zaku dan jini shiri sakamakon matsalar rashin wuta naso narinka muku type akai akai batare da westing time ba Amman kuyi hakuri ana kyawun tare🤝🏻🤝🏻

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Page 9-10

Zeenat kwance a bedroom din ummi hannuta rike da wani English novel face to face tayi zurfi cikin karatun novel din saboda yadda take enjoy din novel din ya .

Yaya DEENI ne yashigo gaishe da ummi kafin yafita aiki ,byn sun gaisa ne ummi tace har ka shirya fita kennan ? Yace mata eh sannan yaja ya tsaya yayi shr ya zubawa ummi idanunshi .
ummi ta dubeshi tace da magana ne ? Tunda tarigada tasan muddin yayi shr irin haka to da magana a bakinsa.

koda yake tasan dai zance nasa bai wuce maganar zeenat bane " Kuma daman tana son zeenat din tajima kunneta idan ta amince ruwanta "
dan haka ummi kalleshi da kyau tana nazarinsa ta numfasa sannan tace masa kayi shr alhalin nasan da magana abakinka .
, muryasa a shagwabe yace first lov kan dai maganar zeenat ne ,dan Allah first lov, ba yabon kai ba "ina da qualities din da za'a bani auren kowace irin mata nake so" Kuma ko Yar gidan waye ,.
Yar taki ma daba wani kyau ne daita ba" dan ma zan taimaka mata "ya fadi haka fuskarsa a hade ,.

ummi tace duk da haka day bazan bada diyata ba kaje waje ka gwada sa'a r ka" wai ma in tambayeka DEENi yamaida hankalinsa sosai ga umminsa" tace kai da kake ta damun kanka da zance nan kullum. kasamu ita yarinya da maganar ,kun daidaita kanku ne ?
DEENI yace uhmm kece dai zaki sanar mata, ummi ta nuna kanta da dan yatsanta, nice ma zan tayaka yakin nemar maka soyayyarta" lallai ma bason auren nata kakeyi ba" kashare zance kawai tunda baka shiriya neman aure ba. yace to ni first lov in na fada sai naga tamkar Raina ne zatayi, ummi tace kunji girman kan ba a hassale ummi tace dan Allah kayi hakuri kabar zance nan. haba duk kabi katadda hankalinka da nawa. yarda ne dai bazanyi .
dan haka kayi hakuri kabar zancen nan kwata kwata dan ba yarda zanyi ba .

DEENI daya gaji dayiwa ummi magiya ya hakura ya ficewarsa ,yana jin takaici kansa, tunda daga lokacin da zeenat taji DEENi ya ambaci sunanta ta mike zubur zaune daga kwanciyar datayi, hankalinta a tashe jikinta har rawa yake tsabar rudewa" ita zeenat din yaya DEENi yake nufi ko wata daban.
ahankali ta furta in ko ita yake nufi dakuwa ta more a rayuwarta, dan gaskiya yaya DEENi ba irin namijin da mace zatace bataso bane , ahankali ta sake furta A'a dan Allah ummi kada kimin bakinciki mana.

tana jin fitarsa ta fito da sauri daga dakin tana kallon ummi dake zaune tana jan carbi, zatonta ko ummi zata mata maganar ne. Amman sai taga sabanin haka .
dan kuwa ummi ko kallon inda zeena take tsaye batayi ba.
dan tarigada tasan taji komai" to Kuma bayanin me zata tsaya yi mata. Ta dai yi shr ne taga yadda zata dauki lamarin .
Can kuma, ummi ta dago tana duban zeenat din tana nazarinta" yayinda zeenat din itama ummi take kallo" har zuwa lokacin ummi batace komai ba .
sai ma kau da kanta gefe datayi , ganin ummi bada niyyar ce mata komai ,yasa zeenat kira sunan ummi" ta juyo tana duban zeenat din da kyau".
ahankali cikin sanyi murya tace ummi wai wata zeenat din yaya DEENi keso ?
Ummi ta dan tabe baki sannan tace dan Allah rabu dashi wai ke yake nufi "da sauri zeenat tasa hannuwanta duka ta dafe kirjinta dasu tana zaro idanu waje "tace da gaske ni yake so ?
ummi tace zan miki karya ne" zeenat ta marairaice murya tace shine Kuma ummi zakice masa baki yarda ba.

ummi tace to may kike nufi ,kina son kice min kina son DEENi kennan ? Zeenat Tayi shr dan bata da amsar bawa ummi dan gabadaya ilahirin jikinta bbu inda bai dauki rawa ba.
ummi ta sake yin magana daman kina son DEENi ne naga duk kin tada hankalinki haka ?zeenat tace nifa bance ina son shi ba Amman ke meyasa zakice A'a Kuma ma mayye dalilin dayasa kika ki amincewa ,ummi tace ok tutseni zakiyi" kan naki yarda ko yaya , zeenat tace ba haka bane" ummi tace tsaya ma kiji abinda yasa naki yarda, DEENi "da" nane' ni haife shi da cikina sannan ke ma kinsa halinsa sarai da shege miskilanci da saurin jin haushi mutun ,abu kankani ke hassalashi ga tarin girman kan tsiya, zeenat ta tsugunna nan gaban ummi hade kamo hannuwan ummi duka cikin nata muryarta sanyaye tace haba ummi dan day kawai saboda wannan halin nasa ne "zai sa kike amincewa , in dai dan haka ne' ni na amince da aurensa kinji .
ummi tace duk kinbi kin koma kalar tausayi wai ma meyye birgeki da DEENi ne naga duk jikinki ya dauki rawa haka ?.
Zeenat tace ai gaskiya yaya ba irin mutunmin da za'a tsaya cewa ba,aso bane ni dai na amince ,ummi tace ko kin amince, ni nace A'a ban yarda ba ,.

Zeenat ta mike cikin fushi tayi bedroom din ummi .
da kallo ummi tabi bayanta dashi ummi taji matukar mamakin ganin reaction dinta musamman da tasan zeenat din ,bata fiyye nuna fushinta akan abu ba .

Koda tashiga dakin ma waje tasamu ta zauna abunta tayi tagumi batayi aune ba, kawai taji hawaye na silalowa mata.
ita kanta tasha mamakin ganin hawayen na zuba a idanunta "ta tambayi kanta to daman can tana son DEENI ko yaya? domin abun itama yayi maseefar daure mata kai ".
kuka takeyi " iya karfinta hade da ganin laifin ummi din ,to meyyesa ummi zatace batason aurenta da ya'ya DEENi byn ita tasha kisma haka a ranta .
taci kukanta sosai har sai da taji alamun kanta ya fara mata ciwo ta runtse idanunta sannan ta kwanta "nan a gefen bed din ummi tacigaba rera kukanta kasa kasa .

Yinin ranar tayi shi ne cikin daki hade da tunanin DEENi da kitsima kalar rayuwar da zatayi a gidan DEENi.
Da zarar taga ummi kuwa take hade fuskarta saboda jin haushin abinda tayi " .
kusan zuwa Maryam uku gidan "Amman zeenat taki saukowa kasa" dan gabadaya takasa samun sukuni gabadaya haushin kowa take ji.
,ita kuwa ummi sai binta take da idanu dan ma kasa magana tayi , gashi ranar Sam DEENi ma kin dawowa yayi da wuri sai wajen shabiyu , .

haka ma washegari tun asubar fari yabar gida ya dai shigo ya gaida umminsa a tsaitsaye.

,byn ummi ta idar da sallah ne kafin ta soma lazimi , yayinda zeenat ke kwance akan bed , idanunta a runtse tamkar may bacci Amman Kuma ba baccin take ba .
ummi takira sunanta kusan sau uku Amman tayi mata shr alhalin tana jinta.
ummi ta sake kiran sunanta tace zeenat nasan kina jina Kuma idanunki biyu Amman kika min banza , hade da ganin laifina .
bakomai yasa kika ga naki yarda da maganarki da DEENi ba" nasan halin DEENi ciki da bai bashida dadin sha'ani kwata kwata gashi da bakar zuciya tsiya azo ayi auren nan yazo yana gana miki azaba, .
Chapter 7 · 0% Book details