← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 82

Sashe 9

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   kwana Uku mu"azzam yayi Ummi bata barinsa Fita ko"ina wai sai yagama warwarewa Ranar na ukun da kuzarinsa yatashi shima din dakyar tabari yatafi aiki sai daya tabbatarmata da cewa ya warke kuma zai kula da kanshi..Suna Fita yacema Ushe kaduna zasu sai da Shureim ya gansa kwatsam kiransa kawai yayi yacemai yana ina ?yace yana cikin asibiti "

  Kallo Farko Shureim yayima Mu"azzam yasan ba lafiya yana tsakar duba patient ne ammh dole ya yanke ya turama wani Likitansu yadda kai kawai mu"azzam yayi bisa kafadansa yana fadin"Yazanyi dan"uwa ina cikin damuwa kirjina yamin Nauyi bansa yazanyi ba na shiga tsaka mai wuya"Yafada kamar zai fashe da kuka bubbuga bayansa Shureim yakeyi baiyi mgana ba sai zuwa chan yadago kujera yaja masa ya zauna karamin Fridge din dake office din yabude ya dauko Ruwa kofunan dake saman gun ajere ,yadau daya ya tsiyayamai Ruwa ya mikamai ba musu ya karba yasha Yakara mikamai alamar yakarama ba musu Dr Shureim ya zubamai sai dayakusa shanye rabi kana yadagamai hannu maida komai yayi ma"adanarsa kafin yakoma ya zauna yana Fuskartarsa kafin ma Dr Shureim yayi mgana Mu"azzam ya rigasa da cewa.

  "Sun saka Ranar Dauren Auren fa"Yafada cikin wani yanayi zaro ido Dr Shureim yayi kafin yace"Kai don Allah wasa ko gaske"Wani kallo Mu"azzam yamai kafin yace"Kaga alamar wasa atare dani wlh da gaske nake jiya baffa ke fadamun nan Da two week nazo adaura Aure"Dafe kai Dr Shureim yayi yana Fadin"Innalillahi Dan"uwa Abu fa ya rikice Yazamuyi Da Ummi shine babban problem din

"kallonsa kawai mu"azzam yayi idanunsa sunyi jawur yace"Shine nakasa nemo mafita.juz tell me ya zanyi.ni kamar ma na gudu daga kasar gabadaya wlh"yafada yana dafe kansa saurin girgixa kai Dr Shureim yayi kafin yace"No bashine solution ba,yanzu Abunda za"ayi kakoma gida gobe zanzo sai mutaru mu fadama Ummi ko ya kagani"zare ido mu"azzam yayi kafin yace"Wata Ummi kaga mallam nemo wata hanya dai...Kana tsammanin Ummi taji wannan lbrin bata Yanke jiki ta fadi ba kasan ko yadda Ummi tadauki gaba mai tsanani dasu Baffa"Yafada cikin Nuna Abun ya ishesa.

Dafe kai Dr Shureim yayi kafin yace"Hajiya fa bazatayi wani Abu akai ba"dagowa yayi kafin yace"Hajiyarmu.."gyada masa kai Dr shureim yayi Dan ihu Mu"azzam yayi kafin yace"Yes gud..Ka kawo shawara kafadama hajiyar tamu yadda kukayi sai naji..Ammh wlh fadama Ummi ba mafita bane dan"uwa kafi kowa sanin Ummi kai fi daya ce"

"insha Allah komai zai Tafi daidai karka damu" shureim yafada Mikewa Mu"azzam yayi ya mikasa hannu sukayi musabaha yana fadin"Ina da wata shari"a Zan koma sai munyi waya"Damke hannunsa Dr yayi kafin yace"Kadaina damuwa plz dan"uwa anytin will be alright kaji"Gyada kai kawai yayi kafin ya fice a office din Ransa a jagule...

Koda Dr Shureim yakoma gida bai fadama hajiya ba sai da safe itakanta ta shiga rudu tadinga juya Abin Aranta kafin tace"Shureim akwai mtsala Suhaima tanajin dukkan mganata ammh akan  Abunda yashafi zuru"ar moodu zuciyarta ta tsaure Abunda suka mata yasakarmata dafi mai zafi wanda mantashi sai anyi babban jihadi..Kai na ya kulle wlh Suhaima baza tataba yarda Mu"azzam ya auro diyar fadi ba bazata taba yarda ba"Tafada cikin tabbatarwa..Jikin Shureim yayi bala"in Sanyi rausayar dakai yayi kafin yace"Plz hajiya do Sometin ke kadai ce hop dinmu wlh"Kallonsa tayi kafin tace"baka son komai ba shiyasa ai shi mu"azzam din yasani shiyasa yakasa Fadamata,ammh kubar komai Ahannuna zuwa gobe in na yanke decision zan Nemeka"mirmishi yayi yace"yauwa barrister tink abount it nasan baki rasa mafita"Fulon kujera tamakamai Tana fadin"Ka maidani kakarka ko Shureim"Ficewa yayi yana fadin"Matsayinki na mutum uku ne uwa,uba,kaka kinga dole na dinga taba kowani barayi"Dahaka yafice yana dariya.

****  *****  ******  *****

  *MAID*

  Achan kuwa Tuni duk wani Shirye shirye ya kamkama Zahirah batasan komai ba itadai Bahna dinta yace ta tattaro kayanta zata koma gun yakura da zama murna kamar zai kasheta jiki na rawa ta hada ya dauketa yakaita gun yakura.itakuwa batare da tsayawa wasa ba ta shiga gyara yarta tata Zahirah yarinyace,shiyasa bata fahimci komai ba,ammh abun yana bata mamaki komai aka bata tasha wanka ma bada ruwan banza take ba hakama tsarki..Turaren tsugunno ko har tagaji dashi kuma Abunda yafi dauremata kai tadaina zuwa mkranta data tambayi baffa sai cemata yayi "Kada tadamu xata koma mkranta ammh ba anan garin ba"To miskilancinta yahanata kara magana..Uwa uba ga Nasihohin da yakura kullum dare take doramata kan tayi hakuri da duk Rayuwar data tsinci kanta karta bari a fahimci Rauninta, zahirah yarinyace miskila wacce mgana ba damunta yayi ko ta tambayi yakura amsa daya take bata"Mtsayinki ne zai karu yahna"daganan bata kara cemata komai Itakuma bakinta na mata Nauyin kara tambaya.

  Ayayinda biki yarage Saura one week duk wanda ya kamata yaji sai yaji don Bukar ya shiryama Abun gayyah yayi sosai shida mahgana Wanda mutane dadama Sunyi mamakin wai Mu"azzam dan Suhaima wanda ba"arabu ta dadi ba za"a kuma kulla auratayyah wasu dadama sun kasa gasgassta abun wasu kuma so suke suji yadda wannan al"amari zai Faru Shikuwa Shettima ya dole kunnensa Ruf burinsa kadai yake Muradin cikawa.

•°•°•°•°•°•°••°•°•°•

   """"Kokarin daura tie yake lokacin da wayar ta shigo masa Sai da gabansa yafadi dayaga, sunan BUKAR MAID Ya fito baro baro..Gabansa ya fadi har sai da wayar ya yanke yarasa Abunyi kafin ya nemo mafita wayar ta sake daukan kuwa..Cikin mutuwan jiki ya daga kiran kokafin yayi mgana yaji muryan Baffa na kwarara sallama cikin mutuwan jiki ya amsa bayan ya gaisheshi.

  Baffa Shettima yace"Daman dalilin kira na karin Tuni ne Rana ita yau ne za"a daura Auren kada ka sha"afa don Allah kada kabani kunya dana"Yafada cikin karyewar murya Cikin daburcewa mu"azzam yace"Bazan baka kunya ba baffa ammh bazata tare ba ko? Saboda akwai shirye shiryen danake son gudanarwa"Bude bakin baffa sai cewa yayi "Kada kadamu da wannan Ai zahirah kanwarka ce..Babu abunda zaka wahalar da kanka ko dakin dakake kwana ka ijiyeta babu damuwa komai sai yazo daga baya..Ammh kamim alfarmar ana daura aure zaka taho da matarka nan"jikin Mu"azzam yadau rawa zufa tana yankomai yanaji baffa nata hello hello ammh kuma ya kasa mgana dakyar ya iya cewa"Shikenan Baffa Umarninka shine nawa...Allah ya kaimu'Yafada kamar zai saka ihu.

   *MU"AZZAM....!* yaji muryan Ummi takirasa daga baya cikin muryan fushi da tsantsan bacin rai, a firgice ya waigo yana kallon Ummi wacce ke tsaye kikam akofar dakin nasa Fuskarta babu Annuri tana Fitar huci cikinn Fushi da bacin Rai...Ai Tuni mu"azzam yaji kansa na juyawa jikinsa yahau rawa babu Tamtama Ummi tagama jin komai yau karyansa takare.

   Abunda baisani ba tun sanda yafara waya Ummi na tsaye awurin tagaji da jiransa yaxo suyi breakfast ne yasa ta biyo sawunsa hankalinsa yayi gabane shiyasa baiji karan bude kofarta ba dukkan Abunda yafada a kunnenta.

Takowa take cikin Fushi tana karisawa kusa dashi tace"Mu'azzam minaji kana fadi..Naji kana fadin in an daura aure matar bazata tare ba? kuma naji kana ambatan Baffa wani Baffan?'"Tafada cikin Tsawa tana zaremai ido jikinsa na rawa yaja baya yana Fadin"A"a Ummi tsaya kiji kada ki daga hankalinki don Allah"Tsareshi tayi ido wanda suka kada kafin tace"Zaka fadamin ko sai naci UBANKA YANZU ANAN"Tafada kamar zata dakesa.

Bai da Zabi illa zubewa dayayi agabanta yana fadin"Ki yafemin Ummi rashin gayaminkin dabanyi ba..Bani son Tashin hankalinki ne narasa mafita Ummi"Yafada kamar zaiyi kuka hannu tadagamai kafin tace"go to d point Mu"azzam wani Baffan kuma wata matar naji kana mgana akai"Tafada cikin Tsawa runtse ido yayi kafin yace"Zuwan danayi maiduguri baffa yakirani yana bani UMARNIN auren Diyar marigayiya Inna Fadi ta da rasu ta bar... " *TAS.."TAS..."TAS..* kakejin Karan tafika ta ko'ina haka Ummi ke zuba su bisa Fuskar mu"azzam Tana kuka take fadin

" IBRAHIM nizaka ci amana...Nizaka Tozarta to wlh baka isa ba, zoka Ficemin daga gida kaje bani bukatarka wlh na barma Shettima kai, daman Burinsa kenan..Zoka fice Ibrahim bani kaunar ganinka zo ka Ficemin.."

tafada cikin wani yanayi Kafin tajuya Tafara tafiya tana kuka jiri ne ya kwasheta kafin kace me ta zube kasa warwas kamar gawa cikin wani irin Rudewa Mu'azzam ya mike lokaci daya yana kwallah kara da fadin

   *UMMI NA*..."yafada cikin Sauti wanda,duk wanda ke gidan sai da yaji wannan Sautin.

_*hohoho..Anzo gunfa janaf fans...Akwai badakala mai ban mamaki da tsausayi da Nadama..Kubiyoni ni zan warware muku ZARE DA ABAWA*_

*#TEAM ZAHIIRAH#* _Kutanadi Botiki na taran hawaye_😛

*#TEAM MU"AZZAM#* _kuma ku Shirya shiga cikin kuncin rayuwa,garari tareda fadawa tarko mai wuyar fita_😂

*#TEAM UMMI#* _Ku kuma ku daura damarar daukan Fansa,ba mutumci yasin no respect_😎

*Comment*
*Share*
*Vote*

*#intelligent writer's#*
*#Uwar mijina...!#*
*#Janaf#*
*#One love#*
[18/08, 14:17] 80k: _*INTELLIGENT WRITERS ASSO*🖊_

🌺 *UWAR MIJINAH..!*🌺
        _(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri, Tareda biyayyah mai Tsanani)_

       *ALKALAMIN:JANAF*💕
        *WATTPAD:JANAFNANCY*

*DEDICATED To my BLOOD Sisters JANAF*

*NOT EDITED*⚒

*NO.8*

    '''''''''''Lami da Uwani Dake kichen suna kokarin hada breakfast sukaji wannan ihun tare da kiran Sunan Ummi,cikin Dimautuwa suka fito falo nan sukaci karo da karime itama ta rumtumo zata shigo kichin din hannunta dafe da kirji take fadin"Lami kunji abunda naji kuwa?'Tafada tana haki.

Lami bata samu zarafin mgana ba ,sai ga Sani maigadi da Falalu mai bawa fulawa ruwa da ushe suma sun Rumtomo zuwa falon Suna tambayan lafiya ihun me sukaji haka"Karime ta nuna Saman Hajiya tana fadin"Wlh bamu Sani ba ammh kamar daga bangaren Hajiya ne fa"Basu samu zarafin mgana ba suka ga Yallabai ya fito cikin tashin Hankalin hannunsa dauke da Ummi wacce ke halinn rai da Mutuwa.

Cikin sarsarfa yake saukowa yana Fadin"Bring d car plz"Yafada cikin tashin Hankali ganin haka yasa ushe rumtumawa waje ya bude motar yallabai wanda ya fito da ita 607 kirar Piogion ,su karime ko hannu suka daura akai suna fadin"Mun bani hajiya innalillahi wa"inna Alaihirraju"un"Haka suketa maimatawa har mu"azzam ya fice da sauri.

  Kokafin sufito tuni har yasakata a mota ushe yaja sani ya budemusu get sun fice cikin hanzari..Lami da karime jikinsa babu inda baya Rawa Uwani tace'Mun bani meyafaru da hajiya ne'tafada kamar zatayi kuka babu wanda ya iya cewa komai sai ma karisa da sukayi gun sani maigadi wanda ke zaune da falalu suma suna janjanta Abun haka sukayi tsaye tsuru tsuru babu mai iya cewa komai kuma sun kasa komawa sucigaba da aikin gabansu.
Chapter 9 · 0% Book details