← Book details Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 82

Sashe 5

Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Tunda Sukayi Aure Sau biyu Tak moodu ya kusanceta..Saboda shikanshi baida kwanciyar Hankali Koyarwan ma dayake don yazama Daolene Kwatsam Shettima yatada ballin Tunda Baffa yarasu to moodu yazo yabar musu gida da karuwa donsu haryanzu basu yarda Aure sukayi ba dauka Sukeyi Abokiyar Shashancinsa ne....

Wannan Shine mafarin komai Daren Da moodu yaji haka bai kwana Duniya ba zuciyarsa ta buga Allah yayi masa Cikawa..Mutuwar data girgiza xuciyoyi uku alokaci daya Shettima,Fadi,da Suhaima wanda ko amafarki basu zata ba. Mutuwar da haryanzu suke kokamata wanda basuda Ranar Dainata ba..Suhaima Sai Da Tayi awa uku asume har Saidai aka kai moodu zuwa gidansa na gaskiya ta farfado..Allahu Akbar duk mai imani yaga Suhaima sai ya zubar mata da kwallah domin Ayanzu bata da wanda zata kallah tace natane..Lokaci daya taji Duk Duniya bazata ta taba yafema Shettima Da Fadi ba don Sune silar mutuwar bango kuma ginshikinta.

S Fadi sun koka na Rashin Dan"uwamsu ammh kash hakan baisa sun Saduda ba anayin bakwai Suka tattara komai na moodu suka rike Suhaaima ko Tsinke basu bata da sunan bata da gadon dan"uwansu..Rayuwa tayima Suhaima kunci babu mai Tsausayamata Sai Yakura,Fadi kuwa kullum tazo zagi da cin mutumci babu wanda batasha tadinga jifanta da mugayen kalamai nacewa ita karuwace koda yake itama ta hanyar da"a ka haifeta kenan..Suhaima tayi kuka kamar idanunta zasu rufe gashi bata da nombar Khamis balle takira bata da kowa sai Allah.

    Tunbayan Rasuwar moodu Suhaima ta fahimci tanada jaririn ciki wanda bayyanansa gareta wani Taimako ne da budi daga Allah moodu yatafi Moodu yadawo..Suhaima tayi farinciki matuka lokaci daya tadorama cikin wani soyayyah wacce bata da karshe..Takudiri niyyar boye cikin domin kauda idonsu Shettima da Fadi,Haka ko akayi daman bafitowa takeyi ba komai adaki take,sai yakura ne ke shigowa dubata tana kaimata abinci Shima aboye,Sai dacikinta yakai wata shidda dayake tana da girman ciki yakura tafara ankarewa dashi lokacin Da Suhaima tafahimci yakura tafahimci Halin datake ciki.

   Ta tsorata harsaida Tsoron ya bayyana Afuskarta ta rike hannu yakura hawaye suna kwaranyomata tace"Kiganni ko duk boyensa danake sai da ya fito kirufamin asiri kada sufadi su Sani wlh zasu iya rabani da shi.kuma yanzu duk duniya shine kadai Sanyi idaniyata"Tafada da hausanta wacce ke chakule da larabci.

  Mirmishi tsausayi yakura tamata bayan tasanya hannu ta share hawayen Suhaima tace"Shi ciki duma ne Suhaima komai boyenki sai ya bayyana..Ki kwantar Da Hankalinki Insha Allahu bamai Rabaki da cikin"Da wannan kalaman Hankalin Suhaima ya kwanta.

Fadi bata farga da cikin Suhaima ba sai da yashiga watan Haihuwa cikin nata yaba kowa mamaki saboda girmansa gabadaya ta kumbura ko Tafiya bata iya yi gashi yayi girma sosai har yakura nace mata yan biyu..Lokacin Da fadi tayi Arba dashi sai da tazauna saboda razana saboda tijara sai tahau kururuwa tatara musu jama"a tana kuka tana Fadin"Dama mai hali bai fasa halinsa yanzu daga abokin Shashancin naki yarasu har kinje kin kunso ciki ko? to wlh ba gidanmu ba zo.zo ki fice ki san nayi ko kuma ko yanzu jiki magayi"Yakura saboda bakinciki batasan Sadda tashiga gayama Fadi mgana ba"  

   "Haba Fadi Haba Fadi..Zuciyarki ma imani ne haba tunda baiwar Allah nan tazo baki barta ta huta..Haba karkimanta Abunda kayi shi xa"ayi maka bakisan Ranar da zata miki ba"Fadin Haka da yakura tayi yazama Fitina don Shafin cin mutumci Fadi ta bude tanayi tana zagin yakura tana hadawa Da Suhaima..Yakura kuwa tabawa banza ajiyarsa.

   Koda Shettima yadawo wannan karon bai goyi bayan Fadi ba domin kirikiri yahana koran Suhaima, yace ai jinunsu na jikinta tabari randa tahaifemusu tabasu Abunsu Sai ta kara gab,to da wannan mganar Suhaima tacigaaba da zaman acikin gidan wanda tasama suna bakin gida,wasa wasa Saida suhaima Ta tsallake wata Tara bata haihu ba hartashiga na goma haihuwa shuru ba lbri gashi ita ba fita take balle tasan hayan Asibiti To in ma Tasani ina taga kudin Wanda ko Abunda ba"a bata mallaka ba daga dukiyar moodu ba.

  Cikin ikon Allah wata Ranar jumma"a Suhaima Tahaifi Danta Namiji bayan tasha doguwar Naguda tun daren jiya take Abu daya sai Ranar jumma"a bayan an sakko sallar Ta haifi Danta katoto wanda yafito sak mahaifinshi Sai dai kallo zakamai kafahimci Ruwa biyune, ma"ana Tsatsan barebari da tsatson larabawa,..Tunda Suhaima tahaihu lokaci daya taji kamar anzaremata wani Nauyi yaron da jini da komai takamashi ta kamkame tana kukan Farinciki mai hade da tunawa Da mahaifinsa kan kace kwabo yakura ta gyare Suhaima da yaro..Kayanma daza"asama yaron yakura ta dauko mata cikin kayan datake tarawa.

   Lokacin Da Shettima yasamun lbrin haihuwan Abun mamaki sai gashi yataka har dakin da Suhaima take yadauki dan wanda yadade ahannunsa yana kallo don photocopy Moodu ne sak lokaci daya yayi masa huduba yana mikamata yace"Allah ya raya *IBRAHIM MOODU* bata damu ba Ta amsa Da Amin domin sunan baida wani Aibu.

  Lokacin Da Fadi ta kyallah ido ga jarinrin Suhaima ai nan fa sai taji duk duniya shi takeso tasakama Shettima kukan Kan ita zata rike Ibrahim tunda bata taba haihuwa bata tunanin Shima Shettiman baitaba haihuwa ba Ta bullo da wannan mganar ne bayan anyi fitan bakwai raguna biyu Shettima ya yanka mishi suna kuma yabada kudi yakura ta siyama Suhaima dan kala daya da ita da jarinrin, Shettima bai maida kai agame da mganar ba sai Fadi ne tazo Tafurta ma Suhaima wacce taji Abun kamar Saukan Aradu..Lokaci nafarko Da Suhaima tadaga ido takalli fadi duk cin kashin datake mata,wani malalacin kallo tabita dashi kan tace"Tabdijam..Wannna karon baza kuyi nasara ba domin mu"azzam ni na haifesa kuma dana ne, saboda matukar ina Numfashi babu wanda ya isa ya karbesa koda kuwa kice ko Shettima"Saboda mamakin Suhaima Fadi ta kasa mgana.

  Aikuwa anyi karamin yaki domin Suhaima ta Shirya fito na Fito ga duk wanda zai Rabata da Farincikinta..Shettima bai zafafama kansa illa lallaba fadi yayi tabari ayayesa ammah baza atsuge yaro anonon uwarsa ba abaki mganar gaskiya..To wannan Dalilin shi yalafar Da mganar har Suhaima tacigaba daRainin Mu"azzam dinta cikin kwanciyar Da hankali da Taimakon Yakura wacce bata gajiya da dawainiya dasu.

  Lokacin Da Mu"azzam ya shekara Tuni Suhaima tafara Tunani  barin maiduguri gabadayanta tatafi ta nemi wani guri sucigaba daRayuwa ita da danta,ammh sai mai lokacin data bijiro da mganar Shettima yasakama idonsa toka yace Matukar zata tafi yawon Duniya to bada dansu ba sai ta dire musu Abunsu sai tayi gaba dama ba wani dalili,jin haka yasa hankalin Suhaima yatashi in tatafi ta bar mu"azzam ita ya rayuwa zata kasance mata bata da kowa aduniya sai Shi duk duniya ba wanda take kallah tayi mirmishi sai Shi dole tasa ta hakura da kudirinta tazauna ta cigaba da kula da Danta.

  Ganin zama bazai mata haka ba ga wahala takarun mata Sai tafara wankau tana aikawa makota aiko tana Samu Abunda tadan yi aka biyata dashi take hidiman kanta dana yaronta..Wanda tunda yatashi baisan kowa ba sai *UMMI* itace uwansa itace ubansa sai ko yakura,mu"azzam tun yana shekara daya dawani Abu yafara tafiya yaro ne mai wayau dashiga rai gashi miskili ne babu Ruwansa Da rigima Suhaima tazama baiwa domin komai takeyi Arayuwa don yadda zata gina Rayuwar tilon yaron nata guda daya take.

  Mu"azzam nada Shekara uku Aduniya yafara sanin wahalar rayuwa domin duk wani gwargwarmaya tare dashi akeyi..Babu mai kula dashi karamin yaro ne ammh yana da hangen nesa ko wasa bai yi da yara,kullum yana Tare da Umminsa saboda ita kadai yasani..Tun baya fahimtar rayuwa har yafara Fahimta yana da Shekara takwas Aduniya Yafara girma Suhaima tagaji da Zaman ukuba da Rashin yanci ga mu"azzam ya girma ya isa shiga mkranta ammh daga Fadin Har Shettima babu wanda yake bi takansa ita Fadi tace  tunda Suhaima tahanata to gata gashi..Ganin haka yasa Suhaima takai kukanta,gun wata makociyarsu Ita tadauketa takaita gidan wata barrister Baraka muhammed wacce lauyace mai zaman kanta tana tallafama gajiyyayyu da marasa karfi..Ita Suhaima tasamu ta karanta mata komai na rayuwarta wanda Sai da Baraka takoka mata itace ta share mata hawaye ta maka Su Shettima ababban kotun Jahar maiduguri kan tana son Kotu ta mata Adalci.

  Lokacin Da Shettima suka ga Sammaci suman Tsaye Sukayi domin basu taba tsammanin Suhaima zata musu haka ba..Ammmh sai me koda suka duba bata ma agidan bata dauki komai nata ba Hajiya baraka tace tadawo gidanta da zama har agama Shari"ar Shine silan komawarta kuma yakura kadai tama sallama...

  Tun Ashiga kotun Farko kotu ta zartan Hukunci Domin Shaidu sun Nuna Sheettima da Fadi basu da gaskiya sun cutar da baiwar Allah..Kotu ta yanke hukunci Mu"azzam zai cigaba da zama tare da mahaifiyarsa har abada ammh da sharadin bazata nisantashi da danginshi duk inda Suke dole ta sanar Dasu don Suna da Hakkin akanshi..Itakuma Suhaima kotu ta musu iyakata da ita domin basu da alhakin doramata karan Tsana...Kana ta Umarcesu dasu Bawa Ibrahim dukiyansa don mallakinsa ne..Hakanan babu yadda suka iya suka tattara komai Suka mika Suhaima itakuma ta damkama Hajiya Baraka.

*WACECE HAJIYA BARAKA*

  Hajiya baraka haifaffiyan, garin maiduguri ne uwanta da ubanta duk yan channe, kafin Allah yayi musu Rasuwa Hajiya baraka tana shekara goma sha takwas aka aurar da ita gawani dan Uwanta soja ne..Shiya sanyata Amkranta ta dora karatunta hartazama lauya..Lokacin da Allah yamai Rasuwa sakamakon hargitsin boka Haram Danta daya ne Aduniya *SHUREIM* wanda yaro ne mai hazaka da himma yataso cikin gatan iyayansa biyu har zuwa mutuwar mahaifinsa sakamakon hajiya baraka bata da wasu dangi shiyasa tarike danta suna zaune a tamfatsetsen gidansu Dake Famfamari..Gata lauyace mai zaman kanta tayi suna wajen tallafama marayu da gajiayayyu kuma tana daga cikin kungiyan na ta taimakama mata da kananan yara.

   Hajiya baraka ita tatafi Da Suhaima gidanta da niyar riketa na har Abada Su Shettima bisa Umarnin kotu suka bisu sukaga mazauninsu..Hajiya baraka tana matukar tsausayin Suhaima shiyasa asatin dasuka dawo ta sanya mu"azzam mkranta inda Shureim yake zuwa tunda daman zasu zo tsara shima din yaro ne..Hazakarsa da kuma yadda yaron keda kaifin basira yasa aka ijiyesa primary 2 cikin ikon Allah kan kace kwabo mu"azzam yabama kowa mamaki domin Kan yahada shekara amkrantan kowa yasan dashi saboda yadda Allah yayi masa baiwa kwakwalwa.
Chapter 5 · 0% Book details