Sashe 77
Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Babu dadewa aka sallahci baffa Shettima zuwa gidansa na gaskiya,wanda hakika yayi jama"a sosai dan adam sun taru makabartan dake kusa dasu aka binnesa,Hatta Dr,Abduljabar yasamu jana"izar baffa,amakabarta haka mu"azzam ke kuka harda majina shabe shabe,sai da su Shureim suka rikosa kana ya dago daga kan Kabarin baffa yana hawaye..Allahu akbar Allah kenan,wanda Shine hallicemu domin muzo duniya mu bauta masa,kuma yayi alqawarin daya bayan daya zamu koma garesa,Sai dai muyi fatan Allah ya karbi bakuncin Baffa yakuma yafema iyayyanmu,dasuka rugamu gidan gaskiya yasa Aljannah tazo kyakywan makoma agaresu Amin ya Allah.
Bayan andawo daga makabarta awaje aka baza tabarmu mutane suka zazzauna ana amsan gaisuwa,cikin gida kuwa Mata sunsha koke Zahirah ko tana kwance zazzabi ya rufeta saboda kuka,kan kace kwabo sai kulolin Abinci ke yawo agidan da katan katan din lemuka da ruwansha wanda mu"azzam yabada Umarnin aka sauke saboda mutane,baima san zahirah bata da lafiya ba, sai washegari daya shiga cikin gidan nan ya isketa kwance,hankalinsa ya tashi sosai,Dr,Abduljabar ya dubata yace damuwace ya rubutamata magunguna harda na karin jini domin yace jininta yayi kasa sosai,Fada sosai mu"azzam ya dingama zahirah kafin yakoma lallashi Kamkame juna Sukayi ita dashi suna kukan rasa uba majingini agaresu,to yazasuyi Abunda Allah ya tsara bawa bai isa ya tsallake shi ba.
Yau akayi addu"ar bakwai din Baffa Shettima duka jama"a sun watse daga kofar gida,sai na cikin gida kadai irinsu Ummi da su hajiya,anyi addu"an bakwai kowa ya kama gabansa,Su mu"azzam da Shureim da bukar suna cikin falon gidan zazzaune anakarama juna gaisuwa,Ummi ce da Mahgana sai hajiya da yakura,su Zahirah da zulaika da lubna suna cikin daki su da yara,Taruwa sukayi suna bawa yakura hakuri saboda yadda haryau batabar kuka, ba dole tayi kuka mutuwar miji ba wasa ba,Gyada kai kawai take bata mgana sai dai share kwallah,nan Bukar ke fadamasu Ummi rasuwar matar Tsohon mijin Zahirah Alhaji kabiru wato yagana,wanda yace harma Tayi arba"in da rasuwa azencen dayakeyima harma Mahaifiyarsa tamai Aure daga kano.
Rike baki hajiya tayi tana fadin"oh duniya Yanzu duk bala"in matanan game da mijinta,sai gashi ta mutu ta barshi.."Bukar yace"dama haka rayuwar take,ance chan wajen bin yawon bokayentane sukayi hatsari Ita da wata hatsabibiyar kawarta, ance motarsu Ta shige kasan Daf ne rai ko daya ba"a fitar ba daga motan,tsakanin kankara zuwa Dutsenma Abun ya faru.."Sallallami suka dauka Yakura tace"Allah yajikanta,duniya kenan duk yadda kaso ga Sonta watarana sai ka mutu ka barta.."duka suka amsa da Amin Ummi ce tasaka baki takira zahirah Ta fito nan take shaidamata rasuwar Yagana dafe kirji tayi kafin tace"innalillahi yaushe Ummi? wlh banji ba..."Tafada idonta na cikowa da kwallah nan Ummi ke fadamata yadda bukar yafadamusu,kanta ta sunkuyar tana fadin"Allah yajikanta da rahama.."Tafada cikin Rauni hawaye yana tarun mata,kwallah na Shirin zubomata dago kanta tayi suka hada ido da mu"azzam saurin girgizamata kai yayi yana mata nuni da hannu alamar karta bari hawayen idonta su zubo,saurin kauda kai tayi tana kokarin danne kukanta.
Mu"azzam yakalli Ummi yana fadin"Gobe kafin mu wuce sai muje muyimasa gaisuwa,daman inason ganinsa,kunga yamazo adaidai kenan.."kowa kallonsa yayi yana mamakin Furucinsa kauda zencen yayi da cewa"Kuma Baba zamu tafi da yakura chan Abuja,su zauna tare da Ummi nan kuma sai A rufeshi duk sanda akazo sai abude asauka aciki.."Bukar yayi ajiyar zuciya kan yace"Shikenan Tunda haka ka yanke,ada naso ni na dauketa takoma gidana,ammh babu komai dachan da nan Duk dayane aie..Allah ya jikan baffa yasa ya huta.."Gabadaya suka amsa da Amin yakura na kuka tace"Dama kun barni nayi zamana anan,inyi ta sallah da ibada har nima nawa lokacin ya cinmin"Tafada tana kuka wanda yayi sanadiyar tashin zahirah da Sauri takoma daki saboda tsausayin yakura.
Dafata hajiya tayi kan tace"a"a yakura baza"ayi haka ba gwara kikoma chan ku zauna tare da suhaima,kinga nan ke kadai ne,kadaici zaiyi miki yawa,chan ko ko banza akwai kiriniyar yara,zaki ji zuciyarki ta rage kuncin datake ciki.."Kowa yayarda da kalaman Hajiya har ita yakura ta gyada kai tana share kwallah,nan dai sukayi addu"an kafin atashi taron.
Haka ko akayi washegari da safe dukkansu sukayima gidan Alhaji kabiru kwanya,Bukar shine jagoran tafiya sunazuwa kofar gidan yadaga waya yakirasa yace gasu awaje yazo da baki ne,jin hakane yasa Alhaji kabiru Fitowa ganin mutane da yawane,yasa yace dukkansu su Shigo don Allah,ammh har lokacin bai lura da zahirah ba,dumguma sukayi har zuwa falon gidan,Alhaji yahau kwalama matarsa kira hajara tafito da sauri tana ganinsu ta hau musu sannu da zuwa,Amsamata sukayi cikin sakin Fuska kichen ta shige takawo musu lemuka,da ruwa ita da zulai,Wacce itace ta lura dasu little Ummi,aiko da gudu ta isa garesu ta dauki Ummi tana fadin"La Alhaji ga Ummi karama.."tafada tana nuna mishi ita,shima da mamaki yake kallonta kan yamika hannu yana fadin"a"a Zo zo..,"yake fada yana amsanta kan yace"ina moodu ne? Fadin haka yaji moodu ya rikemai kafa yana bangala dariya kallonsa yayi yana fadin"a"a manya diban Fari,ashe kana kusa"yafada yana dagasa da hannu daya,suka ko lafe sunamai dariya da gwarancinsu kamar sun ganeshi kallon bukar yayi kafin yace"Ai sai kacemin da yarana kake tafe kabarni Shuru sai da suka shaidani.."Dariya bukar yayi kan yace"Ai duka Alhalinmu muke tafe,harda mamansu da mahaifinsu gabadaya"yafada yana kallon mu"azzam.
Alhaji ya washe baki yana fadin"Masha Allah.."lokacin ne,kuma yaga zahirah wacce kanta ke duke,mu"azzam ne da kansa ya mike ya isa ga Alhaji ya mikamai hannu yana fadin"Sunana brr,mu"azzam nine mijin zahirah nada,da na yanzu.."mikasa yayi sukayi musabaha kan Mu"azzam ya cigaba da cewa"munji lbrin rasuwar maidakinka Shine kafin mu wuce mukace bari muzo muyi maka gaisuwa.."Cikin jin dadi Alhaji yace"Hakuri da godiya wlh ngd sosai,kuma yanaku hakurin? Allah yajikan Sheettima yasa ya huta.."Suka amsa da Amin kafin su Ummi Su shigamai gaisuwa yana amsawa zahirah ce ta karshe tafada asanyaye,Shima asanyayen ya amsamata yana kokarin danne wani Abu,matarsa hajara yakallah kan yace"Kinga zahirah dana baki lbrinta nan,ga yan biyu,suma kingansu wa"innan iyayyantane da mijinta suka zo min gaisuwa,dayake suma Wan mahaifinsu ya rasu,yau sati daya.."gyada kai tayi kafin tace"ayyah sannuku da zuwa,Allah yajikansu.."suka amsa da Amin.
Kafin ya cigaba da cewa"Matata kenan Sunanta hajara daga kano na Aurota.."Su Ummi suka amsa da masha Allah,suna musu fatan zama lafiya da zuru"a dayyiba."ya amsa da Amin Amin Falon yadanyi Shuru kafin mu"azzam yayi gyaran murya yace"Dama na dade inajiran wannan Ranar,dazato nima narama maka Kwatankwacin Hallarcin dakamin.."yafada kan ya cigaba da fadin"kowa ya Shaida Alhaji yasaki zahirah ne saboda ya cece rayuwata daga mutuwa.."Kowa afalon ya bishi da ido banda Ummi da Lubna sai zahirah wacce kanta ke kasa.
Bukar yace"bamu gane ba,kasamu aduhu mu"azzam.."Alhaji yayi saurin cewa"Don Allah karka tada mganarnan ni don Allah nayi,kuma harga Allah bantaba fadama wani nawa ba,mu binneta iya mu da muka sani.."Ummi ce ta mike tana fadin"Bazai yuyu ba Alhaji dole mu fadi kowa yaji.."Kan tajuya kan bukar tana fadin"Eh da gaske ne,ninazo dakai na rokeshi tare da fadamai halin da mu"azzam yake ciki alokacim,Nan ta shiga basu lbrin komai Tundaga farko har karshe,kafin ta karishe da cewa"kuma banyi hakan dawata manufa ba,sai don Ceto Mu"azzam daga Halin dayake ciki.."Sai falon ya dau Shuru kowa yana auna Abun yana jinjinakai Hajiya ce tayi karfin halin cewa"Baku kyauta ba Suhaima,gaskiya baku kyautaba,ai ba haka akeyi ba,mutum da matarsa kizo kice sai ya saketa saboda danki,to shi wani hali zai Shiga in ya rabu da ita.."Sunkuyar dakai Ummi tayi kafin tace"Nakasa juran ganin halin da Son yake ciki ne alokacin wlh banma san sadda nazo ba"Tafada tana kuka.
Bukar ne yace"Ya isa hajiya tunda aikin gama ya riga yagama,shima Alhajin baikamata ya biyemusu ba,ammh hakan babu laifi donko a addini akwai sadaukarwa, wani Abun indai Abun yafi muhimmanci garesa,kuma yafika bukatuwan Abun,hakan babu kuskure acikin saidai muyi fatan Allah yabamu da ladan Abun.."Dukkansu suka amsa da Amin.
Mu"azzam baiyi mgana ba ya kama hannun Alhaji danasu Little Ummi yahada yana fadin"Ku shaida daga yau ni mu"azzam muhammed moodu na barma ko nace na mallakama Alhaji kabiru Little Ummi da moodu karami halak malak,ko bayan raina shine mahaifinsu ni sai dai na amsa sunan Ubansu asuna.."yafada yana kallon idanunwan zahirah da Ummi,wanda sukaji mganar abazata.
Zaro ido Alhaji yayi yana fadin"Ni..Ni..Ka..ba..Ma...."yafada yana rawar baki,gyadai mu"azzam yayi yana fadin"Eh na baku su halak malak kaine yanzu mahaifinsu matarka kuma mahaifiyarsu.."Ai sai Alhaji yayi luuu zai fadi mu"azzam yatarosa yana kiran sunanshi,fashewa da kuka kawai Alhaji kabiru yayi kafin ya hada Mu"azzam da yaran ya rumgume yana fadin"Ashe akwai ranar da wani zai sani Farincikin daka sani,duk duniya bani da kishirruwan komai sai nasamu zuru"a Ammh kuma Allah bai bani ba,sai gashi wanda banzata ba ya mallakamin Abunda ni bazan iya samarwa ba niko dawani baki zanyi godiya,Don Allah kutayani godiya"yafada yana hawaye,Sakinsa mu"azzam yayi kafin yace"Basai ka godemin ba,nima kabani abu mafi soyuwa da daraja atare dani,so ya"yan ne yanzu kafara tarawa,da an haifa an yaye zasu dawo hannunka,insha Allahu.."washe baki Alhaji yayi kamar yayima mu"azzam sujudda.
Hajara tazo ta amshi su little ta rumgume tana hawaye,ta duka harkasa tanama mu"azzam godiya,suka ko lafe ajikinta kamar sunsan yanzu itace makwafin uwarsu,Ummi da zahirah Zuciyarsu bata baci ba saboda hukuncin mu"azzzam duba da yadda Alhaji yayi musu hallarci yasake basu daman mallakan juna akarona biyu,Ummi kowa bata saka komai,domin nan da wata shekara ai wasu jikokin zasu zo bama daya ba biyu ba,kila Fiye da haka itama ta nuna murnanta haka hajiya da Shureim,Bukar ko yakasa mgana saboda Farincikin nan fa aka hadu anata godiya tare da jinjima Karamci da Zurfin Tunanin Mu"azzam,shiko damam Wannan kyautar tuni tadade aransa,tun Sadda zahirah ta bashi lbrin Alhaji da halin dayake ciki,shiko yayi alqawarin Shima sai yabashi wani Abu mai muhimmanci kamar yadda Shima yabashi.