Sashe 43
Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Badon Ushe yagama yarda ba yafada mota yayi Reverse,yakoma hanyar gida,sai dabMu"azzam yaga kulewan Ushe kafin ya juya yana dauke hawayen idonsa,Karamin siririn glass din dake makale gefen aljihun rigarsa ya ciro ya saka,kan ya saka hannu ya tsaida Keke napep din daketa wucewa,nan da nan ko daya ya tsaya batare da bata lokaci ba yace"Airport zaka kaini.."hau muje yallabai.."yabashi amsa,Cikin azama yafada ciki,mai keken yaja suka fara Tafiya,basu wani jima ba,mu"azzam ya zaro wayarsa ya ciro layin dake ciki, ya saka abaki ya Tauneshi kafin ya Furzar dashi ta waje,ya kashe wayar gabadaya ya maidata aljihu.
Tafiyan minti talatin ta sadasu da Airport din ya sauka ya biyashi kudinsa ya karisa cikin Airport din,yana zuwa kuwa yasamu Jirgin da zai Tashi nan dan lokaci shine wanda zai yada zango a lagos,bayason bata lokaci nan da nan ya siya Tikiti yazauna zaman jira,domin ya kagara yafara nisa da garin Abuja,sai duba agogon Fatar dake hannunsa yake bayan kowani dakika.
Baifi Mintin arba"in da zuwa ba,aka fara sanarwan tashin jirgin kafin akafara kiran sunayen masu tashi,cikin lokaci aka kammallawa komai suka shiga jirgi ya tashi yafara yawo Asararin samaniya,Runtse ido mu"azzam yayi yana fadi afili.."Ki Yafemin Ummi na, Dan"Uwa kaima ka yafemin my hira and u too.."Yafada yana kwantar da kanshi bisa kujeran jirgin yanaji yadda kowani gaba na jikinsa ke amsawa hannu yasa yana maida sumar kansa baya yana kokarin ba kansa karfin gwiwa fadi yake"Zan iya,insha Allahu Zan iya.."wanda ke Sit din gefensa dayake A First class suke da kallo ya bisa yana mamakin to meke Faruwa da wannan ne,yana ta sambatu shikadai.
*SAFE LANDEED ZAHMUZ*😘
____________________
Tun bayan Tafiyan mu"azzam taji gabadaya yanayinta ya chanza gabanta na wayan Faduwa,kafafunta kuma suna rawa,haka kurum lokaci daya kuma zuciyarta ta hau tsinkewa sama,ta haura ta dauko wayarta ta sauko falo tafara kokarin kiran mu"azzam din ammh network yaki bari dole ta hakura ta zabga tagumi tana fatan Allah yasa lafiya.
Batawani dade zaune ba,Taji sallamar Ushe a tsakiyar falon saboda yadda tayi zurfi Atunani ko shigowar motar bataji ba ganin ushe sai da yasa gabanta ya fadi Ras!Ras!Ras,jikinta na rawa ta mike hannunta dafe da kirji tace"Kai lafiya?ina da'na yake..?
Tafada cike da tsoro da Razana,cikin girmamawa ushe ya dan rankwafa kafin ya zaro Takarda a aljihunsa yana fadin"Am srry Hajiya,yallabai ne ya aiko ne,na kawo miki wannan takardan wai ya manta ne kafin ya fita bai baki ba.."
Cikin wani yanayi Ummi ke bin Ushe dashi da zungureriyar takardan dake hannunsa da kallo,kafin tace cikin Rawan murya."Ni..Ni..Ku..ma.."Tafada lokacin dataji zuciyarta ta tsinke,gyada mata kai yayi ,Cikin mutuwar jiki ta mika hannu ta amshi takardan tana fadin"Ina shi mu"azzam din.."?
"Yace na kawo miki,shi zai hau Taxxi ya karisa na sameshi achan.."Ai Ummi bata jira Ushe yagama bayani ba ta warware takarda, ta iske Dogon Rubutun danta mu"azzam cikin Rudewa da firgici tafara karantawa a bayyane kamar haka.
_*Assalamu Alaiki Ummi na,Ina fatan lokacin da Wannan takardan Zai Riskeki zaki yi hakuri ki dauki kaddara,Ummi na na yanke hukunci yin Nisa dake da duk wani abun jin dadi daya danganceni,ciki harda ke da Sana"ata,nazabi Na tafi na barku ko Allah zai sa na tsinci Farincikina achan,zuciyata bazata iya zama babu Zahirah ba ummi,itace ginshiki na rayuwata,Itace haske Fitila dake haskaka rayuwata,itace komai nawa Ummi rabani da ita dakikayi tamkar kinyi kokarin rabani da Numfashi na ne,Bazan iya juran ganin Hirah bata dawo gareni ba,bazan iya juran ganinta agidan wani ba Ummi,shiyasa na yanke hukunci Tafiya chan wani waje mai Nisa inje incigaba da rayuwata harta Allah ta kasance agareni,kiyi hakuri Ummi ko na zauna wlh tallahi bazan iya yimiki biyayyah ba,nikuma bani so na zama cikin wa"inda Allah zaiyi Fushi dasu,Kiduba dakina, a saman Side drower na bar miki kudade sannan ga Atm dina na banki guda biyu,akwai makullayen motocina dana wannan gidan damuke ciki,kana akwai na wani gida nawa,wanda ke jabi road,ushe yasan da gidan ko shi kikama mgana zai kaiki,ki dinga amfani da kudin wajen biyan bukatanki na yau da kullum,kikuma rika biyan ma"aikatan dake gidan hakkinsu nasan dukiyar da na bar mike zata isheshiki har karshen rayuwarki Ummi na,Kada kuma ki wahalar da kanki wajen nemana,nariga nayi miki nisa,nisan da bazaki taba samu na ba har abada,nidai Fatana ki yafemin laifin dana aikata miki,kikuma samun albarka,Nagode daga Da"n ki mai kaunar Farincikinki..Ibrahim Muhammed moodu Allah ya hada Fuskokinmu da Alheri Ummi na*_
Ai Tunkan Ummi takai karahen takardan Ta sulale ta zube kasa lokaci daya ta yanka wani uban ihu hannunta bisa kanta tana fadin"Wayyo na shiga uku,na mutu na lalace..."Take fada lokaci daya tana buga kanta jikin kujera,Shikanshi ushe dayaji komai hannu ya dora akai yana kiran"Oh Jesus..."Su karime dasu lami dake kichen da gudu suka fito suna tambayan lafiya,sani maigadi da falalu ma ba"a barsu abaya ba suka shigo falon suna tambayan meke faruwa.
Ummi datagama haukacewa,tuni ta mike ta isa ga Ushe tadamke wuyan rigansa tana fadin"Don ubanka ina ka kaimin da'na,ina kakai min da'na nace..."?Tafada cikin tsawa tana jijjigasa lokaci daya hawaye na wanke mata Fuska,shima hawayen yake yana fadin"I don"t know hajiya i Swear..."Yafada jikinsa na rawa su karime dake tsaye sun kasa Fahimtar meke faruwa,cikin wani ja baya Ummi tayi kan ta kwasa da gudu ta fice hannunta bisa kai tana fadin"Da'na Da'na jama"a ina Da"na yake,ku nemomin da"na,wayyo nikaina..Na bani na lalace ni Suhaima banda kowa bani da kowa sai shi,ku taimakeni don Allah."Haka take fada bayan tafice haraban gidan tana kuka da sambatu kamar zautattaciya.
Ushe ne yake koramusu karime bayanin dayaji Ummi ta karanta a takarda,ai suma dukkansu sai suka dora hannu aka suka fasa kuka,Sani maigadi fadi yake"Wlh ba hajiya kadai ta shiga uku ba hadda mu.."yafada yana share kwallah,karar faduwar abu sukaji kamar na mutum, shiyasasu Rumtuma wa da gudu zuwa haraban gidan,abunda sukagani ne ya firgitasu domin Ummi ce kwance akasa tana wani kakkafewa bakinta na Fitar da wani kumfa kamar wacce tasha Guba,kowani abu wanda zai mata lahani.
Cikin karaji da firgici dukkansu sukayi kanta suna jijjigata karime ke fadi cikin kuka"Wayyo Allah Hajiya don Allah kema ki tashi,in kika mutu ya zamuyi babu yallabai babu ke..Wayyo ni kaina kaicho da wannan rayuwar mai cike da kalubale.."Tafada tana kuka,Ushe ne yayi saurin cemusu su kamota bari ya kawo mota sukaita asibiti,haka ko akayi ya kawo mota wajen suka ciccibeta suka sanyata amota,karime ta shiga tare da ita,shikuma shida Falalu suka shiga gidan gaba,suka fice aguje cikin tashin hankali fuskarsu ko kadan babu Annuri saboda wannan Sabon Tashin hankalin da sukaci karo dashi da sassafen nan.
Specialist hop,suka kaita domin Ushe yasan nan ne Asibitin dasuke zuwa Dr,Abduljabar na kan Duty ranar,shi ya amshi unmi cikin rudewa yana fadin"innalillahi,meya faru ne haka? ina brr.? yafada bayan Nurses sun kawo gadon marasa lafiya an dorata akai kai tsaye aka shigeta da ita emargency cikin tashin hankali da rudewa saboda yadda Ummi take wani abu kamar wacce Zata fado daga kan gadon da"a ka daurata.
*********
Suko Su Uwani da"aka bari agida suna shiga gida lami ta yanke shawaran adau wayan hajiya akira Chan zaria afada musu hadin dasuke ciki,Sunyi na"am da shawaranta sai dai kuma wayar ta Ummi tana cikin password babu wanda ya iya budewa dole suka tasama waya ido,sunajiran Abunda Allah zaiyi,duk da Ummi tabasu tsausayi azahirin gaskiya komai ya faru Ummi ce sila gashi tayi sanadiyar da danta kwara daya jal aduniya ya gujemata,to wagari ya waya tsakani Ga Allah.
Achan kuwa asibiti sai da suka kwashe wajen awa biyu kafin likitocin su Fito suna share zufa,Dr Abduljabar ya kariso wajensu Ushe yana fadin"Ina brr, ne? yafada yana kallonsu,kallon kallon akayi tsakanin ushe da karime kafin karime ta bude baki ta shiga fadama Dr"abunda yafaru ushe na kara koramai bayani,baya Dr.Abduljabar yayi yana fadin"innalillahi wa"inna Alaihirraju"un..."yaketa maimatawa bayan ya dafe kansa yake fadin"why brr,?zaka ma Ummi haka,bayan kafi kowa sanin Ummi bazata iya daukan kaddarar rasaka ba.."yafada yana jin wani Raunin zuciya yana shigansa juyawa kawai yayi ya shige office dinsa, yana sallallami wayarsa ya zaro ya shiga kiran layin mu"azzam din ammh kuma baturiyar tana sanar dashi layin akashe yake,dole ya hakura ya maida akalan kira ga Dr,Shureim.
Dr Shureim na tsaka da duba patient kiran Dr.Abduljabar ya shigo wayarsa,har ga Allah yaji faduwan gaba sanda kiran ya shigo,cikin mutuwar jiki ya dauki kiran yana fadin"Dr,brk da safiya.."Cikin tashin hankali Dr.Abduljabar yace"Dr.Shurein akwai mtsala,komai kakeyi ka barshi kutaho yanzu kaida hajiya zuwa Abuja.."yafada cikin nuna damuwa,saurin mikewa yayi yana fadin"Subhannallahi Dr.Wani abu ya Faru? ko jikin dan"uwana ne ya kara tashi.?."cikin wani yanayi Dr.Abduljabar yace"Komai ma ya rikice Dr.Mganar bazata yuyu ta waya ba,ammh ga Ummi an kawo asibiti ba yarda take,sannan ma"aikatan gidan suna fadamin wai brr,ya tafi ya bar Ummi shine sanadin shiganta halin datake Ciki.."Kadan ya rage Dr.Shureim bai fadi ba sakamakon Saurin dafe tebur din dake gabansa dayayi da hannu daya, zufa na ketomai ta ko"ina yake fadin"Allah gareka muke,kuma gareka zamu koma..."yafada lokaci daya yana datse wayan,yadafe kansa yayi yana ta kiran sunan Allah tuni idanunsa suka kada sukayi jawur cikin wata murya yake fadin"wayyo Ummi kin cucemu kin Cucu kanki,kin raba kanki da dan'ki da kanki,kin rabani da dan"uwa na,wanda tunda muka taso bamu taba rabuwa ba,koda da rana daya ba,kaichon ki Ummi,kaichonki Ummi.."yafada wasu zafafan hawaye na zuraromai,Cikin zafin nama ya tarrara kayansa ya fice domin patient din dayake dubawa tuni takama kanta tayi waje taga likita da kanshi na hawaye.
Cikin wannan yanayin yajema hajiya zubemata kawai yayi yana kuka fadi yake"Shikenan Hajiya,Burin Ummi ya cika ta rabamu da mu"azzam" yafada yana fashe mata da kuka,iya rudewa Hajiya tayi rude,ganin kukan da Shureim yakeyi gakuma kalaman dayake fada cikin tashin hankali da Firgici tace"Badai Mu"azzam ya rasu bane Shureim..? girgizamata kai yayi kafin ya hau fadamata abunda Dr.Yagama fadamasa,hannu hajiya tadora akai tana kiran Sunan Allah kafin tace"Shikenan kurunkus kan kusa,Dama Abunda suhaima takeso kenan,kuma gashi ya faru,ohni baraka Allah kabamu ikon cinye wannan jarabawan na rayuwa dakake jarabtanmu.."Tafada kwallah na ziraromata.Shiko shureim kokarin kiran mu"azzam yake awaya ammh shima ana fadamai layin akashe yake,dafe kansa kawai yayi yana digan hawaye lokaci daya yanajn tsausayin mu"azzam yakamasa domin yafi kowa sanin waye mu"azzam Tunda yace yatafi to ya tafin ne,kuma sai Abunda Allah yayi.