Sashe 39
Uwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baisamu zarafin mata mgana ba, ya nufi shashen mu"azzam din yahau bugamasa kofa yana fadin"Dan"uwa kazo ka bude nine..."ammh ina mu"azzam na jinsu sai dai kuma baida karfin iya tashi saboda yadda jikinsa ya saki gabadaya jininsa ke zuba ta baki ta hanci ga yadda zuciyarsa ke zafi,yana so ma ya mike ya kasa.
Hankalin Shureim ya tashi da baya yaja yama kofar duka daya ta bude, da gudu suka rankaya shida Ummi cikin daki suna kwalamai kira,Ummi kuwa kamar ta zare tsabar rudewa,sun shiga bedroom din suna kiran sunansa ammh duk basu lura dashi yashe kan kafet ba,sai da Shureim ya duba tiolet nan ma babu shi kana yafito yana kokarin Ficewa daga bedroom din ne yaji ya shuru kafan mutum,cikin wani razana yakai kallonsa kan mu"azzam wanda gabadaya jikinsa ya baci da jini cikin wani karaji ya karisa garesa yana rikosa lokaci daya yake fadin"Mu"azzam....."da karfi cikin tashin hankali.
Da gudun gaske Ummi ta kariso wajen ganin yadda mu"azzam yazama kamar mataccen ga jini duk yabatamai jiki ai sai ta dora hannu akai tasaki ihu tana fadin"Na shiga uku ni Suhaima, mezan gani haka mu"azzam? tafada tana tale mai ido kamar wata zararra ganin haka yasa kawai Shureim Ficewa da sauri zuwa haraban gidan yana kwalama su Ushe kira da hanzari suka fito da hannu kawai yayi musu alamar dasu biyosa,suna shiga dakin suka tarar da Ummi durkushe gaban mu"azzam tana girgizasa tana kuka da sambatu,cikin Rudewa shureim yace"Ku taimakamana mukaisa mota.."Yafada muryansa na rawa suma din cikin Tashin hankalin suke da hanzari suka tallabeshi sukayo waje dashi,su karime dake tsaye suna ganin An Fito da yallabai kamar gawa ai sai suka rikice da kuka,Ummi kuwa kamar ta zare Amota suka sanyasa shureim ya shiga mazaunin Direba Ummi kuma dako takalmi babu balle mayafi ta shige baya wajen mu"azzam tana rumgume dashi tana kukan ta shiga uku.
Specialist hop,suka nufa,suna isa Shureim yayi ciki yana kiran Nurses da gudu kuwa sukazo da abun daukan mara lafiya suka ciccibi mu"azzam suka dora da gudu sukayi cikin asibitin dashi,kai tsaye aka shiga emaergency dashi cikin mawuyacin hali mai wuyar fassaruwa.
Ummi zaman dirshan tayi abakin emergency tana rusa kuka,shureim yakasa mata mgana domin shima kamar yayi kukan yakeji,tabbas in abunda yake zargi ne yakama mu"azzam lalle rayuwarsa tana cikin hadari,ganin Ummi tafara tara musu mutane ne yasa ya isa gareta yana fadin"Don Allah Ummi,kiyi hakuri kibar wannan kuka,taso muje ki zauna insha Allahu Mu'azzam zai tashi bazai mutu ya barki ba.."dagowa tayi ta kallesa idanunta suncika da hawaye tace"Haba shureim inbar kuka fa kace? baka duba da ni ya nawa rayuwar zata cigaba matukar mu"azzam ya mutu ya barni,wlh rayuwata,bata da amfani ina mai tabbatarmaka nima zaku iya rasani.."Tafada tana rusa kuka.
Kallonta yake cikin tabbatar da abunda ta fada,kafin ya riko hannunta ya mikar da ita yana fadin"Naji Ummi,ammh kitashi addu"anmu kadai yake bukata ba kukanmu ba taso muje ki zauna kinji.."Dole tatashi yana riketa da ita harzuwa kan wani benci ya zaunar da ita shima ya zauna agefenta yana sakin ajiyar zuciya lokaci daya,itako Ummi hannunta ta hau kirgawa kamar tana charbi sai muyi muyi take da baki hawaye na shatata bisa kuncinta.
Sun dade shuru kafin shureim yakatse shurun da cewa"Wai duk meyajawo wannan abun ne Ummi? ni a iya sanina Mu"azzam baita ciwo makamancin wannan ba.?."Yafada yana kallonta,shuru Ummi tayi tana kallon kasa kan ta share hawaye tace"Takan na rabasa da wannan Tsinanniyar yarinyar mana,ashe ba haka tabarmin dana ba,sai da ta asirceshi kafin ta barshi.."Cikin Rudewa Shureim yace"Wa? zahirah Kike Nufi Ummi? badai kin saka mu"azzam ya saketa ba..?'wani banzan kallon Ummi tamai kantace"kwarai ni dakaina na saka ya saketa ,.."Tafada kai tsaye.
Shureim dayayi mutuwar zaune cikin wani yanayi yace"Kan wani dalili Ummi? Gefe ta kallah kan tace"Kan daliin cin amanata da sukayi yayi mata ciki batare da na sani ba,nikuma har abada bazan hada zuru"a da Diyar Fadi ba, har abada."Tafada cikin son tabbatarwa.
Dafe kai shureim yayi yana fadin"Shikenan Ummi,kinyi sanadiyar dakushe Farincikin Mu"azzam,wlh tallahi zahirah itace ginshikin Farincikin rayuwarki data mu"azzam gabadaya.."Yafada cikin karaya wani banzan kallo Ummi tamai kafin tatashi ta chanza wajen zama tana hararan shureim din,shiko kallonta yake yana mamakin Ummi ashe haka tayi nisa baitaba sani ba,ki raba miji da mata,kuma harkina kirari da kanki,kai Tir da wannan bakar zuciyar,zuciyar da bazata kulla maka alkhairi kan mutane ba sai sharrinsu.
Wajen awa biyu likitoci suka kwashe da Mu"azzam kafin su fito cikinsu harda Dr.Abduljabar,office kawai yace Shureim ya biyosa,ummi na ganin haka tayi zuruf tabi bayansa kamar wacce akace dama bazata ji ba,suna zuwa office din Shureim ya zauna yana fadin"Dr,ya jikin Dan"uwa na hop dai ba abunda nake zargi bane..ko?"
Yafada yana kallonsa,jinjina kai Dr Abduljabar yayi kafin yace"Nayi matukar mamakin yadda Ciwon zuciya yakama brr,mu"azzam lokaci daya,wani irin tashin hankali ne ya gani ko ya faru dashi,wanda yayi sanadiyar taba masa zuciya haka..? dafe kai Shureim yayi yana fadin"hasbunallahi wa"ni imal wakil..."Ummi kuwa dake gefe ta dora hannu kai tana fadin"menaji kuna cewa,Son din nawa ne yakamu da ciwon zuciya,na shiga uku ni Suhaima tsakani na da Shettima Allah ya isa bazan taba yafemai ba..' Tafada tana kuka ko kallonta Shureim baiyi ba Saboda yadda ta bashi Haushi,kina neman kashe danki da kanki ammh kina sakarci kin kasa ganewa.
Dr.Abduljabar ne ma ya shiga bata baki,shureim ne ya katseshi da cewa"Dr wht iz d solution now..? Dr Abduljabar yace"Munyi nasaran dawo da Numfashinsa,ammh yanzu yana bukatar jini gaskiya,kuma dole ne aguji tuna mai da abunda zai dinga tadamai da hankali,kuma don Allah abunda yake bukata ko yake son gani to ya kasance yana kusa dashi,gudun tashin ciwonsa.."Rausayar dakai Shureim yayi kafin yace"Abunda zai gani ya kwantar mai da hankali har ya sashi Natsuwa Ummi tayi sanadiyar da yayi mai Nisa na har abada.."yafada kai tsaye yana kuma kallon Ummi,wacce tayi Tsuru tana kallonsa,shiko ko ajikinsa illa mikewa da yayi yabama Dr hannu sukayi musabaha tare da fadamasa suje a dibi jininsa domin shi yana iya bama kowa.
Leda biyu na jini aka diba na shureim aka sakama Mu"azzam wanda ke daki na mussamam babu mai shiga sai likotoci,ko Ummi duk kwakwanta anki barinta shiga sai dai ta lekasa ta jikin glasa din daya ma dakin kwanya,har dare suna Asibitin bai farfado ba,daman Dr Abduljabar yace ana sa ran farfadowansa yau zuwa gobe insha Allahu.
Sai lokacin yaduba wayarsa misseds clls ruturutu,na zulaika dana hajiya yasani dole hankalinsu ya tashi har dare bai dawo ba,haraban asibitin yafita yaje cikin msallacin asibitin yayi sallolin dake kansa,kafin ya samu Natsuwar kiran hajiya,wacce yana labartamata abunda ke faruwa tana zaune ne,sai da tazamo kasa saboda tashin hankali cikin wani yanayi ta Furta"Innalillahi wa'inna Alaihirraju"un...,Ashe suhaima bata da hankali bansani ba,ashe Suhaima haka take bansani ba,ashe bata da wayau bansani ba,sakarya kawai mara tunani,taje ta kashe danta akan gabanta na banza,shettima ko yana asara kadan ne,ita sai tafi kowa kuka da shiga damuwa"Hajiya tafada kamar tama zahirah da mu"azzam din kwallah
Shureim yace"wlh hajiya sai ma kinga yadda dan"uwa yadawo kamar wanda ya shekara yana ciwo.."yafada kamar yayi kuka,hajiya tace"Allah sarki bawan Allah,ya hadu da jarabawar Uwa,Allah ya tashi kafadunsa..,"Shureim ya karba da Amin..Kafin hajiya tace"in ita Suhaimar..? yace"Tana cikin Asibiti tana ta ma mutane koke koke.."Tsaki hajiya taja kan tace"mtseww...Koke koken banzanta,ubanwa zata ma kuka bayan duk abubda ya faru itace sila,sakarya mara wayau,kai gobe ma Kabiru zai kawoni dole nazo nacimata mutumci,kuma saita bar asibitin nan,kada ma ya farka yacikaro da ita zuciyarsa tabuga ya mutu gabadaya.."Shureim dai hakuri yake ba hajiya ammh ta inda take fita dabam ta inda take shiga dabam,sallama sukayi hajiya nakara jadaddamai gobe tana tafe.
Dakyar shureim ya lallaba ummi,suka koma gida don wajen basu bukatar mai jinya suke kula da komai balle shi da ko ganinsa ba"ayi balle tace saboda shi zata zauna,koda suka koma gida yadda Ummi taga rana haka taga dare tayi kuka kamar ranta zai fita,shettima ko da fadi sunsha Tsinuwa harda na bala"i,koda gari ya waye tukan Ma shureim ya tashi tasaka Ushe yakaita chan Asibitin tana ko zuwa aka hanata shiga har kuka tayima Dr Abduljabar kan yabari tashiga,taganshi ammh yahana saboda dokace sai in ya farka,nan ta zauna tana lekensa tana share hawaye.
Karfe goma tayima hajiya baraka acikin asibitin dayake dama tasan Asibitin kai tsaye tazo,Shureim shiyazo yayi mata jagora zuwa wajen da"a ka ijiye mu"azzam,wanda shima bai dade da zuwa ba,Ummi tana ganin hajiya ta fashe da kuka tatashi zata rumgumeta hajiya takauce tana fadin"Karki sake ki tabani,kuka kikeyisuhaima,ai nadauka yadda zuciyarki takekashe da rashin imani bazaki taba kuka saboda halin da kika jefa danki da kanki ba.."Sororo Ummi tayi tana kallon Hajiya kan tace cikin kuka "Ni kuma yaya..? tafada tana nuna kanta.
Gyada mata kai hajiya tayi kan tace"Kwarai da gaske,ai bandauka haka kika zama mara imani ba da tsausayi,ace ki saka danki ya saki matarsa da tsohon ciki,kuma ki koreta a daren,haba rashin imanin naki Suhaima ya wucema yadda nake tsammani wallh.."Tafada ranta bace,dukewa kawai Ummi tayi tana kuka hajiya ko ta cigaba da cewa"bansan cewa haka sakarcin naki yayi yawa ba sai yau,ke aka cuta daga karshe suke da riba,domin kin saka ya saketa,takoma gida,sun karbi diyansu sun rike sunbarki da halinki,kuma ciki jikinta inta haifeshi,nasu ne ke kuma kinga kin,rasa farincikin danki gashi kwance rai a hannu Allah ,ke baga da"n ba kuma ke baga suruka ba,kuma ke baga jokokinki ba,duk kinyi batan batatatan,kin zabi ki durkushe rayuwarki da hannunki suhaima,wlh Tir girmanki da wayonki bai tsinana miki komai sai ci baya.."Hajiya tafada kwallah na ziraromata.
Ummi kuwa akasa ta zauna tana rusan kuka tana fadin"Na shiga uku ni yaya,taya zaki dinga ganin laifi na,wlh har abada bazan yi nadaman abunda na aikata ba" Tafada tana kuka t Hajiya tace',Baki shiga uku ba tukunnah,Sai in dan naki ya mutu gabadaya kinga nan saiki lalace gabadaya,kuma nadama bayanzu nake sonkiyi ba Suhaima,sai lokacin Nadamar naki yazo lokacin nake so yi Nadama,"Tafada cikin bacin rai.